Daga Murat Sofuoglu
Harin da ƙungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila a wani lamari da ba a taɓa ganin irinsa ba, ya nuna yadda Tel Aviv ta gaza kare kan iyakarta da yankunan Falasɗinu mai cike da matsala.
Harin nuna ƙarewa da ƙungiyar Hamas ta kai ya matuƙar bai wa Isra'ila da ƙawayenta mamaki, lamarin da ya jawo wasu jami'ai suke tunanin cewa ba zai yiwu a ce wata ƙungiya a karan-kanta kaɗai ta kai irin wannan harin ba, sai dai idan wata ƙasa mai ƙarfi ta taya ta.
Jami'an leƙen asiri na ƙasashen yammacin duniya da masu sharhi na nuna yatsar zargi a kan Iran kan taimakon Hamas da ta yi wajen karya lagon ƙaƙƙarfar rundunar sojin Isra'ila.
Amma, in baya ga kalaman goyon bayan da ta saba yi, Iran ta yi watsi da cewa tana da hannu a harin da Hamas ɗin ta kai.
"Kun yi matuƙar sanya al'ummar Musulmai farin ciki kan wannan aikin basira da ya yi nasara," a cewar shugaban ƙasar Iran Ebrahim Raisi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran IRNA ya rawaito.
Hamas ta kuma yi watsi da batun cewa tana da hannu a harin da aka yi wa laƙabi da “Operation Al Aqsa Storm”, wanda “wani mataki ne da Falasɗinu da Hamas suka ɗauka”,a cewar wani babban jami'i na ƙungiyar, Mahmoud Mirdawi
Amma a wata maƙala da Mujallar Wall Street Journal ta wallafa da take ambato “manyan jami'an Hamas da Hezbollah”, wata ƙungiyar Shi'a da Iran ke goyon baya a Labanon, ta yi ikirarin cewa "Jami'an tsaron Iran sun taimaka wajen shirya harin da Hamas ɗin ta kai.
"Yana da matuƙar wahala a yi magana a kan ainihin irin rawar da Iran ta taka a yaƙin jajircewa da Hamas ke yi yanzu a haka a Falasɗinu. Hamas da Iran suna da daɗaɗɗen tarihin ƙawance mai kyau," kamar yadda Ramzy Baroud, wani mawallafi dan Falasɗinu kuma mai sharhi kan al'amuran siyasa ya shaida wa TRT World.
Duk da cewa Iran ta fi kusanci sosai da Ƙungiyar masu da'awa da fafutukar Jihadi ta Falasɗinu wato Palestinian Islamic Jihad (PIJ), wacce Iran ke goyon baya, dangantakar Hamas da Tehran tana ƙara ƙrfi sosai a shekarun baya-bayan nan.
Hakan ya faru ne sakamakon alaƙar da ke tsakanin Hamas da ƙungiyar Hezbollah ta Labanon.
Amma ƙungiyoyin biyu ba su taɓa zama ƙut da ƙut da juna ba.
A lokacin Yakin Basasar Syria a shekarun baya, Hamas ta goyi bayan ƙungiyoyi masu hamayya da Gwamnatin Bashar Assad ne, wadanda mafi yawansu 'yan Sunni ne, alhali shi kuma Assad din yana samu goyon bayan Iran, wanda hakan ya kawo sabani tsakanin kungiyar ta Falasdin da Iran.
A shekarar 2017 ce suka dinke barakar da ke tsakaninsu lokacin da Assad wanda yake samun goyon bayan Iran da Rasha ya fara cin galaba a yakin.
"Abin da ya faru a ranar Asabar 7 ga Oktoba ya kara tabbatar da dinkewa tsakanin Hamas da Iran da Hezbollah. Abin da hakan ke nufi shi ne Hamas ta sake komawa cikin hadakar 'yan tawaye ta yankin Gabas ta Tsakiya," in ji Baroud.
Hadakar 'yan tawayen Gabas ta Tsakiya wata hadakar harkokin siyasa da soji ce tsakanin Iran da Gwamnatin Assad da Hezbollah da sauran masu adawa da Amurka da Isra'ila da suka fito daga kasashen Iraki da Yemen da Syria.
Duk da cewa Iran ta ce ba ta da hannu a harin na Hamas, lallai da wahala a tsame hannun kungiyoyin Hezbollah da PIJ, wadanda duk suke samun goyon bayan Iran a hare-haren na Hamas a Isra'ila kamar yadda Baroud ya bayyana.
Aion Liel, tsohon Darakta Janar na Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Isra'ila ya bayyana cewa ya yi amannar akwai sa hannun Iran a hare-haren. "Mun yi amannar cewa makiyarmu babbar kasa ce, ba wai wata 'yar kungiyar 'yan bindiga ba," inji Liel a lokacin da yake kwatanta Iran.
