A ranar Talata da marece ne wani harin sama da Isra'ila ta kai ya faɗa kan Asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza. Hoto: AA

A ranar Talata da marece ne wani harin sama da Isra'ila ta kai ya faɗa kan Asibitin Al Ahli Arab da ke Gaza, ina da Falasɗinawa fararen hula 500 suka mutu, ciki har da mata da yara, a cewar Ma'aikatar Lafiya ta Falasɗinu a yankin da aka yi wa ƙawanyar.

Ba ɗaruruwan majinyatan da suka ji raunuka a hare-haren baya ne kawai a kwance a asibitin, wanda ake tafiyar da shi ƙarƙashin jagoranci ƙungiyar agaji ta Kiristoci ba, a lokacin da aka kai harin, akwai kuma ɗaruruwan mutanen da suke samun mafaka a wajen a matsayin tudun-mun-tsira sakamakon rasa muhallansu da suka yi.

Tun bayan mummunan harin wanda ake kallo a matsayin laifin yaƙi, Isra'ila ta fitar da bayanai daban-daban na abubuwan da wataƙila suka faru.

Da fari, rundunar sojin Isra'ila ta ce mayaƙan Falasɗinawa ne suka fake a asibitin wajen harba rokoki, inda ita kuma Israi'la ta ce makamai masu linzaminta mai yiwuwa suka daki asibitin ba da gangan ba.

A yanzu dai, an sauya zancen inda ake nuna yatsar zarin a kan ƙungiyar mayakan sa kai da ke da'awar Jihadi ta Falasɗinawa (PIJ). Isra'ila ta zargi PIJ da harba roka daga wata maƙabarta da ke kusa da asibitin inda ta faɗa cikinsa.

Amma ƙwararru da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗa'adam a baya sun sha yin bincike a kan ire-iren waɗannan ikirari na Isra'ila inda suka gano cewa ƙarya ne, har ma da ƙaryata bayanan da ke cewa Hams da PI na amfani da fararen hula a matsayin kariya.

Tel Aviv tana amfani da manyan makamai a kan mayaƙan Falasɗinawa waɗanda suka dogara da amfani da ƙananan makamai da kuma rokoki ƙirar hannu don kai wa Isra'ila hare-hare.

"A yanayi irin wannan ko da mun gaskata ɓangaren Isra'ila, ko da an ce to mun ji, kun yi daidai akwai mayaƙa kaɗan a asibitin da suke harba rokoki, to dai kun kashe mutum 500, 500 da ba su ji ba ba su gani ba," a cewar Neve Gordon, wani farfesa na shari'ar ƙasa da ƙasa da ƴancin ɗan'adam a Jami'ar Queen Mary da ke London.

"Tsarin daidaito bai yarda ka aikata hakan ba."

Isra'ila ta sha nanata cewa tana kai harin da Amurka ke mara mata baya a Gaza ne saboda masu kai mata hari na sajewa a cikin fararen-hula, duk kuwa da cewa ko kayan amfanin yau da kullum ma sai dai a yi fasa-ƙwaurinsa cikin Gazan wanda ke da mutum fiye da miliyan biyu a tsawon shekara 17.

A lokacin yaƙin da Isra'ila ta yi a Gaza a watan Mayun 2021 da ya yi sanadin mutuwar falasɗinawa 260, ciki har da yara 66, Tel Aviv ta zargi Hamas da sauran ƙungiyoyin kan yawan mace-macen da aka samu.

A lokacin da ayyukan jinƙai ke yin muni a Gaza, ana son dole sai ƙasashen duniya sun yarda da labarin da Isra'ila ta kitsa tun da ita ce ke da ikon bai wa masu bincike masu zaman kansu da ma'aikatan agaji damar shiga yankin da ke gaɓar teku wanda Falasɗinawa ke so ya shiga cikin ƙasar da suke muradin samu a nan gaba.

A ranar 16 ga watan Mayun 2021, sojojin Isra'ila suka kai hari Titin Al Wahda da ke Gaza, inda ya lalata gine-gine da dama da hallaka fararen hula 44.

Isra'ila ta yi gaggawar ikirarin cewa ta kai harin ne da nufin samun maɓoyar Hamas da ke hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da kuma cibiyar mayaƙanta. Amma wani binciken Ƙungiyar Kare Hakkin Dan'adam ta Human Rights Watch (HRW) bai gano wata hujja da ke goyon bayan zargin ba.

"Rundunar sojin Isra'ila ba ta gabatar da wasu bayanai da ke nuna cewa akwai irin waɗannan hanyoyin na ƙarƙashin ƙasa ko kuma cibiyar mayaƙa ba a wannan yankin, kuma ba ta nuna cewa ribar da sojojin suka yi hasashen samu daga hare-haren ta fi munin abin da aka tsammaci zai samu fararen hula da dukiyoyinsu ba," kamar yadda HRW ta rubuta a wani rahoto a lokacin.

Wannan ba shi ne karon farko da Isra'ila take yin wannan ikirari ba.

Bayan yakin Isra'ila da Gaza na 2014, binciken Amnesty International bai iya fayyace ikirarin Isra'ila na cewa ana amfani da gine-gine da suka hada da makarantu wajen kaddamar da hare-haren roka na 'yan bindiga ba.

Ga misali, dakarun Is'ra'ila sun rusa asibitin Al Wafa gaba dayansa, wanda ke Shuja’iyyeh, bayan sun yi ikirarin ana amfani da shi wajen harbo makamin roka. Amma Amnesty ta ce ba ta iya samo hujjar da za ta tabbatar da maganar Isra'ila ba.

Da wannan ikirari na amfani da mutane wajen garkuwar hari, a baya Isra'ila ta kai harin bam kan kadarorin al'umma kamar tashar lantarki tilo ta Gaza, wanda ya janyo gallazawa rayuwar mutanen Falasdinu.

Gordon ya ce, “Batun cewa ana amfani da mutane a matsayin garkuwa batu ne sananne, kuma an yi hakan sau da dama a Isra'ila da Sri Lanka da ma sauran wurare, don ba da hujjar kashe farar hula.

Abin kenan sai kawai ka ayyanu a matsayin garkuwa, kawai don an harba roka kusa da asibiti ba ya nufin asibitin ya cancanci hari.”

Ya ce "abin da Isra'ila ta yi "laifukan yaƙi" ne.

TRT World