Dakarun Isra’ila sun sha kai hari Masallacin Kudus, na uku mafi tsarki a Musulunci, a lokutan azumin Ramadan.
Mun yi nazari game da muhimmancin Masallacin ga mabiya addinin Musulunci. Al Aqsa, ko Kudus, wanda ke nufin "mafi girma" ko "mafi daukaka" a harshen Larabci, masallaci ne da ke tsakiyar Birnin Kudus.
Musulmai mabiya kowacce darika suna matukar daraja shi baya ga masallatai biyu mafiya tsarki – da ke Makkah da Madina.
An ambaci Kalmar Al Aqsa a wurare da dama a cikin Alkur’ani mai tsarki. Misali, aya ta 17:1 a Suratul Al Isra tana cewa: “Tsarki ya tabbata a gare Shi wanda ya dauki bawansa da daddare daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Al Aqsa; wuraren da muka martaba, za mu nuna masa wasu daga cikin alamominmu. Tabbas Shi Mai ji ne, Mai gani ne.”
Ayar tana magana ne a kan Isra’i, wato tafiyar da Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW) daga Madina zuwa Masallacin Kudus da ke birnin na Kudus, inda ya gudanar da salloli, gabanin Mala’ika Jibrilu ya dauke shi zuwa sama domin ganawa da Allah Mai Girma.
Bayanai na Musulunci sun nuna cewa ganawar ta Annabi Muhammad da Ubangiji ta wuce duk wani hasashe na masana kimiyya da sararin samaniya.
An yi tafiyar ce cikin ilhama daga Masallacin Harami zuwa Masallacin Kudus, inda daga nan aka tafi da shi zuwa sama.
Annabi ya yi tafiyar ne a yayin da yake fuskantar tsanani da kunci daga kabilarsa da ma wasu danginsa. Shi da sahabbansa suna shan suka da wulakanci da danniya saboda sun yi Imani da Allah Madaukakin Sarki.
Ayoyi da Hadisai da dama sun bayyana muhimmancin Masallacin Kudus. A cikin Alkur’ani an fito karara an bayyana sunayen masallatai biyu ne, wato Masallacin Harami da ke Makkah da Masallacin Kudus da ke Birnin Kudus.
Ya kuma bayyana Al Haram, wato yankin da ya kewaye Kaaba, inda Musulmai daga ko ina a fadin duniya suke zuwa domin gudanar da salloli da dawafi ga Allah.
Kazalika, Alkur’ani ya bayyana Masallacin Kudus a matsayin cibiyar Bayt al Maqdis, wato “Kasa mai Tsari” da kuma “kasa mai albarka” ko kuma kasa mai ceto da zaman lafiya.
A Alkur’ani, an bayyana Kudus da yankunan da ke kewaye da shi a matsayin wadanda ke da “albarka”.
A tsarin Musulunci, kalmar “kasa mai albarka” na nufi wadda Allah ya yi wa martaba ta fili da ta ruhi wadda za ta amfani dukkan halittu.
Kasar Annabawa
Kusan dukkan annabawa – ciki har da wadanda aka haifa a wani wuri daban – sun zauna a Kasa Mai Tsarki ko kuma suna da dangantaka ta musamman da ita, abin da ya sa kenan Kudus yake da matukar kima a idanun Musulmai.
Haka kuma Annabi Muhammad ya yi bayani game da muhimmancin daren da ya yi isra’i ga dukkan mabiya addinin Musulunci da wadanda suka gabace su.
Wani Hadisi ya bayyana cewa “Lokacin da Annabi Sulaiman ya gama gina Baytul al Maqdis, ya roki Allah abu uku: hukunci da ya yi daidai da irin nasa, mulkin da babu wani a bayansa da zai samu irinsa, da kuma cewa ka da kowanne mutum ya je masallacinsa da zummar yin sallah ba tare da yana da tsarki ba kamar ranar da aka haife shi.”
“An karbi addu’o’i biyu, kuma ina fata ta ukun ma ta karbu.” Tabbas annabawan da suka fito daga al’ummar Yahudawa na cikin wadanda Musulmai suke hadawa da su idan suka bayyana Kasa Mai Tsarki a matsayin "kasar annabawa" kuma a addinin Musulunci su ne suka rika annabta kafin ta iso kan Annabi Muhammad.
Wani misali game da Annabin da ke da alaka ta musamman da Kasa Mai Tsarki da kuma Birnin Kudus musamman, shi ne Annabi Ibrahim.
Bayan ya lalata gumakan da al’ummarsa ke bautawa a birnin Babylon, ya fice daga birnin. Ya tafi yankin Falasdinu.
A cikin Alkur’ani, an ambaci sabon wurin da ya isa a matsayin Kasa Mai Tsarki. “Mun tseratar da shi da dan uwansa Ludu sannan muka gaya musu su tafi Kasar da muka sanya ta zama mai albarka ga dukkan al’umma.” (Al Anbiya, 21:71)
Tafiya mafi al’ajabi da Annabi ya yi da daddare
Ganin cewa Birnin Kudus ne wuri daya tilo da aka sani inda Annabi Muhammad (SAW) ya jagoranci dukkan Annabawa don yin sallah, ya bai wa birnin karin daraja.
Dukkan annabawa suna Kudus a daren da annabi ya yi isra’i kuma hakan ya sake fito da muhimmancinsa, kamar yadda Alkur’ani ya bayyana:
“Ka ce, ya ku wadanda kuka yi Imani ku ce, ‘Mun yi Imani da Allah da dukkan littafan da aka saukar mana; da dukkan littafan da aka aiko wa Ibrahim da Isma‘il, Ishaq da Ya‘qub, da zuriyarsu; da wadanda aka bai wa Musa da Isa; da wadanda aka bai wa Annabawa daga wurin Mahaliccinsu; Ba ma nuna bambanci a tsakanisu…” (al Baqarah, 2:136)
Alkibla ta farko ga Musulmai
Kazalika Alkura’ni ya yi magana game da Masallacin Kudus a matsayin alkibla ta farko – inda ake fuskanta domin yin sallah – sannan ya bayyana shi a matsayin wurin da wasu jerin abubuwa za su faru gabanin tashin alkiyama.
A farko-farkon Musulunci, Annabi Muhammad da sahabbansa suna fuskantar Birnin Kudus ne idan za su yi sallah.
Hadisai da dama sun bayyana cewa yana tsaka da sallah, Allah ya umarce shi ya juya ya fuskanci Kaaba.
Shi ne Annabi na karshe da ya fuskanci Masallacin Kudus da Kaaba a cikin sallah daya. Annabi Muhammed yana yawan kwadaitar da Musulmai da su kai ziyara Kudus, yana mai cewa yin sallah raka’a daya a masallacin daidai take da sallah raka’a 500 a gama-garin masallatai.
“Ka da ku ziyarci kowanne masallaci don neman albarka idan ba masallatai uku ba: masallacin (Kaaba), da masallacina (wanda ke Madina), da Masjidil Al Aqsa (da ke Kudus),” kamar yadda aka ruwaito a wani hadisi.
Don haka ne Masallacin Kudus yake da matukar muhimmanci ga mabiya addinin Musulunci.
Ba wai kawai kasa ce gama-gari ba. Musulmai na ganin duk wani hari da aka kai wa Masallacin tamkar an kai shi ne kan Musulunci.