Kawar da abokan gabarka daga cikin al’umma yana daya daga cikin dabarun Amurka, wadannan yanzu Isra’ila take amfani da su a kan Hamas. Photo: Evelyn Hockstein

Kawar da abokan gabarka daga cikin al’umma yana daya daga cikin dabarun Amurka, wadannan yanzu Isra’ila take amfani da su a kan Hamas.

A sakamakon hakan, Isra'ila tana ƙoƙarin nuna cewa ayyukan da take yi suna da hujja, waɗanda da yawansu sun kai matakin laifukan yaƙi, ta hanyar amfani da kakkausan harshe na cusgunawa ɗan'adam, kamar irin yadda take alaƙanta ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas da magoya bayansu fararen hula da cewa, "dabbobi ne su a fatar mutane."

Tun shekarar 2007 Hamas ke jagorantar Gaza bayan da ƙungiyar, wacce take da ƙarfi a siyasance, ta yi nasara a zaɓuka da gagarumin rinjaye.

Ƙaurin sunan da ƙungiyar Daesh ta yi a kan rikici da zalinci kamar yanke kawunan mutane da rataye mutane a bainar jama'a, ya sa Isra'ila take ƙoƙarin yi wa Hamas irin wannan kallon ta yadda za ta samu lasisin kashe fararen hula da sunan yaƙi da Hamas ɗin kamar yadda gamayyar ƙawancen da Amurka ta jagoranta ya yi a kan Daesh, inda aka kashe dubban fararen hula a ayyukan yaƙi da ta'addanci da aka yi a faɗin Siriya da Iraƙi.

Dakarun Amurka da ƙawayenta sun kuma kashe fararen hula da dama da suka haɗa da yara a Afghanistan da sunan kawar da mayaƙan ƙungiyoyin Al Qaeda da Daesh da kuma yaƙi da Taliban a ƙasar da yaƙi ya ragargaza.

"Kungiyar Daesh ta zamo wani bala'i da ba ta da alaka da kowace irin fafutuka da wani zai so ya kare ta," in ji Heiko Wimmen, darakta na wata kungiyar bincike ta Amurka International Crisis Group, mai aiki da Iraki da Siriya da Labanon.

Sai kwatanta ayyukan kungiyar Hamas da Daesh "ya tsayar da duk wata tattaunawa a game da dalilai da dokoki" da suka sanya aka mayar da Falasdinawa kamar 'yan fursuna, wanda hakan ne ya sa Hamas ta kaddamar da hare-haren ranar 7 ga Oktoba, kamar yadda Wimmen ya shaida wa TRT.

Wannan lamarin ya kuma ba Isra'ila wata damar da take bukata kasancewar babu wanda zai amince a yi sulhu da kungiyar ta'addanci irin Daesh.

Da wannan ne masu ra'ayin tabbatar da mulkin Yahudawa suka rufe dukkan wata damar sulhu da Hamas, suka kuma dauki matakin yakin kare dangi, har da kashe fararen hula.

"Ba a sulhu da kungiyar ta'addanci. Kisan kiyashi ake musu har su kare daga ban kasa," in ji Wimmen.

Amma a wani lamari na kwan-gaba-kwan-baya, ko a wannan karon Isra'ila ta yi sulhu da Hamas, kamar yadda ta sha yi a baya ko dai domin tsagaita wuta ko kuma shirya yadda za a kai kayayyakin agaji zuwa Gaza, wanda yanki ne na Falasdin da ke karkashin mamaya ta sama da kasa da ta ruwa tun a shekarar 2007.

Akwai wasu makwabta da aka kashe su baki daya a wannan rikicin da ake yi na Isra'ila da Hamas Hoto: AA

Amma matsalar a nan ita ce, Hamas tana da tarihin shekara 30 da ke bambamta harkokinta da na kungiyar ta'addanci ta Daesh, sannan ta sha shiga sulhu da Isra'ila da shi kansa Netanyahu, in ji Ibrahim Moiz, wanda mai sharhi ne a kan harkokin siyasa da suka shafi harkokin soji da kungiyoyin 'yan bindiga kamar Taliban.

Amma saboda a yi watsi da wannan sanannen tarihin na baya, sai "Masu yada farfagandar Isra'ila suka kara gishiri a miya, inda suka yada farfagandarsu a duniya domin bata sunan Hamas da cin mutuncin Falasdinawa baki daya," in ji Moiz a tattaunawarsa da TRT.

