Masallacin Aqsa shi ne masallaci na uku mafi daraja ga Musulmai. Hoto: AA

Yaƙin Isra'ila-Falasɗinawa shi ne yaƙin da ya fi daɗewa a duniya, rikici ne da ya faro tun farkon shekarun 1900 lokacin da wasu masu kaifi kishin son kafa ƙasar Isra'ila (Zionist) da ke Turai suke ƙoƙarin kafa ƙasar Isra'ila.

A shekarar 1917, Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya Arthur Balfour ya rubuta wasiƙa ga Lionel Walter Rothschild wato Shugaban Al'ummar da ke da Kaifin Kishin Kafa Kasar Isra'ila.

A wasiƙar, Balfour ya yi amfani da ƙarfin ikon gwamnati Birtaniya "wajen ƙoƙarin samar da ƙasar Isra'ila a yankin Falasɗinawa".

Ana kiran wasiƙar Ayyanawa ta Balfour tun lokacin.

A shekarar 1922, Kungiyar Kasashen Duniya ta The League of Nations ta ba Birtaniya iko a kan Falasdinawa. Ya hada da wani bangare na ƙasar Isra'ila a yanzu da wani ɓangare a Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gaza.

A ƙarƙashin haka, Birtaniya ta amince da tuɗaɗowar Yahudawa zuwa yankin Falasdinawa kuma daga nan ne aka fara sauya al'amura a yankin ta yadda za a kafa kasar Isra'ila a yankin Falasdinawa.

Kafa kasar Isra'ila

Yahudawa da ke komawa yankin Falasdinu tsakanin shekarun 1933 zuwa 1939 sun jawo zaman tankiya da rikici tsakanin Yahudawa da Larabawa.

A ranar 14 ga watan Mayun shekarar 1948, Isra'ila ta kawo ƙarshen ikon Birtaniya a kan Falasdinawa biyo bayan kudurin Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1947, wanda ya buƙaci raba yankin tsakanin Larabawa da Yahudawa.

A rana guda, an kafa kasar Isra'ila a wurin da aka shata wa Yahudawa a kudurin tsarin raba yankin.

Washegari yaki ya ɓarke tsakanin Larabawa da Yahudawa, inda ya hada da dakaru daga Masar da Syria da Jordan da İraki da kuma Labanon.

Bayan yakin da Larabawa suka yi rashin nasara, an lalata kauyuka 500 na Falasdinawa da garuruwa da birane, kuma akalla Falasdinawa 750,000 ne aka raba da muhallinsu.

Wanzuwar bore

Falasdinawa sun zama ba su da ƙasa, kuma kasar da ake kira ta Falasdinawa kafin shekarar 1948 ta zama kasar Isra'ila a yanzu.

Karshen yaki tsakanin Larabawa da Isra'ila ya zama masomin rikici. Daga nan ne rikicin Falasdinawa da Isra'ila ya kara zama mai sarƙaƙiya tun lokacin.

Isra'ila ta kara yin yake-yake hudu da Larabawa (a 1956 da 1967 da 1973 da kuma 1982) kuma za a iya cewa ta samu nasara a dukkansu.

Larabawa wadanda suka yi watsi da kudirin tsarin raba yankin na Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, yanzu a shirye suke su amince da adadin yankin Falasdinawa kafin karshen Yakin Kwana Shida a shekarar 1967: Gaza da Gabar Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Birnin Kudus.

A shekarar 1987 wani bore da ake kira da sunan Intifada na farko – an fara ne a Gaza kan 'yan Isra'ila da suka mamaye Yammacin Gabar Kogin Jordan da Gaza da kuma Gabashin Birnin Kudus.

An kawo ƙarshen rikicin ne bayan sanya hannu a kan Yarjejeniyar Oslo a shekarar 1993, inda aka kafa Hukumar Falasdinawa (PA) a matsayin gwamnatin rikon kwarya da kwarya-kwaryan 'yancin kai a yankunan Yammacin Kogin Jordan da Gaza.

Ko da yake Isra'ila ta ci gaba da rike ikonta na tsaron yankin a galibin kasar, abin da ke sa ta iya kai farmaki a kowane lokaci.

Karfin ikon Hamas

A shekarar 1995, Isra'ila ta zagaye Gaza da katangar lantarki da kankare, kuma tana sanya ido kan al'amuran yankunan Falasdinawa.

An kafa Hamas ne a shekarar 1987 jim kadan bayan fara boren Intifada na farko.

Kungiyar wadda tun daga lokacin take kara suna, ta kalubalanci Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta Oslo, kuma ba ta aminci da kasancewar kasar Isra'ila ba, kuma ta amince da kafa kasar Falasdinawa kan iyakokin shekarar 1967.

An kafa bangaren dakarun kungiyar mai suna the Izz al-Din al-Qassam Brigades, don samar da rundunar mayaka da su yaki mamayar Isra'ila.

Hamas ta kasance ita ce take iko da Gaza tun shekarar 2007, yankı ne mai fadin kasa da ya kai muradba'in 365 kuma yake da mutane fiye da miliyan biyu, bayan ta yi nasara a zaben majalisar dokoki a shekarar 2006.

A watan Yunin 2007, Isra'ila ta mamaye Gaza ta kasa da sama da kuma ta ruwa. Ta rika kai farmaki a kan Hamas akai-akai, inda mutum miliyan biyu suke a killace a abin da wasu suke kira wani katafaren gidan yari.

Ci gaba da zubar da jini

Duka yarjejeniyoyin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ba su yi aiki ba bayan duka bangarorin biyu sun zabi mayar da hankali kan ci gaba da rikici.

Tsarin samar da zaman lafiya ya kasa yin tasiri saboda ba a mayar da hankali kan babban batu na samar da 'yanci ga Falasdinawa na ba su kasar kansu da mayar da miliyoyin 'yan gudun hijira da suka kai miliyan shida.

Falasdinawa wadanda suke zaune a halin yanzu a yankin da ake rikici sun kai kaso 21 cikin 100 na gaba dayan Falasdinawa wato miliyan 9.73.

Bayan kwashe tsawon shekaru a rikici, yakin ya ci gaba kuma an ci gaba da arangama tsakanin Isra'ila da Hamas.

Hakan abin zai ci gaba, idan har Falasdinawa da Yahudawa kowanensu ya ci gaba cewa shi ne ke da gaskiya.

Falasdinawa da sunan fafutikar kwato kasarsu, su kuma 'yan Isra'ila da "sunan kare kansu" da "yaki da ta'addanci" – don murkushe Falasdinawa.

TRT Afrika