Kasar Falasdinu a baya tana daga cikin Daular Usmaniyya a sama da shekaru 100 da suka wuce. A lokacin Yakin Duniya na Daya, wanda shi ne lokacin da Daular ta rage ƙarfi sannan ta rushe, wanda daga baya ta zama Jamhuriyar Turkiyya, sai Birtaniya ta ƙwace iko da ita.
A 1917, a wata wasiƙa da Arthur James Balfour wanda shi ne sakataren harkokin wajen Birtaniya ya rubuta wa Lionel Walter Rothschild, ya goyi bayan "samar da matsuguni ga Yahudawa" a Falasdinu, wanda hakan ya bude ƙofa ga Isra'ila.
Shawarar da kuma Balfour ya bayar ya kuma yi kira da a kare Larabawa inda ya ce "babu abin da za a yi wanda zai saba wa hakkokin farar hula da addinin al'ummomin da ba Yahudawa ba," duk da cewa bai sanar da ra'ayinsa na siyasa ko kasa ba.
A lokacin da Birtaniya ta fara mayar da Yahudawa zuwa Falasdinu, adadin Yahudawa kaso tara ne kadai cikin 100 a Falasdinu. Bayan da Yahudawa da ke Turai suka soma komawa can a ƙarƙashin amincewar Birtaniya, sai adadin ya ƙaru zuwa kusan kaso 27 na adadin a 1922 da 1935.
Kafa Isra'ila
Irin kisan kiyashin da aka yi wa Yahudawa a lokacin Yakin Duniya II a Turai a shekarun 1940 ƙarƙashin mulkin Hitler ya zama daya daga cikin manyan dalilan da ya sa suka yi hijira zuwa Falasdinu.
Wannan ya faru ne duk da cewa a 1939, Birtaniya ta saka doka kan cewa adadin Yahudawa masu hijira zuwa Falasdinu a duk shekara kada ya wuce 10,000.
Bayan Yakin Duniya na biyu, Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya ya cimma matsaya inda ya nemi a raba Falasdinu gida biyu tsakanin Larabawa da Yahudawa a ranar 29 ga watan Nuwambar 1947. Wannan ne ya bayar da dama aka kafa kasar Isra'ila.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Isra'ila a ranar 14 ga watan Mayun 1948 bayan umarnin da Birtaniya ta bayar kan Falasdinu ya kawo ƙarshe, Majalisar Jama'ar Yahudawa sai ta hadu a gidan tarihin Tel Aviv, inda ta bayyana kafa kasar Isra'ila.
Amurka ta amince da ƙasar a daren da Yahudawan suka kafata sannan ƙungiyar USSR bayan kwanaki uku.
Yakin shekarar 1948
Kirkiro Isra'ila ya yi sanadin yin babban yaƙi tsakanin Isra'ila da kasashen Larabawa masu maƙwaftaka, yaƙin da Isra'ila ta yi nasara, inda ta ƙara fadada kasar fiye da yadda take baya.
Falasdinu tana kiranta da "al Naqba," wanda hakan ke nufin "bala'i", a daidai lokacin da nasarar da Isra'ila ta samu ta jawo Falasdinawa 700,000 suka rasa muhallansu.
A tsakanin 1949 da 1960, Yahudawa har miliyan daya masu gudun hijira da karin 250,000 wadanda suka guje wa kisan kiyashi sun gudu zuwa Isra'ila, kamar yadda BBC ta ruwaito.
Kafa kungiyar PLO
A 1959, Yaser Arafat da abokansa sun ƙaddamar da Fatah, wadda ƙungiya ce ta 'yan turjiya a Falasdinu a Kuwait, wadda karamar kasa ce a yankin Gulf domin nuna turjiya ga mamayar Isra'ila.
A 1964, Arafat da sauran shugabannin Falasdinu sun yanke hukuncin hada kai domin kafa kungiyar PLO domin kafa kungiyar hadin kai domin yakar Isra'ila.
Yakin Larabawa da Isra'ila
A shekarar 1967, yakin da aka yi na kwanaki shida ya ɓarke ne a tsakanin Isra'ila da Masar da Jordan da Syria.
