Sama da al'ummar Sudan 3.2 sun tsallaka iyakar ƙasashe maƙwabta don neman tsaro, cewar Majalisar Ɗinkin Duniya. / Hoto: NRC

Daga Sylvia Chebet

Um Adel, wata 'yar gudun hijira daga Sudan tana jiran tsammani a sansanin Metche da ke gabashin Chadi, kuma ba ta haɗu da mai gidanta ba cikin sama da shekara guda.

Ta ce, "Mijina ya ɓata, kuma ban san inda yake ba".

"Ɗanmu Khalid yana da ƙoshin lafiya kafin abinci ya fara wahala. Bayan kwana ɗaya ko biyu na rashin abinci da kyau, ya fara zazzaɓi. Ba na jin daɗi a nan, kuma lamarin ba shi da kyau... Ina so na koma gida Sudan."

Yayin da aka shiga sabuwar shekara, Um Adel na fatan ganin daidaitar yanayi a ƙasarta, bayan yaƙi tsakanin sojojin Abdel Fattah al-Burhan da rundunar sojin RSF da Mohamed Hamdan Dagalo ke jagoranta.

Rikicin na cikin gida a Sudan ya ɓarke ranar 15 ga Afrilun 2023. An rasa rayuka sama da 60,000 tun lokacin. Adadin waɗanta suka tagayyara ya haura miliyan 14. Aƙalla miliyan 26 suna fama da ƙarancin abinci.

Duk ta inda aka duba, yaƙin Sudan shi ne matsala mafi girma da ɗan'adam ke fuskanta a duniya yanzu. Amma duk da haka, shekara 2024 ta wuce duniya ba ta ma kula da yaƙin ba ko kaɗan kamar yadda ta ɗauki barazanar yaƙi a wasu wuraren daban, kamar yadda yaƙin Rasha da Ukraine ke ɗaukar hankula ake kuma yawan maganarsa.

Miliyoyi ba su da matsuguni

Al'ummar Sudan sama da miliyan 3.2 sun tsallaka iyakar ƙasashe maƙwabta kamar Chadi da Sudan ta Kudu da Habasha da Jumhuriyar Tsakiyar Afirka da Masar da ma Turai da Gabas ta Tsakiya.

Lamarin da ya fara da rikici a Khartoum yanzu ya koma faɗan hare-hare da ruwan bama-bamai a faɗin ƙasar tsawon watanni 20.

A cewar Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam, rikicin ya ƙunshi ta'annati, da kisan ƙabilanci da fyaɗe.

Kotun Duniya mai Hukunta Manyan Laifuka (ICC) tana bincike kan zargin laifukan yaƙi. Ba a samun wadataccen abinci da ruwan sha mai tsafta. Yara suna fama da rashin abinci mai gina jiki.

Cututtuka suna yaɗuwa. Asibitoci ba su da yawa kuma ba su da tsaro. Ba a samun taimako kan lokaci.

"Wannan mummunan rikici da ke keta zarafin ɗan'adam da haifar da matsalar jin-ƙai yana gudana ba tare da damuwar al'ummar duniya ba" in ji Babban Kwamishinan MDD kan 'yan gudun hijira, Filippo Grandi.

Ya yi amanna cewa ko da kafin fara yaƙin kisan ƙare-dangin da Isra'ila ke yi a Gaza ya ɗauke hankali, yaƙin Sudan abu ne da aka "ware" duk da munin tasirinsa.

Grandi ya yi tir da "ƙarancin damuwa da rikici-rikice a Afirka”, kamar na Jumhuriyar Dimukuradiyyar Congo da na yankin Sahel, a matsayin "mai firgitarwa da tayar da hankali".

Ya yi tararrabin makomar Sudan idan yaƙi bai tsaya ba a nan kusa.

"Me ce makomar ƙasa kamar Sudan, wadda yaƙi ya lalata?" Grandi ya tambaya, cikin damuwar cewa 'yan Sudan "da suka haɗe kan ƙasar" an kassara su gaba ɗaya.

"Sun san abu ya ƙare. Sun rasa ayyukansu, an ruguza gidajensu, kuma sun ga yadda aka kashe danginsu da 'yan uwansu. Abin takaici ne".

