An haska totocin Amurka da Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain a bangon katangar tsohon garin Jerusalem ranar 15 ga Satumba, 2020 don nuna goyon baya ga shirin daidaitawar Isra'ila da kasashe biyu na Larabawa. / Hoto: AFP

Daga Kubra Solmaz

Ruwan bama-bamai da Isra'ila take ba ƙaƙƙautawa kan Gaza, wanda tuni ya hallaka dubban Falasdinawa farar hula, yana tunzura al'ummar Gabas ta Tsakiya, kuma yana kawo cikas kan shirin daidaitawa tsakanin Isra'ila da kasashen Larabawa.

Masharhantan da suka tattauna da TRT World sun ce, duk wata nasara da aka samu don cimma daidaitawa tsakanin Isra'ila da kasashen Larabawa za ta iya samun babban koma baya, amma ba za ta kai ga salwanta ba.

“Cikin dabara, su (kasashen Larabawa) za su so su ci gaba da wannan alaka, amma yanzu za su bukaci rage saurin daidaitawar, saboda tsoron fushin al'umma a cikin gida,” in ji Joost Hiltermann, daraktan kungiyar International Crisis group, yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.

Ya jaddada cewa kasashen Larabawa ba dole su dakatar da alaka da Isra'ila gaba daya ba, amma za su bukaci daukar salon ƙin bayyana batun a fili, kamar rage yawan haduwa, misali ta yawon shaƙatawa.

Tarihin daidaitawa

Daidatawar Isra'ila da wata kasar Larabawa ta fara ne da Masar a shekarar 1979, daga nan kuma sai Jordan a shekarar 1994.

Mehmet Rakipoglu, shugaban nazarin ilimi a cibiyar Dimension for Strategic Studies, ya ce Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yana matukar ganin girman shirin daidatawar da ke gudana.

A yanzu ana dab da samun karin wata kasar mai karfi a yankin wato Saudiyya, saboda duk wata nasarar samun wata kasar Larabawa tana taimakawa shugaban na Isra'ila ya ƙara kwarjini.

Rakipoglu ya ce, “Sugabannin Isra'ila da suka yi nasarar daidaita alaka a shekarar 1979 da 1994 sun cimma matsayin gwaraza a siyasar kasar. Kenan, daidaitawa da Saudiyya wani babban buri ne ga Netanyahu".

Wani mai sharhin siyasa na Isra'ila, Nimrod Goren, kuma shugaban cibiyar Mitvim Institute, mai nazarin dabarun tsare-tsare a Isra'ila, ya bayyana cewa, “Yarjejeniyar Abraham Accords tana cikin manyan nasarorin Netanyahu, sannan ya sha ambatar cewa daidaitawa da Saudiyya wata babbar nasara ce ta harkokin waje ga gwamnatinsa.”

Yarjejeniyar Abraham Accords

Shekara uku baya, a 2020, Amurka ta assasa kafa wata yarjejeniya tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain, da kuma Isra'ila, inda suka ƙudurci daidaita alakarsu. A watannin da suka biyo bayan sa-hannu da kasashen biyu na Musulmai suka yi, Maroko da Sudan sun shiga yarjejeniyar.

Rakipoglu ya ce, amma daidaitawa karkashin yarjejeniyar Abraham Accords da kuma shirin daidaitawa da Saudiyya sun bambanta daga wadda ta faru da Masar da kuma Jordan a baya.

Ya bayyana cewa, “Dalilin shi ne gwamnatocin Masar da Jordan sun nemi daidaitawar ne bayan [gazawa] a yaƙe-yaƙensu. Amma kuma, idan aka zo batun matakan daidaitawar kwanan nan, Amurka ce ke izawa, kuma kasashen Larabawa suna nuna taka tsantsan saboda damuwarsu kan al'ummominsu da ke goyon bayan Falasdinawa".

Yayin da Rakipoglu yake kallon illar shigar Amurka a wannan tattaunawa, Goren ya ce, “Shigar Amurka batun a yanzu zai karfafa damar cigaba da alaka tsakanin Isra'ila da Larabawa, da kuma ta hanyar bin kasashen Larabawa a kokarin daidaita lamarin kafin daga bisani a nemi mafitar zaman lafiya.”

Tattaunawar daidaitawa tsakanin Saudiyya da Isra'ila

Saudiyya, a dayan bangaren, ba ta shiga yarjejeniyar Abraham Accords da Amurka ta sasanta yi ba sai a 2020. Amma kuma, wannan shekarar a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, Saudiyya da Isra'ila sun nuna alamun yiwuwar daidaitawa tsakaninsu.

A wata tattaunawa da tashar Fox News, Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman ya bayyana cewa tattaunawar da ke gudana tare da Isra'ila na nufin cewa yiwuwar daidaitawa tana ƙara “matsowa kusa a kullum.”

Yariman ya ce, “A wajenmu, batun Falasdinu yana da muhimmanci matuka. Muna bukatar warware wannan bangaren.”

Duk da cewa ba a samu sanarwa a hukumance ba daga Saudiyya ko Isra'ila, Reuters ta ruwaito cewa Saudiyya tana jinkirta shirin daidaita alaka da Isra'ila wadda Amurka ke sasantawa, a cewar majiyoyi biyu da suka san matsayar gwamnatin Saudiyya.

Goren ya nuna cewa Netanyahu zai so ya inganta wannan alaka amma a yanzu yana bukatar fifita martanin Isra'ila kan harin Hamas, ko da kuwa hakan zai haifar da komabaya a daidaitawar na dan lokaci.

