Daga Mazhun Idris
A wani jawabi mai sosa rai da ya yi gabanin ranar Zaman Lafiya ta Duniya, wadda ake bikinta duk 21 ga Satumba, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya koka da yadda rikice-rikice a fadin duniya suke "tilasta wa mutane barin muhallinsu".
A Afirka, kamar yadda yake a da yawan yankunan duniya da ake neman zaman lafiya mai dorewa, mabambantan dalilan da ke haddasa rikici da makami, da rikicin siyasa, da na yanayi, suna janyo ayyukan samar da zaman lafiya ya yi wahala.
Zaman lafiya ba ya samuwa shi da kansa, kuma ba a samar da shi ta amfani da jiragen yaki, ko ta ayyukan masu bayar da agaji, ko sakamakon ayyukan dakarun wanzar da zaman lafiya. Hatta yarjejiya zaman lafiya ba ta iya samar da cikakkiyar lumana kai-tsaye.
Kaɗa gangar yaki da aka yi ta yi a daruruwan shekaru a tarihin duniya bai koyar da darasin cewa zaman lafiya ba abu ne da ake iya zartar wa da baki ba, ko a tursasa ta hanyar doka.
Ana bukatar mutane su yi aike tare don hana tararrabi ya haifar da tashin hankali. Idan har za mu iya shelanta tsagaita wuta, ko yarjejeniyar zaman lafiya, to kuwa ya wajaba mu yi aiki don gina zaman lumana.
Akwai tarin rikice-rikice a da yawa daga kasashen Afirka, da suka hada da Nijeriya, da Mali, da Mozambique, da Nijar, da Kamaru, da Chadi, da Sudan, da Libya, da Burkina Faso, da Habasha, da Somaliya da kuma Senegal, wadanda suka faru sakamakon dalilai daban-daban.
Ana bukatar sabbin dabarun kawo zaman lafiya a yankunan Afirka, duba da abubuwan da ke haddasa rikice-rikice a nahiyar.
Masu cin ribar rikici
Nazarin rikici wata hanya ce ta fayyace sanadin rikici, don shirya tsare-tsaren da za su taimaka wajen gina zaman lafiya. Kafin yanke hukunci kan shirin magance rikci, muna bukatar fayyace musabbabansa, kamar na tattalin arziki ko siyasa ko tsattsauran ra'ayi.
"Akwai masu cin ribar rikice-rikice a Afirka," in ji Dr Maji Peterx, wanda ya yi shekaru 20 yana shirya dabarun kawar da tsattsauran ra'ayi, da kula tunanin wadanda rikici ya shafa, da karfafa guiwar al'umma kar su shiga rikici.
Dr Maji wanda shi ne babban darakatan cibiyar Equal Access International ya gaya wa TRT Afrika cewa, "Wannan batu ya taso ne saboda gwamnatoci sun fi son amfani da karfin soji don magance rikici, sakamakon babban burinsu shi ne dakile rikici da dawo da doka da oda."
Yawanci babu ma'ana a ce an fifita kin amfani da hanyar kawar da tsattsauran ra'ayi da isar da sakonni cikin hikima, don kawar da ababen da ke jawo mutane su fara shiga rikici saboda samun arziki.
Dr Maji ya bayyana cewa, "Ta hanyar nazarin matsayin rikici da tuntuba, za mu gano wadanda ya shafa na ciki da na waje, da masu ruwa da tsaki, da jagororin al'umma, sannan mu yi duba kan bukata da kalubalen kowannensu.".
Da zarar an gano masu cin amfanin rikici, da masu cin ribarsa, maradi na gaba shi ne rabewa tsakanin wadanda ke shiga rikici saboda dalilin tsana, da kuma masu tsattsauran ra'ayi da masu shiga saboda an tursasa su.
Dr Maji ya ce, "Daga nan, sai a far aiki tare da al''ummomin don kawar da azzalumai masu cin ribar rikicin, da kawar da rashin yarda a al'umma."