Isra'ila ta samu nasara inda ta kama gabashin Birnin-Kudus, da Gabar Yamma da Kogin Jordan da Zirin Gaza da Tuddan Golan da yankin Sinai.
Peter R Mansoor, wanda yake rubutu ga Cibiyar Hoover ya bayyana cewa, "Duk da Tuddan Golan da akasarin Gabar Yamma da Kogin Jordan na karkashin ikon Isra'ila, amma duk da haka Isra'ila ta mayar da yankin Sinai ga Masar a matsayin wani bangare na yarjejeniyar Camp David a 1978 da kuma barin wuraren Isra'ila da ke Gaza a 2005."
Yakin 1973
A shekarar 1973, an sake yin wani yaƙin, wanda shi ne yaƙin Larabawa da Isra'ila a watan Oktoba.
Masar da Syria sun gwabza yaki a lokacin hutun addini na Yom Kippur (6 ga Oktobar shekarar).
Jawabin Yasser Arafat a Majalisar Dinkin Duniya
A wani jawabi da ya yi ga Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar 13 ga watan Nuwambar 1974, shugaban PLO na lokacin Yasser Arafat ya yi watsi da lakabin da aka yi na " 'yan ta'adda" ("in ba haka ba, da Amurkawa a gwagwarmayar 'yantar da kansu daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya, da sun kasance 'yan ta'adda; da kuma yadda Turawa suka yi tsayuwar daka kan 'yan Nazi da ya zama ta'addanci") inda ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta yi kokarin wanzar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
"A yau, na zo dauke da icen zaitun a hannu daya, da kuma bindigar mai fafutikar neman 'yanci a dayan hannun. Kada ku bari reshen zaitun ya fadi daga hannuna
Boren Falasdinawa a karon farko
Boren da Falasdinawa suka soma a karon farko ya soma ne bayan abin da Isra'ila ta kira kuskure inda Falasdinawa a nasu bangaren suka kira shi tsokanar fada: "A ranar 8 ga watan Disamabar 1987, wani dan kama wuri zauna na Isra'ila Herzel Boukiza ya banke wasu ma'aikata Falasdinawa wadanda suke komawa gida a shingen binciken Erez/Beit Hanoun.
An kashe ma'aikata hudu daga Jabalya da Maghazi a Gaza a harin ta'addanci.
Daga nan aka soma zanga-zanga da tarzoma; wanda yakin ya kawo karshe bayan an saka hannu kan "yarjejeniyar Accord".
Yarjejeniyar Oslo
A Oktobar 1991, Sifaniya ta shirya wani taron zaman lafiya a Madrid da hadin gwiwar Amurka da USSR. Sifaniyar ta tara wakilai daga Isra'ila da Lebanon da Syria da Jordan da Falasdinu. An ci gaba da wannan tattaunawa a Washington da Moscow a 1992.
Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta bayyana, "Zuwa 1993, ba a cimma matsaya kan tattaunawar da aka yi a Washington ba, inda tattaunawar sirri ta Isra'ila da Falasdinu da kuma Isra'ila da Jordan suka sha gabanta, lamarin da ya samar yarjejeniyar Isra'ila da Falasdinu wadda ake kira yarjejeniyar Oslo.
An yi ta ne Satumbar 1993 sai kuma yarjejeniyar Isra'ila da Jordan Oktobar 1994.
A 1993, Firaiministan Isra'ila Yitzhak Rabin da shugaban kungiyar PLO ta Falasdinu Yasser Arafat sun saka hannu kan yarjejeniyar Oslo.
Bayan shekara guda, sai Arafat ya kafa wata hukuma ta Falasdinawa bayan Isra'ila ta fita daga akasarin Gaza da birnin Jericho na Gabar Yamma da Kogin Jordan.
A 1994, Jordan da Isra'ila sun saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Oktoba, inda a watan Disamaba, Rabin da Arafat da Shimon Peres suka zama wadanda suka ci gasar Nobel
Kisan Rabin
An kashe Yitzhak Rabin daga baya a 1995, inda wani mai tsatsauran ra'ayi dan Isra'ila ya kashe shi, wanda hakan ya sa Peres ya zama Firaiminista.
