Firaministan Habasha, Abiy Ahmed da jagoran sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan sun kaurace wa taron na IGAD. Hoto. Reuters      

Daga Coletta Wanjohi

Sabani na kara bayyana a tsakanin kasashe takwas na Kungiyar IGAD ta kasashen Gabashin Afrika, biyo bayan kaurace wa babban taron shugabannin kasashen kungiyar da aka fara a 18 ga Janairu a birnin Kampala na kasar Uganda, ba tare da kasashen Sudan da Habasha ba.

Sudan tana kaurace wa harkokin kungiyar ne domin nuna rashin dadin gayyatar Mohamed Hamdan Dagalo, shugaban dakarun paramilitary Rapid Support Forces wato RSF da suke fafata yaki da shi.

Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar, ta bayyana cewa gayyatar Dagalo ya "saba dokar shugabancin kasarta, da dokokin gudanar da IGAD da tsare-tsaren kungiyoyin duniya."

A daya bangaren kuma, Habasha ta ce ba za ta halarci taron ba ne saboda, "wani uzuri da ya danne zuwa taron, da kuma yadda ta samu gayyatar taron a makare."

Abin mamakin shi ne an shirya taron ne domin tattauna sabanin da ke tsakanin Habasha da Somalia da kuma yakin da ake cigaba da gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF din.

Bayan Sudan da Habasha, sauran kasashen IGAD su ne, Djibouti, Eritrea, Kenya, Somalia, South Sudan, da Uganda.

Hedkwatar kungiyar, wato Djibouti ne ya kira babban taron a ranar 11 ga Janairu.

Rashin jituwa a yankin

Rikicin Habasha da Somalia ya samo asali ne daga wata yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Habasha da Somaliland . A 1 ga Janairun bana, Habasha ta rubuta wata yarjejeniyar karbar hayar wani yanki na tsibirin Somaliland, domin ita kuma ta amince da ita a matsayin kasa mai cin gashin kanta.

Daga cikin yarjejeniyar, Somaliland za ta ba da hayar kilomita 20 na kasarta a gabar teku ga kasar Habasha domin ta gina sansanin jiragen ruwa, kamar yadda Shugaban Kasa Muse Bihi Abdi na Somaliland ya bayyana.

"Yarjejeniyar za ta ba Habasha dama ga teku, da kuma samun wasu hanyoyin harkoki a tekun," kamar yadda wata sanarwa daga Ofishin Firayministan Habasha ta bayyana.

Habasha da Somaliland sun sa hannu a yarjejeniyar ce a ranar 1 ga Janairun 2024. Hoto: Firayministan Habasha

Somalia ta yanke alaka da Habasha, inda ta nanata cewa Somaliland na karkashinta ne, kuma ba ta da hurumin shiga wata yarjejeniyar alaka da wata kasa baga-gadi.

Ita dai Somaliland ta balle ne daga Somalia tun sama da shekara 30 da suka gabata, amma har yanzu Majalisar Dinkin Duniya ba ta ayyana ta a matsayin kasa mai cin gashin kanta ba.

Amon rashin aminci

A gefen taron NAM karo na 19 wanda yake wakana a lokacin daya da taron na IGAD, Babban Sakataren Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje na Somalia, Hamza Adan Haadow ya ce kasarsa ba ta da niyyar fara yaki da makwabciyarta.

Sai dai kuma ita Habasha ba ta shirya yanke alakar da ta kulla da Somaliland ba. Tuni kasashen biyu ma suka shiga yarjejeniyar kawancen soji.

Ganin yadda fargaba ke karuwa, Amurka ta saka baki a kan lamarin, inda ta bayyana matsalar da yarjejeniya tsakanin Habasha da Somaliland.

"Abin da muka fi damuwa da shi, shi ne yarjejeniyar za ta iya kawo tsaiko a yakin da Somalia da Afrika da ma duniya baki daya ke yi da kungiyar al-Shabab," inji John Kirby, daraktan sadarwa na Hukumar Tsaro ta Amurka.

Taurin kan Sudan

Sudan ta yanke alaka ne da IGAD kimanin wata daya bayan gwamnatin karbar mulki karkashin jagorancin Shugaban Kasa Abdel Fattah al-Burhan da dakarun RSF sun amince su fara tattauna yiwuwar tsagaita wuta.

A yayin da ake tsaka da sauraron samun maslahar, yanzu ita Sudan ta nuna rashin jin dadinta a kan yadda IGAD ta sanya tattauna rikicinta na cikin gida, "ba tare da izininta ba." Sannan kuma gayyatar Dagalo ya kara fama mata ciwon da take ji, lura da sanarwar Ma'aikatar Harkokin Kasashen Waje na kasar na makon nan.

Wannan mataki zai haifar da matsaloli da dama. Yanke alaka da IGAD na nufin dakatar da duk wata tattaunar sulhu a yankin.

Wannan mataki zai haifar da matsaloli da dama. Yanke alaka da IGAD na nufin dakatar da duk wata tattaunar sulhu a yankin.

"Idan ana batun tattauna tsakanin kasashe, sabani da son kai tsakanin kasashen na kawo tsaiko wajen samun nasara da maslaha," inji Nuur Mohamud Sheek, tsohon kakakin Babban Sakataren IGAD a shafinsa na X.

"Batun tsaro yanzu ya wuce batun tsaro a iyakar kasashe kawai, dole a samu hadin kan kasashe masu makwabtaka. Domin fahimtar wannan sabon sauyin, dole IGAD ta gane lokaci ya canja ta hanyar neman shawarwari da gyare-gyare domin aikinta ya yi kyau," in ji shi.

Mutanen kasar Sudan dai suna cigaba da dandana kudarsu saboda yakin. Tun bayan hambarar da gwamnatin Omar al-Bashir a 2019, har yanzu mutanen Sudan ba su samu kwanciyar hankali ba.

Kimanin wata tara da fara yakin, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana da, "daya daga cikin yake-yaken da suka yi saurin girmama, kuma wanda ya fi raba mutane da muhallansu a duniya."

Kimanin mutum miliyan 7.4 ne yakin ya raba da muhallansu. Yadda Sudan take yanke alaka da IGAD, da kuma yadda Habasha ta kauracewa wannan babban taron, ya nuna lallai akwai sauran rina a kaba a yankin.

TRT Afrika