Tafiyar kwana 21 mai cike da wahala da Bakri Moaz ya tsere daga Sudan zuwa Kenya a watan jiya wato Yuli-Tafiyar tsira daga yankin da ake yaki da ya faro da ƙafa, daga baya ya hau mota, sannan a karshe ya hau jirgi- labari ne mai kama da wani tsararren fim na wanda ya tsira daga yaki.
Bayan watanni a cikin rikicin kafin ya yanke shawarar neman hanyar tsira daga kasar, dan Sudan din mai shekara 30 wanda yake da fasahar kirkira ya rayu cikin tashin hankali mafi muni a rayuwarsa.
Ya ga yaki ƙuru-ƙuru, ya ga yadda motocin yaki ke jefa bama-bamai a kusan kullum. A lokacin, a ko yaushe suna rayuwa ne cikin fargabar wa makara ke jira.
A daidai lokacin da rayuwa ta yi ƙunci, sai Bakri ya danne zuciyarsa ta hanyar neme wa kansa farin ciki ta hanyar zane-zane, inda ya riƙa amfani da fasaharsa wajen zayyana yadda yakin ke wakana da zimmar bayar da asalin labarin yakin daga zuciyarsa.
Gidansu Bakri ya kasance kusa da sansanin sojin Sudan, wanda hakan ya sa yake ko dai cikin aminci, ko hatsari duba da yanayin yadda rikicin ya zo da lokaci.
Idan sojojin za su iya kare harin da aka kawo ta kasa, ba za su iya kare hare-haren sama ba. An tarwatsa gidaje da dama a irin wadanann hare-haran na sama.
A cikin dan littafin nasa, Bakri ya bayyana yakin yadda mai fasahar kirkira ne kadai zai iya - ta hanyar amfani da zane da ke nuna fuskoki cikin damuwa da sauransu.
“Ina daukar dan littafina na zane-zane ne zuwa duk inda zan je. Na ji ne kawai akwai bukatar bayyana yadda yakin yake, da yadda ya yakin ya daidaita mu,” in ji Bakri a tattaunawarsa da TRT Afrika a lokacin da yake bayani a kan littafin nasa na Zayyanar Yaki, wanda ya tattara aikace-aikacensa wanda tuni ya kai Taron Baje Kolin Fasahohi a Jamus.
Yadda ya tsira
Sama da wata uku bayan ya isa kasar Kenya, sai Bakri yake tuna yadda ya auna arziki bayan ya kusa yanke ƙauna.
“Da kyar na samu na isa bodar Habasha bayan tsallake shingen sojoji da jihohi da dama na Sudan a kafa. Da na isa Habasha, sai na nemi biza zuwa Kenya, na shiga jirgi zuwa Addis Ababa, sannan na karasa zuwa Nairobi,” in ji shi.
Ko da Bakri ya isa Nairobi, ya riga ya gaji. Amma duk da gajiya ta kama shi, zuciyarsa a natse take. Akalla ya huta da jin karar harbe-harbe da bama-bama ba dare ba raba a garunsu na Al ‘Aylafun, da ke Gabas da Tekun Nile.
Bayan natsuwar da ya samu ta tsira daga kugin yaki, sai Bakri ya fara tunanin mahaifiyarsa da ’yan uwansa, wadanda suma sun tsere daga Al ‘Aylafun wata uku bayan shi lokacin da yakin ya kusa riskarsu.
“Ban san ina suke ba yanzu tun bayan da suka tafi. Amma ina fata suna lafiya. Ina nan ina tsammanin kiransu, su fada min cewa suna lafiya,” in ji Bakri.
Littafin zane-zanensa
A lokacin da yake tafiyar tsira, Bakri ya cigaba da zane a cikin dan littafinsa kan abubuwan da za su iya kawo sauyi a Sudan.
