Ana ganin sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD sun nuna gazawa wurin samar da zaman lafiya a DR COngo. / Hoto: Reuters

Shirin Wanzar da Zaman Lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali wato Minusma, ya kammala janye dakarunsa daga kasar, inda takwarar shirin wato Monusco wanda ake yi a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ya soma janye dakarun a hankali bayan Kinshasa ta bukaci hakan.

Shekarar 2023 ta kasance shekarar da aka yi watsi da ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD a nahiyar, inda ake kallon zaman sojojin a matsayin wani lamari da ke janyo bacin ran jama'a da kuma zanga-zanga wanda a wasu lokuta suke jawo asarar rayuka,

Da alama a halin yanzu, ba a maraba da hular kwano mai shudiya a Afirka.

Janyewar Minusma daga Mali

Sojojin Minusma 11,600 da 'yan sanda 1,500 sun bar Bamako a ranar 11 ga watan Disamba domin kawo karshe zamansu na sama da shekara goma inda aka kai su domin yaki da 'yan ta'adda. Janyewar ta gaggawar ta zo ne sakamakon bukatar da Bamako ta yi.

A watan Yunin da ya gabata, an ga abin da ba a yi zato ba bayan Ministan Harkokin Wajen Mali Abdoulaye Diop ya fito a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya inda ya bukaci Minusma su bar Mali, tare da ba su har zuwa karshen Disambar 2023 su kammala ficewa.

Sakamakon goyon bayan da ta samu daga kungiyoyi masu zaman kansu, Bamako ta tsaya kan bakarta domin tabbatar da janyewar dakarun duk da turjiya da aka samu daga kasashe wadanda suka hada da Amurka wadda ta yi Allah wadai da wannan matakin.

Haka kuma Monusco wanda shi ne shirin wanzar da zaman lafiya mafi tsada da MDD ke aiwatarwa a duniya, ya soma janye dakarunsa daga Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a ranar 19 ga watan Disamba bayan gwamnatin Kongo ta bukaci haka.

Janyewar na zuwa ne duk da damuwa da aka rinka fuskanta daga gabashin kasar a daidai lokacin da kasar ta kama hanyar gudanar da zabe.

Akwai dubban sojoji da ke yi wa shirin MINUSMA aiki a Mali. / Hoto: Reuters

Kinshasa na so a janye dakaru cikin gaggawa

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna matukar damuwarsa kan yiwuwar karuwar rikici a gabashin kasar idan babu dakarun wanzar da zaman lafiyan. Sai dai Kinshasa na ganin cewa dakarun na Majalisar Dinkin Duniya babu wani aikin da suke yi wurin kare farar hula daga kungiyoyin 'yan bindiga wadanda suka shafe sama da shekara 30 a yankin.

Hukumomin kasar sun bayyana cewa, hadin gwiwar "ya nuna iyakarsa, a wani yanayi na yaki na din-din-din, ba tare da an dawo da zaman lafiya da aka dade ana jira ba a gabashin Kongo."

Mambobin Kwamitin Tsaron MDD da dama wadanda suka hada da Amurka sun nuna shakkunsu a 'yan watannin nan kan ko dakarun Kongo sun shirya maye gurbin Monusco domin samar da tsaro.

"Mambobin wannan majalisar za su sa ido sosai kan abubuwa, a daidai lokacin da gwamnatin DRC ke son daukar cikakken alhakin kare fararen hula tare da janyewar Monusco." kamar yadda Mataimakin jakadan Amurka Robert Wood ya jaddada.

Sojojin MDD ba za su iya aiki ba tare da amincewar kasar da za su yi aiki a ciki ba.

Abin da ya 'rura' wannan wuta

Abin da ya tunzura janyewar dakarun na MDD ya samo asali ne bayan dakarun Faransa na Barkhane sun janye daga Mali a 2022 bayan sojojin da ke mulki a Mali sun bukaci haka.

Dakarun na Faransa sun shafe shekaru tara a cikin Mali inda aka kai su can domin yaki da masu tayar da kayar baya.

Sai dai rinka yi musu kallo a matsayin masu wata manufa ta daban - ana ganin cewa suna aiki ne a matsayin abokan kawancen sojojin Mali da masu kare kungiyoyin masu dauke da makamai.

Zargin da aka rinka yi musu na alaka da 'yan tawayen Tuareg shi ma ya rage musu kima.

Bayan makonni, sojojin Faransa na musamman wadanda ke jibge a Burkina Faso sun soma janyewa. Daga nan ne aka soma zanga-zangar kin jinin su bayan Keftin Traore ya hau kan karagar mulki.

Sojojin Faransa na musamman sun koma sansanoninsu da ke Nijar sai dai zamansu a can bai jima ba sakamakon a Yunin 2023, babban dogarin shugaban kasar Janar Abdourahamane Tiani ya kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.

Janar Tiani ya kafa gwamnatin rikon kwarya wadda ta kunshi sojoji da farar hula inda suka yi watsi da yarjejeniyoyin da Paris da Yamai suka saka wa hannu.

Ya bukaci dakarun na Faransa su bar Nijar nan take. Tuni sojojin na Faransa suka kammala ficewa daga kasar.

Dakarun Faransa sun janye daga Nijar da motocinsu. / Hoto: Reuters

Mali da Burkina Faso da Nijar, wadanda baki dayansu ke karkashin mulkin soji, sun kawo karshen duka wasu yarjejeniyoyi da aka yi masu muhimmanci musamman na tsaro da kasar da ta yi musu mulkin mallaka.

Kasashen a halin yanzu wadanda suka hada kai a matsayin Alliance of Sahel States (AES), sun kuma rufe kofar G5 Sahel - wadda kungiya ce wadda ta hada Mauritania da Mali da Burkina Faso da Nijar da Chadi.

Faransa ce ta kafa kungiyar domin yaki da ta'addanci a yankin na Sahel.

Kasashen Afirka wadanda a nan ne sojojin ke janyewa, a halin yanzu sun soma karkata zuwa wurin sabbin kawaye, wadanda suke sa ran cewa akwai yiwuwar su taimaka musu cimma burinsu na tsaro da zama masu cikakken iko.

TRT Afrika