Yin bita kan littafin Dan Ephron na New Yorker, Dexter Filkins ya rubuta cewa: "A lokacin da taron Oslo ya yi zafi, [wanda ya kashe Rabin wato Yigal] sai Amir ya zama ya gamsu kan cewa Rabin na kokarin cin amanar Isra'ila kuma musamman masu kama wuri zauna; sai ya shirya gangami a yankunan da aka mamaye domin yin watsi da yarjejeniyoyi inda har ya yi kokari kafa dakarunsu."
Boren Falasdinawa a karo na biyu
An yi bore a karo na uku tsakanin shekarar 2000 da 2005 kuma ya kasance mafi muni fiye da na farkon. Yarjejeniyar zaman lafiya ta wargaje inda Isra'ilawa da Falasdinawa sun zama suna jin haushin juna.
Zack Baauchamp, wanda ke yi wa Vox rubutu, ya kara da cewa zuwa lokacin da aka kawo karshen boren na biyu [bangaren da ke neman zaman lafiya na Isra'ilawa wanda ke cewa ya kamata a biya Isra'ila lada kan hakura da matsuguninsu domin zaman lafiya sai ya zama bai da wani tasiri.
Shakku kan shirin samar da zaman lafiya ya karu, lamarin da ya dagula yunkurin da ake yi a nan gaba na cimma yarjejeniyar da kasashen biyu."
Cibiyar Nazarin Gabas ta Tsakiya wato IMEU ta ruwaito kungiyar kare hakkin bil adama ta B'Tselem inda ta yi lissafin cewa tsakanin shekarar 2000 zuwa lokacin da aka soma shirin Operation Cast Lead a Disambar 2008, dakarun tsaron Isra'ila sun kashe Falasdinawa 4878 inda Falasdinawan suka kashe 'yan Isra'ila 1063.
Amincewar Amurka ga Isra'ila
A Satumbar 2016, Amurka ta saka hannu kan yarjejeniyar taimakon soji ta shekara 10 ga Isra'ila wanda hakan ke nufin za ta kashe kudin da suka kai dala biliyan 38.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, wannan yarjejeniyar ita ce irinta mafi girma a duniya .
A 2017, Donald Trump ya amince da Birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila. lamarin da ya sa Falasdinawa ba su ji dadi ba.
A Maris din 2018, Trump ya wallafa wani sako a shafin Twitter inda ya ce: "Bayan shekara 52, lokaci ya yi ga Amurka ta amince da ikon Isra'ila kan Tuddan Golan, wanda hakan yana da matukar amfani ga tsaron Isra'la da yankin!"
Duk da cewa Turkiyya da sauran kasashen duniya sun yi Allah wadai da hakan, Isra'ila ta ci gaba da gina wasu wurare ga 'yan kama wuri zauna a wuraren da suka mamaye bayan da Trump ya bayar da sanarwa.
Yarjejeniyar 'Trump ta karni'
An ci gaba da rikicin Isra'ila da Falasdinu baki daya a 2018. A 2019, an gudanar da zabuka da dama a Isra'ila sai dai ba a samu wani wanda ya yi nasara ba tsakanin Benjamin Netanyahu da Benny Gantz, wanda hakan ya yi sanadin aka tafi zabe na uku a Maris din 2020.
Zuwa wannan lokacin, Shugaban Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin Netanyahu da Gantz a White House kafin ya bayyana shirinsa na wanzar da zaman lafiya na Mideast Peace Plan.
Falasdinu ta fito fili ta yi watsi da wannan shirin, da kungiyar Tarayyar Kasashen Larabawa da Kungiyar Hadin Kan Musulunci ta OIC.
'Yarjejeniyar Karni', kamar yadda Trump ya kirata, ana kallonta a matsayin ta rashin hikima wanda kuma ta sa Falasdinu ta yi sarandar 'yancinta domin neman taimakon kudi, wanda hakan ya kuma kawo karshen shirin samar da kasa biyu.