“Ba wai zane ba ne kawai, zan iya yin rubutu a ciki-Rubuta fahimtata, aikace-aikace da ma komai. Haka kuma akwai lambobin waya a ciki,” kamar yadda ya bayyana wa TRT Afrika.
“Ina tunanin akwai alaka mai karfi tsakanina da dan littafina. Ina kewar littafin yanzu aka baje kolinsa. In Allah Ya yarda za su kula min da shi zuwa lokacin da zai dawo gare ni.”
Bakri ya yi amannar cewa kalilin ne daga wajen kasar Sudan suka fahimci irin illar da yakin ya yi wa kasar. Sai dai yana farin cikin yadda hotunan da ya zana a lokacin da yake rayuwa a cikin fargaba zai taimaka wajen fahimtar da mutane tsananin da mutane Sudan suke ciki.
“Ina da yakinin cewa duk abin da ka yi domin Allah, Allah zai bayyana shi a duniya,” inji shi.
“Don haka, a lokacin da aka bukaci in kawo littafin a gabatar da shi a taron Baje Kolin Fasahohin Kirkira a Jamus a ranar 4 ga Oktobba, sai na ji burina na cika.”
Duk da cewa Bakri bai samu halartar taron ba saboda matsalar biza, tunanin aikinsa ya kai idon duniya kadai ya sa yake jin burinsa ya cika, amma a daya bangaren kuma yake sanyaya masa gwiwa.
Ƙaryata farfaganda
Bayan bayyana asalin abin da ke faruwa a kasarsa, wadda take ta fama da yaki tun 15 ga Afrilu, Bakri ya kuma ce fasararsa za ta taimaka wajen bayyana wa duniya asalin abin da ke faruwa domin a daina musu mummunar fahimta a game da yakin.
Bakri ya ce bangarorin da suke yakin suna amfani da kafafen sadarwa wajen farfaganda domin samun goyon baya a cikin gida da kasashen waje.
“Ba za ka wanke kowane bangare ba. Dukkan bangarorin na da laifi,” in ji shi.
Bakri ya ce yana da tambaya ga dukkan bangarorin biyu. “Zan so in tambaye su, “Me ya sa? Babu wanda zai yi nasara a wannan yakin. Zai fi kyau a tsagaita kawai.”
Kafin ya bar Sudan, Bakri ya shirya taron baje koli shi kadai mai suna “Behind the Wheel’, taken da karin magana ce da aka tsara domin nuna cewa duniya juyi-juyi ce.
“Wasu lokutan abubuwa marasa kyau suna faruwa, amma suna wucewa. Babu abin da yake dauwama. Don haka da yardar Allah da sannu abubuwa masu kyau din suka maye gurbin marasa kyau din.
Watakila watarana mu koma Sudan mu gyarata ta dawo daidai,” inji shi a lokacin da yake bayyana wa TRT Afrika burinsa na ganin yakin ya zama sanadiyar sauya kasar, wadda ke Arewacin Afrika.
Da baiwar zane aka haife shi
Tun yana karami Bakri ya fara zane, wanda ya samo asali ne da yadda mahaifiyarsa ta fahimci yana da sha’awar zane-zanen da fenti.
“Idan za mu ziyarci abokai, mahaifiyata takan ce in yi zane mu kai su a matsayin kyauta,” in ji Bakri, sannan ya tuno lokacin da mahaifiyarsa ta umarce shi ya yi zane a duk wani bangon da ke gidansu da fenti.
A situdiyonsa mai daki daya ‘Zen da ke Nairobi, duk da cewa bai kai girma da kyawun na Khartoum ba, inda yake iya tsara kowane irin taron baje koli da wakoki, duk da haka yana cigaba da gungurawa.
Da kayan aikinsa teburinsa, Bakri ya cigaba da zayyana yadda yakin yake da yadda Sudan take ciki. Aiki ne me mai wahala zana hali da bukatun da kasar da yaki ta tarwatsa ke bukata.