Tsanantar yunwa

Sama da 'yan Sudan miliyan 26 suna fuskantar karancin abinci a cewar MDD. / Hoto: NRC

Ma'aunin wadatar abinci na IPC, wani ma'aunin ne da cibiyoyin MDD sama da 10 ke amfani da shi, tare da ƙungiyoyin agaji don fayyace matsalar abinci da ta abinci mai gina jiki. Ma'aunin ya nuna cewa yaƙin Sudan "yana ta'azzara" karancin abinci.

Tawagar da ke lura da matsalar yunwa ta gano ƙarancin abinci a yankuna biyar, ciki har da sansani mafi girma a Sudan, Zamzam, wanda ke arewacin gundumar Darfur.

Dervla Cleary, wata babbar jami'ar gaggawa ta hukumar abinci da noma ta MDD, ta ruwaito cewa mutane 638,000 suna fama da ƙaranci abinci.

Ta ce "Lamarin Sudan abin takaici ne. Ba abin da za a aminta ba ne a duniyarmu ta yau".

Cikin shekaru 15, Sudan ita ce ƙasa ta uku a Afirka bayan Sudan ta Kudu da Somalia da aka saka cikin rukunin masu fama da ƙarancin abinci.

Matsalar kiwon lafiya

Ƙungiyar (MSF), wadda ake kira da Doctors Without Borders, ta yi jinyar sama da yara 40,000 da suke fama da rashin abinci mai gina jiki a Sudan.

Ƙungiyar ta kafa cibiyar bai wa marasa lafiya abinci a sansanin Zamzam da ke Darfur ta Kudu, da El Geneina a Darfur, da Nyala da Rokero, da kuma gabashin Chadi, inda tarin 'yan gudun hijira ke rayuwa.

"Yara na mutuwa saboda rashin abinci mai gina jiki a faɗin Sudan. Taimakon da suke buƙata cikin gaggawa ba ya zuwa, idan kuma ya zo, yawanci ana tare shi," cewar jami'in gudanarwa na MSF a Darfur.

"Ga misali a Yuli, an tare motocin ɗaukar kayan abinci na MSF daga kai wa inda suka nufa a Darfur. RSF sun tare motoci biyu, kuma wasu masu ɗauke da makamai sun ƙwace guda."

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta lura cewa rikicin ya saka kashi 80% na kayayyakin kiwon lafiya ba sa aiki, ya gurgurta aikin lafiya.

An ƙwace kayan aiki

A garin El Fasher kawai, MSF ta taimaka wa cibiyoyi da aka kai wa hari sau 12, kuma a asibitin gwamnati guda ɗaya ne kawai ake aikin tiyata tun bayan tsanantar yaƙi a birni cikin watan Mayu.

"MSF ta yi ƙoƙarin cike wasu gurabe. A wurare da dama, mu kaɗai ne ƙungiyar da ke aiki. Ba za mu iya tunkarar wannan ba mu kaɗai. Muna shan wahalar samun kayan aiki da ma'aikata," in ji Esperanza Santos, jami'in kula da ayyukan gaggawa na MSF a jihar Port Sudan.

"Mataki mai tasiri tare da tallafin da zai kai ga jama'a da ke buƙatar shi cikin gaggawa dole ya fara yanzu. babu lokacin ɓatawa."

An samu ƙazantar cutukan malaria da cutuka masu yaɗuwa ta ruwa, inda aka ayyana yaɗuwar kwalara a aƙalla jihohi uku.

Barazanar cutukan yara da ake iya kaudawa ta amfani da riga-kafi, kamar ƙyanda tana ƙaruwa, saboda yaƙin ya haddasa dakatar da ayyukan riga-kafi.

Lamarin ba shi da kyau a ƙasashe maƙwabta inda dubban 'yan Sudan suka yi gudun hijira.

Yayin da rayuwa da walwala da makomar ƙasar ke cikin ƙalubale, babban abin da miliyoyin mutane ke laruwa da shi, shi ne kyakkyawan burin da sabuwar shekara ke fatan kawowa.

TRT Afrika