Ibrahim Adjagbe ya rasa jinsa kwata-kwata yana ɗan shekara tara da haihuwa Photo: TRT Afrika

Daga Firmain Eric Mbadinga

A wani baiti na yabo game da nagartar ƙwaƙwalwa da zuciyarsa, an bayyana Ibrahim Adjagbe a matsayin "mai ceto" wanda ya ƴantar da ƙasa ta hanyar ƙaunar da yake wa ƙwallon ƙafa.

Waƙar da marubucin kuma mai fassara maganar kurame ɗan ƙasar Gabon, Paul Anicet Mounziegou ya rubuta, ta jinjina wa jajircewa, ƙauna da kuma shauƙin da Ibrahim ke da su a kan wasanni, a matsayin wani abu da ya ɗaukaka matsayinsa.

Shekaru biyu bayan rubuta waƙar, an naɗa Ibrahim, wanda lokacin yake riƙe da matsayin shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Kurame ta Gabon, ya shugabanci Hukumar Ƙwallon Ƙafar Kurame ta Ƙasashen Afrika.

Ibrahim kurma ne, amma zai yi wuya ka gano wata alama ta nadama tattare da ɗan shekaru 32 da haihuwar. Idan ma akwai wani abu, ya zaɓi ya rungumi ƙaddara, sannan yana gudanar da rayuwa ta ƙashin kansa da ta sana'arsa - cikakkiya ta kowanne fanni.

"Na zamo abin da na zama yau saboda himma, jajircewa da kuma goyon bayan iyalina da abokaina. Na yi imanin cewa kurumtata ba ta nuna ko ni wane ne, face, gogewata, kyawawan dabi'una da kuma mayar da hankali kan abin da nake muradi," Ibrahim ya faɗa wa TRT Afrika a wata rubutacciyar hira.

Yanke Shawara Mai Ƙarfi

Kalmar "kurma" na nufin wanda jinsa ya yi rauni sosai ko ya ɗauke gaba ɗaya tun daga haihuwa har zuwa ƙuruciya. Masu matsala wajen ji kuma a ɗaya ɓangaren, su ne waɗanda jinsu ya ragu sakamakon wani abu a wani lokaci a rayuwarsu.

"Yanayina bai hana ni samun ci gaba a aikina ba" Photo: TRT Afrika

Ibrahim ya rasa jinsa gaba ɗaya yana ɗan shekara tara da haihuwa. Amma bai yi ko-gezau ba, ya yi amfani da nakasar a matsayin zaburarwa ya inganta sauran gaɓɓansa. "Yanayina bai hana ni bunƙasa a aikina ba.

A maimakon haka, ya ingiza ni, na ƙara azama sannan kuma na shawo kan matsaloli. Ba a ba ni horo ba; na yi ƙoƙari na koyi abin da nake buƙata na rayu ba tare da dogaro da kowa ba," ya bayyana.

Ibrahim ya halarci makaranta tare da yara masu ji - a makarantar Lycée Panafricain d'Enseignement Général a Libreville.

"Ba abu mai sauƙi ba ne fama da larurar rashin ji, amma a kodayaushe ina ƙoƙari na yi abin da zan iya," ya labarta.

A shekarar 2009, shekaru Goma bayan an gano shi kurma ne, mutumin da yake ƙaunar taka leda ya gamu da aboki wanda shi ma kurma ne.

Tare da wannan abokin, Ibrahim ya koyi maganar kurame, abin da ya share masa hanyar shiga wata duniya da bai san tana wanzuwa ba.

" Ban san cewa akwai mutane irina ba. Lokacin da na gamu da kurame a Nzeng Ayong (wata gunduma a Libreville), na yi mamaki da kuma farin ciki da na gan su," ya ce.

Sababbin abokan hulɗa

Gundumar Nzeng Ayong da ke tsakiyar birnin Libreville, nan ne cibiyar ƙungiyar Kurame ta Gabon.

A nan ne Ibrahim zai gamu da marubuci Mounziegou kuma ya yi kyakkyawan tasiri a rayuwarsa. Yayin da Ibrahim ya bayyana ƙaunarsa ga ƙwallon ƙafa, abokansa sun ƙaru.

Ya ci gaba har ya kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa tare da wasu masu sha'awa a cibiyar. An kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kurame ta Gabon ƴan Shekaru daga bisani.

Yayin da Ibrahim ya bayyana ƙaunarsa ga ƙwallon ƙafa, abokansa sun ƙaru. Photo: TRT Afrika

"Lokacin da Ibrahim ya zo nan, mun ƙuduri aniyar mu kafa wata ƙungiyar da za mu bunƙasa harkokin wasanni gaba ɗaya, da kuma ƙwallon ƙafa musamman," Mounziegou ya tuno.

"Tun da muka haɗu, na gani ƙarara. Mun je Brazil, Kenya, sannan na himmar Ibrahim ta taimaka wa wasu. Mun yi tafiye-tafiye dadama tare. Mun je Brazil, da Kenya, da kuma a baya bayan nan, Malaysia domin halartar Gasar Cin Kofin Duniya ta Kurame, duk saboda ƙoƙarinsa."

Game da mu'amalarsa ta yau da kullum, Ibrahim ya ce mutanen da ba kurame ba suna mutunta shi. Wani lokaci yana lura da abin da ya kira "zumuɗi cikin mutuntawa".

"Waɗannan mutanen suna zumuɗin sanin wani abu game da kurumtata kuma a yawancin lokaci suna da ƙarfafa guiwa da nuna fahimta. Wani lokaci, abin takaici ne a kasa fahimtarka, amma ina jin daɗin ƙoƙarin da wasu ke yi don su yi sadarwa da ni," Ibrahim ya gaya wa TRT Afrika.

A matsayinsa na shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Kurame ta Afrika, yana ci gaba da bayyana ɓangarorin da za a iya kyautatawa game da mu'amala da mutanen da Kurame kuma bebaye ne ko kuma suna fama da ɗaya daga cikin waɗannan larurorin.

"Uwa uba, batu ne game da duba yiwuwar wayar da kai a kan rashin nuna wariya da samun biyan buƙata domin a taimaka a zamar da al'umma ta kowa da kowa," ya ce.

TRT Afrika