Kwallon kafa na habaka zaman lafiya tsakanin matasa a birnin Jos. / Hoto: Football + Music = PEACE

Daga Mazhun Idris

Ranar 19 ga Nuwamban, tawagar kwallon kafa ta kasar Sudan ta yi nasara kan takwararta ta Jumhuriyar Dimukradiyyar Congo da ci daya tilo. Al'ummar kasar Sudan wadanda rikicin yakin da ake a kasar ya shafa, sun yi farin ciki har suka manta matsslarsu na dan lokaci.

Wasan da suka buga na neman gurbin shiga Kofin Duniya na FIFA 2026 ne, kuma nasarar ta Sudan ta yi ta nuna tasirin da kwallon kafa ke da shi wajen hada kan jama'a, ko da a lokacin da suke cikin kunci.

Sudan tana fuskantar rikici tun 15 ga watan Afrilu, bayan da rundunonin sojin kasar suka tsunduma yaki tsakaninsu don neman iko da kasar. Sakamakon yakin ya haifar da dubban mutane sun rasu kuma mutane miliyan bakwai sun rasa matsugunninsu.

Ya tabbata cewa kwallon kafa yana da tasiri wajen kawo tsagaita wutar rikici – ko da kuwa na kwana daya ne.

Pele a Nijeriya

Alal misali, a Nijeriya an samu tsagaita wuta na tsawon awanni 48 a shekarar 1969 don a buga wasan kwallo, lokacin da kasar ke fuskantar yakin basasa.

Shafin Marca ya ruwaito cewa ranar 4 ga Fabrairun 1969, ana tsaka da gwabza yakin basasan da aka yi wa lakabi da Yakin Biafra, gwarzon dan kwallon kafan nan na kasar Brazili, Pele, ya jagoranci kungiyarsa ta Santos FC inda suka kara na tawagar Nijeriya a birnin Legas, inda suka ci 2-1.

Kallon kafa hanya ce mai sauki don inganta zamantakewa. / Hoto: Football + Music = PEACE

A yayin wannan wasa na zumunta, bangarori biyu da ke yakin a Nijeriya sun ajiye makamansu kuma suka tsagaita wuta.

A shekarun baya-bayan nan, Birnin Jos, babban birnin jihar Filato da ke yankin Arewa maso tsakiyar Nijeriya, ya kasance garin ta ya yi suna da ayyukan hakar ma'adanai, kuma yana da al'ummomin kabilu akalla 40.

Rikicin kabilanci da addini

Mazauna Jos, wadanda suka kai kusan miliyan guda suna bin addinai daban-daban.

A shekarar 2001, wani mummunan rikicin kabilanci da addini ya barke a birnin. Al'ummomin da suka rayu tsawon shekaru a matsayin makota kuma abokai, sun koma suna takun saka da juna.

Amma ta hanyar tasirin wasannin motsa jiki, musamman kwallon kafa, tashin-tashina tsakanin mabambantan akidoji a birnin Jos yana raguwa.

Gasar Kwallon Kafa ta "Salama Football Tournament" wata gasa ce da ake shekara-shekara don karfafa zaman lafiya a birnin Jos. Kidauniyar Bege Foundation ce ta kaddamar da shirin a 2016, wadda manufar kungiyar ita ce assasa zaman lafiya.

'Dinke rarrabuwar al'umma'

Kenneth Attah, shi ne Jagoran Gidauniyar, kuma ya fada wa TRT Afrika cewa gasar tana hada kungiyoyi 16 a duk kaka, don inganta hadin-kai tsakanin matasa da ke birnin.

Kenneth ya ce "Mun zabi kwallon kafa ne saboda wasa ne da yake hada kan kowa, ba tare da nuna bambancin daraja ko arziki ba. Wasan yana iya warkar da matsalolin da ke raba kan jama'a."

Idan suna buga wasa, kowa na mantawa da rikici ko bambancin da ke tsakaninsu. / Hoto: Football + Music = PEACE

A wasu bangarorin na birnin, kungiyar "Face of Peace Global", wadda aka kafa a 2006, tana amfani da kwallon kafa don habaka zaman lafiya a Jos.

Shugaban kungiyar Salis Muhammad ya fada wa TRT Afrika cewa, "shirin hada kwallon kafa da kida don kawo zaman lafiya" babban shiri ne na kungiyar.

Silar zaman lafiya

Salis ya ce "Taruka ba su faye jan hankalin matasan da rikici ke shafa ba, amma kwallon kafa da kade-kade fagensu ne".

Ya kara da cewa, "bayan nazari kan yanayin al'ummarmu" mun fito da "Face of Peace Global" don amfani da kwallon kafa wajen cimma zaman lafiya.

Shi ma Kenneth Attah na gasar "Salama Football Tournament" ya ce: "Duk lokacin da muka shirya wasa, kowa da ke filin wasan yakan manta da bambancin da ke tsakaninsu. Masu kallo da 'yan wasa suna murna da rungumar juna."

A wajen Salis, gasar kwallon kafar da suke shiryawa tana ba wa kungiyarsu ta Face of Peace Global damar "haduwa da jagororin al'umma da shugabannin matasa" don assasa zaman lafiya.

Kalmomin lumana

Salis ya ce, kungiyoyin da ke buga gasar da muke shiryawa suna saka wa kansu sunayen kalmomin zaman lafiya kamar "yafiya", da "sasantawa", da "kauna", da "hakuri".

Ko da bayan kammala gasar, kungiyoyin suna ci gaba da wasa tare, a cewar kungiyoyin da muka zanta da su.

Salis ya ce kusan kulob din matasa guda 300 ne suka amfana da gasar ta shekara-shekara, cikin shekaru uku da suka gabata.

Umar Shehu Tabako, wanda shi ne tsohon shugaban magoya bayan kulob din kwallon kafa na jihar Filato, wato Plateau United, ya fada wa TRT Afrika cewa kwallon kafa yana dinke barakar addini da kabilanci tsakanin al'ummar Jos.

Mu'amala bayan dage dokar hana fita

Ya ce, "A wani lokaci a baya, an sanya dokar hana fita bayan wani rikici a Jos, amma bayan dage dokar na yi mamakin ganin 'yan wasan kwallo daga al'ummomin da ke rikici da juna, sun fito wasa, kuma sun yi murna tare, maimakon fada tsakaninsu".

Nijeriya daya ce cikin kasashen Afirka da ke kan gaba a wasan kwallon kafa, bisa la'akari da kididdigar FIFA.

Haka kuma daya ce cikin manyan kasuwannin kwallon kafa idan an duba yawan masoya, sakamakon yawan jama'arta da ke bibiyar wasan.

Masu fashin baki sun ce tasirin kwallon kafa wajen inganta zaman lafiya da hadin kai abu ne da za a ci gaba da cin gajiyarsa a kasar, da ma a duniya bakidaya.

TRT Afrika