Salon inganta zaman lafiya
A hakika, zaman lafiya ba abu ne da ke samuwa saboda kawai babu rikici ba. Rikici abu ne da ake samu a rayuwa kuma hanyar mafi kyau don shawo kansa shi ne amfani da damar assasa zaman tattaunawa, da fahimtar juna.
Dr Maji ya ce, "Baya ga tsagaita wuta da dakatar da gaba, jagororin al'umma za su yi aiki don inganta zaman lafiya, karkashin tsarin mutunta juna, da daidaito da aiki tare."
Salon anmfani da karfin soji da gallazawa don dakiel rikici, sau da yawa yana haifar da cin zarafin mutane, da take hakki, da tursasa mutane barin gidajensu, da cutar da muhalli, da rusa turakun walwalar al'umma, da kuma gadar da gaba.
A nan ne kungiyoyin inganta zaman lafiya suke da muhimmanci. Wadannan kungiyoyi sun kware wajen tsara dabarun cimma bukatun magance matsalolin yankinsu. Wata babbar cibiyar inganta zaman lafiya a Afirka ita ce cibiyar Kofi Annan Centre in Ghana.
Ba kamar kotuna ba, kungiyoyin inganta zaman lafiya suna da muradin samar da adalci, da warware takaddama, da fadin gaskiya, da yin yafiya, da fahimtar juna. Tsarinsu shi ne babu amfani da karfi.
Akwai kungiyoyin da yawa, kuma yawancinsu ba na gwamnati ba ne, kuma ba don neman kudi ake kafa su ba. Don haka sukan furkanci rashin karfi wajen, inda Dr Maji ya bayyana cewa "kungiyoyin inganta zaman lafiya suna iya aiki ne kawai a inda dooka ta sahale musu".
Rigakafin rikici
Shawo kan rikici yana auna tasirinsa kan al'ummomi, da gano cutarwar da ya yi musu, kafin fara aikin kashe wutar rikici, da warware shi, da gida hadin kan al'umma.
Kama daga kasar Afirka ta Kudu, da Rwanda da Liberia, an yi nasarar gudanar da tarukan zaman lafiya, don assasa tattaunawa, da diflomasiyya, da fadin gaskiya, da yafiya, sasantawa. Ayyukan sun nuna tasiri wajen sasanta rikici rage tunanin rikici.
Dr Maji ya yi gargadin cewa, "Rikicin da ya dagule musamman wanda ya faru sakamakon tsattsauran ra'ayi yana tasiri matuka kan al'umma, irin tasirin da ke barin baya da kura, idan ba a magance shi ba, sai ya haifar da sabon rikici daga baya".
"Wannan ya sa idan aka gwada tunanin kaduwa a cikin al'umma, ake gano da yawa jama'a suna nuna alamun kamuwa da cutar damuwa saboda rikici a baya, kuma zai ci gaba har sai idan an yi aikin kawar da kaduwar."
Wannan tsarin yana taiumakawa wajen rigakafin bayyanar rikici a al'umma da hana hare-haren ramuwa, da kitsa tunanin daukar fansa. Bambancin masu aikata rikici da wadanda abin ke shafa, yakan yi wuyar ganewa a rikici mai cike da takaddama, saboda yawaitarsa da dadewa ana rikicin.
Dr Maji ya fada wa TRT Afrika cewa, "Don gina dawwamamman zaman lafiya, muna kallon batutuwan talauci, da rashi yarda, da rabuwar kai, da zargi, da rashin daidaito, da rashin adalici cikin al'umma. Daga nan sai a mayar da hankali kan kawar da damuwa, da bayar da shawara, da haukurkurtarwa ga wadanda abin ya shafa.".
Daga karshe, abin da zai faru shi ne tasirin salon ayyukan inganta zaman lafiya zai bayyana da kdan-kadan, ta hanyar raguwar taraddadi, da aiki tare, wanda zai janyo zaman tare cikin lumana, da rayuwa tsakani masu ra'ayi da addini daban-daban.