"Ba ni da wata hujja, amma hare-haren 7 ga Oktoba sun girmama kuma sun munana," inji Liel a tattaunawarsa da TRT Afrika.
"Babu yadda za a yi Hamas ta shirya tare da kai wadannan hare-haren tare da gudunmuwar Hezbollah da PIJ, amma kuma a ce Iran ba ta da masaniya. Dole sai sun sanar da Iran," in ji Baroud.
Wace irin rawa Iran ta taka a hare-haren na Hamas? ko hakan zai kara rura wutar rashin fahimta da zaman tankiya ko a'a? Sannan ko yaya shirin Iran na fuskantar abin da ka iya dawowa daga Amurka da Isra'ila?
Duk wadannan wasu tambayoyi ne da za a ga amsoshinsu nan da wasu 'yan kwanaki ko makonni da suke tafe inji Baroud.
"Babu makawa akwai sa hannun Iran a hare-haren na Hamas, sannan kuma akwai alamar suna shirya wani wanda ya fi wanda aka gani girma."
Isra'ila da abubuwan da kasashen Yamma suke fada
Isra'ila ba ta da hujjar tabbatar da sa hannun Iran a hare-haren, inda ta bayyana cewa har yanzu ba ta kammala gamsuwa ko akwai sa hannun Iran ko babu ba a wajen "tsarawa da horar da Hamas wajen kai musu hare-haren.
Antony Blinken, Sakataren Gwamnatin Amurka ya bayyana a game da yiwuwar sa hannun Iran cikin hikima cewa, "Ba mu ga wata hujjar da take nuna sa hannun Iran ba, ko kuma ta dauki nauyin wani hari, amma lallai akwai tsohuwar alaka," in ji shi.
Wasu masana na kasashen Yamma sun bayyana yakininsu cewa hare-haren na Asabar, wadanda aka nuna kwarewa matuka a ciki wajen aikawata ba zai yiwu ba, ba tare da taimakon wata kasa ba.
Wani masani a kan harkokin kungiyoyin 'yan bindiga masu samun goyon bayan Iran, Michael Knights ya bayyana wa kafar Washington Post cewa akwai alamar "an tsara kai wadannan hare-haren' ne a wani wajen daban.
Ba zai yiwu a kai hare-hare a wurare tsararru masu daraja irin wadannan ba hakanan ba tare da wani shiri na musamman ba."
Masana sun yi amannar cewa wasu rokokin Hamas daga Iran din suka taso. Hamas ta aika akalla rokoki 5,000 a biranen Isra'ila, wanda hakan ya nuna karfin makamansu.
Amma a daya bagaren kuma, wasu masanan sun bayyana cewa ba su ga wata hujjar da take alakanta Iran da hare-haren ba, inda suka ce zai yi wahala mayakan Hamas su iya fita daga Gaza inda suke samun horo na musamman, su tafi wasu kasashen.
Abin da ya sa Isra'ila ke shan wahala wajen yakar kungiyar Hamas shi ne rashin sanin gamsasshen bayani da tsari tafiyar da kungiyar, kamar yadda Bruce Riedel, wani tsohon masanin yaki na Hukumar CIA, kuma babban mai bada horo a Cibiyar Brookings.
"Wannan yaki ne tsakanin Hamas da Isra'ila, amma Iran take taimakon Hamas, amma ita Hamas din ce take yakin," kamar yadda Riedel ya bayyana wa kafar Washington Post. Haka kuma Riedel ya ce yana da yakinin cewa babu 'mashawartar' Iran a Gaza.
Yoram Schweitzer, wanda wani tsohon ma'aikacin leken asirin Isra'ila ne da yake shugabantar bangaren ta'addanci da kananan yake-yake a Cibiyar INSS, wadda wata cibiyar ƙwararru ce ta Isra'ila, ya bayyana wa TRT a shekarar 2021 a wata tattaunawar da ta yi shi cewa Hamas tana zaman kanta ne.
Duk da cewa Iran da Hezbollah "na son nuna" alaƙarsu da Hamas, ita kungiyar ta Falasdin, "tana yawan nuna cewa zaman kanta take yi wajen yanke shawarwari," in ji Schweitzer, sannan ya ƙara da cewa, "Hamas ba ta shiga lamuran Iran ko na Hezbollah ba."
Yunkurin samun Shweitzer domin karin haske a kan wannan tarihin bai cimma ruwa ba, domin yana shirye-shiryen shiga cikin sojojin ko-ta-kwana na Isra'ila, wanda hakan ya sa ba zai samu damar yin magana ba.
Yana cikin mutum 300,000 da sojojin Isra'ila suka kira, wanda shi ne mafi girma da kasar ta taba tarawa tun a shekarar 1948.