Daga Hatem Shurrab
Ranar Litinin Isra'ila ta sanar da saka ƙawanya a bakidayan yankin Gaza, inda ta yanke wutar lantarki, da ruwan sha, kuma ta dakatar da shigar da abinci da magani zuwa cikin Falasdinu.
Tun yammacin Asabar jiragen yaki na Isra'ila suke ruwan bama-bamai kan yankunan Falasdinu, inda suka kashe sama da mutum 490. Martanin Isra'ila ya zo ne bayan kutsen bazata da mayakan Hamas suka yi cikin kasar, a inda 'Isra'ilawa 700 suka rasa rayukansu.
A ranar Lahadi ne Isra'ila ta ayyana yaki a hukumance, inda ta tattaro sojojin ko-ta-kwana, kuma suka hada dubban sojoji a iyakar Gaza.
Sama da Falasdinawa miliyan biyu ne ke rayuwa a Gaza mai yawan al'umma, wanda ya dade yana fuskantar takunkumin Isra'ila tun shekarar 2007. Mazauna Gaza suna tsoron munanar lamarin.
'Yan Gaza, wadanda sun sha fuskantar hare-haren Isra'ila a baya, sun ce a yanzu ƙara da girgizar gine-gine da saukar bama-bamai ke haifarwa ta ta'azzara, kuma tana firgitarwa.
Abu daya ne ke zukatan Falasdinawa a yanzu, neman mafaka. Amma kuma ta yaya?
Babu wajen ɓuya
“Harin isra'ila ya rusa wani gini da ke kusa. Wani bangaren gidanmu ya lalace,” a cewar Tala Alghosain, dan shekara 20, kuma mazaunin yankin Sabra na Gaza kamar ya fada wa TRT World.
“Na ji tamkar ana mana ruwan duwatsu da baraguzai kan kawunanmu. Tagogi sun tarwatse sannan bangwaye sun sun tsattsage. Na kadu!”
Alghosain, wata dalibar likitancin hakori, ta ce ya kamata a ce a yanzu tana daukar darasi a karshen mako. Amma a yanzu yadda take gani, rayuwarta cikin lumana ta kawo karshe.
Ta fada ta waya yayin da kake jin karar bama-bamai, “Dukanmu mun takure a barandar gidanmu. Shi ne waje guda da yake da katanga zagaye da shi. Babu wata maboya”.
“Kai ka ce girgizar kasa ake.”
Kamar yadda yake a baya, sojin Isra'ila sukan kira mazauna cikin ginin da suke so su kai wa hari, su nemi su fice daga ciki. Amma 'yan mintuna kawai suke da shi, na barin ginin da komatsensu. Kuma wannan takatsantsan don kaucewa kashe mutane ba kullum yake amfani ba.
Alghosain ta ce, “Wasu mutane an musu gargadi kafin kai hari, amma wasu ana kai hari gidansu ne yayin da suke ciki da iyalansu".
Jami'an Falasdinawa sun ce cikin daruruwan mutanen da aka kashe a Gaza, akwai gabadaya dangi, inda bama-baman Isra'ila suka kashe zuri'a baki dayanta.
Alghosain ta ce, “Wani hari ya fada kan wani gida a kudancin Gaza ba tare da wani gargadi ba. Gabadaya dangin aka kashe ban da wata yarinya daya. Sunanta Tala Abu Dagga. Wannan misali ne na yadda yaƙin nan ya ƙazanta.”
“Na rayu cikin irin wadannan yaƙe-yaƙe a Gaza tun ina yarinya. Amma wannan kamar shi ne mafi muni.
“Na fi tsoron dare saboda shi ne lokacin da harin bam din ya fi yawaita. Ba ma iya yin bacci. Idan muka yi kokarin yi, sai mu yi ta farkawa saboda ƙarar tashin bam.”
Tararrabin wata tsohuwa
Majda Thabit, kaka ce mai shekaru 76, wadda aka kora daga muhallinta tare da iyalanta a lokacin Nakba ta1948. Ta rayu cikin kuncin rikice-rikicen har da Yakin Kwana-6 da aka gwabza sanda Isra'ila ta mamaye Gaza.
Ta fada wa TRT World cewa, “Ban taba shiga irin wannan matsanancin hare-haren ba. Karar Boom, boom, boom kawai kake ji!”
Thabit, wadda ke fama da ciwon suga da matsalolin zuciya ta ce, “Ni kaka ce ga yara da yawa. Dukansu sun fi son su zauna a gida kusa da ni. Sun fi jin aminci a nan. Na zabi dakin da ya fi aminci a gidan muka tattaru tare. Kamar mutum 10 ne a daki daya.”
“Yayin da harin ya fara, ɗana ya ruga zuwa gidan biredi ya kawo mana karin biredi da garin filawa. Mun yi sa'a, kwana daya kafin hare-haren na je ganin likita kuma na karo maganina. Ina jin tsoron idan yakin ya ci gaba tsawon lokaci, za mu rasa biredi da filawa da magani.”
A shekarun baya, duk sanda yaƙi ya ɓarke, a hankali Isra'ila take fara hare-haren - hakan yakan ba da dama ga mazaunan yankin su tara kayayyakin bukata.
Thabit ya bayyana cewa, “Ba ma barin gida kwata-kwata. Akwai hadari a fitar. Ba gine-gine kawai suke hara ba, suna harar motoci a kan titi, har da masallatai ma an hara. Kenan babu inda ya tsira. Ba za ka san inda za a hara gaba ba.”
Kwana ba barci
Majd Shurrab, dan shekara 15, ya ce iyalansa sun yi sa'a sun sayi abinci da kayan ciye-ciye daga shaguna dab da harin isra'ila zai fara.
Ya fada wa TRT World cewa, “Mahaifiyata ba za ta iya dafa komai ba a irin wannan yanayi mai rudani.”
Shurrab, wanda ke zaune a unguwar Al Rimal, ya ce daren Lahadi abu ya tsananta ga iyalansa saboda harin Isra'ila babu kakkautawa.
“Ban iya barci ba. Harin bam ya fada wa wani ofishin 'yan sanda a unguwarmu. Karar fashewar bam din ya fi kowane irin bam da na taba ji ba a baya.”
Shurrab ya ce, “Ni da kanwata muna da dabarar maganin tsoro. Muna toshe kunnuwanmu da karfi idan muka ji tahowar jirgin yaki na F-16 ko harbin makamai.
Wani lokacin hakan yana mana amfani, wasu lokutan kuma ba ma iya samun lokacin toshe kunne saboda harin ya zo da bazata”.
“Sabon abu a wannan yakin shi ne idan aka kawo harin jirgin sama, suna dira ne duka a tare. Sai daga baya muke sanin mabambantan gidajen da aka hara a lokaci guda.”
Hatem Shurrab marubuci ne dan Falasdinu mazaunin Istanbul.