A mahangar Isra'ila, cimma daidaitawa da Saudiyya yana da muhimmanci matuka, saboda zai nuna kafuwar kyakkyawar alaka da wata babbar kasar Larabawa mai fada-a-ji a duniyar Larabawa.

Rakipoglu ya ce, “Sharuddan Saudiyya na daidaitawa a bayyane suke: kafa kasar Falasdinu mai 'yanci da iyakokin shekarar 1967. Yana da muhimmanci a lura cewa Saudiyya ta jaddada wadannan bukatu ba tare da sassauci ba.”

A fahimtar Goren, yakin zai iya sa tafiyar ta baci, amma ba za ta sauya cigaban tafiyar ba.

“Bayan kura ta lafa, za mu saka ran ganin cigaba, ko daga Saudiyya wajen tattaunawa kan tsaro tare da Amurka. Lokacin da za a cimma daidaitawa a hukumance tsakanin Isra'ila da Saudiyya zai dogara kan me ke faruwa a fagen Isra'ila da Falasdinawa. Kowannensu zai iya daukar lokaci, amma ko da kafin nan, za a iya cimma wata nasara, sannan a karfafa alakar.”

Tun da Saudiyya ta tabbatar da yiwuwar daidaita alaka da Isra'ila karkashin sharadin kafuwar kasar Falasdinu mai 'yanci, Joost Hiltermann ya fassara yadda Isra'ila take kallon daidaitawa da Larabawa.

Ya ce “Ga Isra'ila, daidaita alaka da kasashen Larabawa yana da tasiri saboda ta wannan hanyar, suna fatan kawo karshen rikicinsu da Falasdinawa ba tare da sai sun ba su kasarsu mai 'yanci ba.

"Ta hanyar tallafin harkokin kudi daga kasashen Larabawa, suna fatan cimma zaman lafiyar tattalin arziki: wadda wata dama ce ga Falasdinawa su rayu amma ba tare da sun iya daukar matakan da za su shafi jin dadin rayuwarsu ba, irin na 'yan cikakkiyar kasa.”

Sai dai Rakipoglu ya jaddada muhimmancin sauran kasashen Larabawa da har yanzu ba su shiga tsarin daidaitawar ba, kamar Qatar da Kuwait. Su biyun a kullum suna daukaka batun kafa kasar Falasdinu bisa iyakokin shekarar 1967.

Me al'ummomin Larabawa suke gani kan batun daidaitawa

A masallatai da filayen kwallo da garuruwa a yankin Larabawa, masu goyon bayan Falasdinawa sun karu tun bayan hare-haren Isra'ila na baya-bayan nan kan Gaza, wanda ya janyo nuna goyon baya ga fafutukar Falasdinawa.

Daga Ramallah zuwa Beirut, Bagadaza zuwa Alkahira, mutane sun yi zanga-zangar goyon baya ta hanyoyi daban-daban kamar raba alewa, yin addu'o'i kan kariyar Falasdinawa, da nasarar fafutukarsu kan dadaddiyar mamayar Isra'ila.

Bisa rinjayen ra'ayi na al'umma, kasashen Larabawa suna nuna taka tsantsan wajen bibiyar tsarin cimma daidaitawa.

Rakipoglu ya nunar da cewa, “Da yawan kasashen Larabawa sun dade suna son daidaita alaka da Isra'ila. Amma nasarorin da Hamas ke samu a baya-bayan nan sun janyo jama'ar Larabawa sun takaita kokarin gwamnatocinsu game da batun daidaitawa.”

Idan aka juya kuwa, ya kuma nuna cewa sahihiyar daidaitawa tsakanin kasashen Larabawa da Isra'ila abu ne mai wahalar samuwa.

Masar da Jordan sun bi hanyar daidaitawa da Isra'ila bayan munanan yake-yake da suka barke a 1948 da 1967, tsakanin Larabawa da Isra'ila.

Amma kuma, za a iya kallon daidaitawa da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain a matsayin ba sahihiya ba, saboda da ma can suna da boyayyiyar alaka da Isra'ila, a bayan fage.

Wadannan kasashe ba su taba bayar da dakarun soji ga Falasdinu ba, ko ba da wani tallafin kudi na a-zo-a-gani ba.

Shigar Morocco a shirin daidaitawa za a iya cewa ya samo asali ne daga amincewar Amurka da ikon Morocco kan yankin Yammacin Sahara.

Rakipoglu ya nuna cewa, cikin bangarorin da suka saka hannu kan yarjejeniyar Abraham Accords, Sudan ita ce ta fi daukar hankali.

Gwamnatin riko ta Sudan ta shiga tsarin daidaitawar sakamakon matsin lambar Amurka, bisa alkawarin cire Sudan daga jerin kasashe masu daukar nauyin ta'addanci.

Sudan tana da matsayi mai daraja a idon kasashen Musulmi, saboda lokacin mulkin shekara 30 na Omar Bashir, Sudan ta kasance mai tallafawa Hamas, kuma ta taka babbar rawa wajen karfafa batun Falasdinu.

A cewar Rakipoglu, daidaitawa tsakanin Sudan da Isra'ila za ta iya haifar da mafi girman tasiri kan duniyar Larabawa.

Da yawan batun ya dogara ne kan ko Isra'ila za ta baro iyakar Gaza ko za ta zabi yin mamaya. Idan hotunan matattu da na ta'adi, da na yara cikin makara, suna ta fitowa daga Gaza, yunkurin daidaitawar zai fuskanci babban komabaya da zai yi wahalar shawo kai.

TRT Afrika