Haka kuma daga cikin manufar kwatanta ayyukan Hamas da Daesh, akwai neman "Karin goyon baya daga kasashen duniya da Isra'ila take yi, da kuma neman kasashen duniya su daina kushe yakin da take yi," in ji Wimmen, mai sharhi a kan harkokin siyasa daga Beirut.

"Idan muna yaki da Daesh, wadda 'annoba ce', ai ba za mu damu ba ko? Sannan kuma ai an ga hakan a baya, inda aka yi amfani da karfin tuwo wajen fatattakar Raqqa da Mosul, kuma babu wanda ya nuna damuwa da matakin," in ji Wimmen.

Shin kwatanta ayyukan Hamas da Daesh shirin bata sunan Musulmi ne?

Yadda kasashen Yamma ke zargin duk kungiyoyi da Musulmi suka fi yawa kamar Hamas da ta'addanci ba zai haifar da da mai ido ba a duniya domin masana suna hasashen cewa nan da shekarar 2075, Musulunci ne zai zama addini mafi tarin mabiya a duniya, kamar yadda wani masani ya bayyana.

Bayan harin 11 ga Satumba, sai George W. Bush ya kirkiri wani salo a hakaikaice da ya ayyana da nagari da mugu, ta hanyar amfani da kalmar "sauyi" wajen nuna shirinsa na yaki da ta'addanci wanda Amurka ta yi amfani da shi wajen kaddamar da mummunan yaki a kasashen Iraki da Afghanistan, inda aka kashe sama da mutum miliyan daya a kasashen guda biyu.

Kamar Bush, haka bayan harin na 7 ga Oktoba, manyan shugabannin kasashen Yamma irin su Amurka da Turai sun yi magana a kan 'aikita mummuna karama" da "tsohuwar manufar aikata mummuna" wanda Musulmi da dama suke tunanin da Musulunci suke yi.

Wannan kwatancen ya fito ne bayan hukumomi a kasar Isra'ila sun bayyana Hamas a matsayin "dabbobin mutane" kuma "makiya ci gaba."

"Nuna bambanci tsakanin ayyukan Hamas da Daesh yana samun goyon baya a tsakanin 'yan siyasar Amurka, amma kwatanta su din ya so ya boye bambancin da ke tsakaninsu," in ji Nadia Ahmad, Farfesar shari'a ce da ke zaune a Jihar Orlando, kuma malama a Cibiyar Tsaro da nuna wariyar fata da kare hakkin dan'adam, a lokacin da take bayyana yadda kasashen suke ta kokarin nuna cewa Hamas da Daesh duk daya ne.

Duk da cewa dukkan kungiyoyin biyu suna dauke da makamai, akwai bambance-bambance masu yawa a tsakaninsu tun daga tarihin kafuwarsu da muradunsu da ra'ayoyinsu, in ji Nadia.

Amma kasashen Yamma sun rudu da farfagandar Isra'ila, inda suka kauce daga asalin batun, suke kallon kusan dukkan wani Musulmi a matsayin dan ta'adda kamar yadda Nadia ta bayyana.

"Dukkan Musulmi da Larabawa ana lakaba musu ta'addanci. Da farko ana kiranmu ne da Al-Qaeda, muka koma Daesh, yanzu kuma Hamas," in ji Nadia a tattaunawarta da TRT.

Sai sai duk da zargin nan da ake wa Musulmi, masu sharhi a kan al'amura na kasashen Yamma sun tabbatar da yadda Amurka ta taimaka wajen samar da wasu kungiyoyin ta'addanci kamar Daesh, in ji ta.

David Kilcullen, daya daga cikin fitattun masana harkokin yaki da ta'addanci na duniya, kuma tsohon mashawarcin Janar David Petraeus, tsohon darakta a CIA, wanda ya taba jagorantar farmakin Amurka a Iraki, ya ce samuwar kungiyar Daesh na da alaka ta kai tsaye da yakin Amurka a Iraki.

"Ya kamata mu fahimci cewa mu ne muke jawo wa kanmu wasu matsalolin. Da ba mu yaki Iraqi ba, da ba za a samu kungiyar Daesh ba," in ji Kilcullen a wata zantawarsa da Channel 4 News a watan Maris.

TRT World