An sha samun mutuwar mutane sakamakon turmutsutsu a Nijeriya: Hoto/Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

"Yunwa ba batun sadaka ba ne. Batu ne na adalci." Waɗannan kalaman na marigayi jami’in diflomasiyyar Senegal Jacques Diouf, wanda ya kasance babban daraktan Hukumar Abinci da Noma ta MDD tsawon shekara 18, sun yi kama da gaskiya dan aka yi la'akari da halin da Nijeriya ke ciki na alhinin mutuwar fiye da mutum 60 cikin wannan watan wurin neman abinci da sauran ababen kyauta da aka raba a tarurruka.

Abin da ya ƙara zafin rashin shi ne wannan bala’in da ya faru a wurare daban-daban — a Ibadan da Anambra da kuma Abuja — sun faru ne a lokacin da tsadar rayuwa ke ƙaruwa a ƙasar ta Yammacin Afirka.

Yayin da gwamnati ke dora laifin turmutsutsun kan rashin shirin da ya dace, wasu na ganin kamar waɗanda suka shirya tarurrukan a Ibadan da Abuja a matsayin wani mataki mai taƙaitaccen tasiri.

Rashin tsari

Masana sun ce babban ƙalubalen da ke fuskantar gwamnati shi ne magance matsalolin da ke wa tattalin arziƙin ƙasar zagon ƙasa tare da sauƙaƙa yanke ƙauna na yawancin mutane da ke fuskantar matsalr yunwa.

"Abin baƙin cike ne kasancewar mutane da dama ba su da tsari. Dole mu ƙara tsari a lamurranmu," in ji Shugaba Bola Ahmed Tinubu game da jerin turmutsutsun.

"Ina yi wa waɗanda suka rasa ‘yan uwa ta’aziyya, duk da ya ke dole in ce aba mai kyau ce kyauta."

Shugaban ya bayyana wa maname labarai cewa ya shafe fiye da shekara 25 yana bai wa mabuƙata taimako a gidansa ba tare da wani rashin tsari da zai janyo turmutsutsu ba.

Mataimakin gwamnan jihar Oyo Adebayo Lawal, wanda aka yi turmutsutsu a babban birnin jiharsa Ibadan, ra’ayinsa ya za daya da na Tinubu game da muhimmancin tsara taron jama’a a wuraren ba da taimako.

"Jami’an tsaro sun ce ba a tuntuɓe su ba," a cewar mataimakin gwamnan a lokacin da yake magana game da turmutsutsun Ibadan inda sama da yara 35 suka mutu.

Wani saƙon rediyo da da aka yada a kan taron na Ibadan ya yi shelar za a ba da kyautar abinci da wasu kyaututtuka ga yara 5,000.

Kimanin mutum 8,000 ne suka halarci taron lamarin da ya janyo hargitsi.

Lawal ya yi mamakin yadda wani zai shirya taron dubban mutane ba tare da shirya matakan tsaro ba.

Ana bincike kan manufofi

Dakta Usman Bello na sashen nazarin tattalin arziƙi na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria yana cikin waɗanda suke ganin jerin turmutsutsun a matsayin wani ɓangare na wata babbar matsala.

Tsadar rayuwar da ake daɗe ba a samu irinta ba tuni ta bayyana a bayanan da hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar inda a watan Nuwamba hauhawar farashi ya kai kashi 34.60 cikin 100 bayan an jera watanni uku alƙaluman na tashi.

Faduwar darajar naira na daga cikin abin da ke jawo tsadar rayuwa.

"Abin da ya faru a wuraren sun nuna irin mawuyacin lokacin da muke rayuwa a cikinta.

A lokacin da ba a magance matsalar yunwa ba, za a samu damuwa," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Yawan mutane a wuraren da ake raba abinci da sauran ababen taimako da ake rabawa alamomi ne na matakin wahalar da ake sha."

Dakta Bello ya yi imanin cewa salon gyaran Shugaba Tinubu ya janyo matsalolin tattalin arziƙin da ƙasar ke fuskanta.

"Ɗaya daga cikinsu shi ne karya darajar kuɗi da mayar da ƙimar naira bisa halin da kasuwa ta yi wanda wani mataki ne mai hatsari," in ji shi.

Ɗaya daga cikin matakan da Shugaba Tinubu ya ɗauka bayan ya karɓi ragamar mulki cikin watan Mayun shekarar 2023 shi ne cire tallafin man fetur da kuma “barin kasuwa ta yi halinta” a kan darajar naira, matsayin wani ɓangare na gyara domin ƙarfafa tattalin arziƙin ƙasar.

Masana sun kawo bayanai daban-daban da ke nuna cewa wadannan manufofin sun yi wa ‘yan Nijeriya illa wajen samun damar sayen abu.

“Wata takarda da babban bankin kasar ya wallafa a shekarar 2019 ta nuna cewa babban abin da ke haifar da hauhawar farashin kayayyaki shi ne sauyin Naira zuwa dala,” in ji Dokta Bello.

"Duk lokacin da darajar kudinmu ta fadi a kan dalar Amurka da ya kai Naira 75, hakan na nufin hauhawar farashin kayayyaki a cikin gida."

Shugaba Tinubu ya musanta cewa manufofin gwamnatinsa ne suka sa hauhawar farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabo, lamarin da yake haifar da turmutsutsu a tsakanin mutanen da ke neman agajin abinci.

"Kowace al'umma, har ma a Amurka, tana da ma'adanan abinci. Suna da masu fama da yunwa, su ma. Biritaniya na da bankunan abinci da ɗakunan ajiya," in ji shi a wata hira da kafofin watsa labaru a baya bayan nan.

Matakan gyara

Bisa la’akari da halin da kasar ke ciki, Dakta Bello ya ba da shawarar a dauki matakai biyu, ciki har da sanya na’urorin da za a hana tashe-tashen hankula a wuraren da ake raba kayan jinkai a tsakanin mutanen da ke neman na abinci.

Tsare-tsaren na dogon lokaci ya tanadi sake tunani kan manufofin gwamnati domin ‘yan Nijeriya su samu hutu.

Abinci na neman gagarar miliyoyin mutane a fadin Nijeriya.

“Daya daga cikin irin wannan mafita ita ce sauya wasu munanan manufofi, kamar rage darajar Naira,” in ji shi.

Sai dai furucin na Shugaba Tinubu na nuni da cewa ba za a ja da baya ba a kan abin da ya ce “manufofin ‘yanci” da aka tsara su don farfado da tattalin arzikin kasar da kuma samar da fa’ida ta dogon lokaci.

Cire tallafin man fetur yana cikin wadannan shawarwari.

"Muna kashe makomarmu, muna kashe dukiyar tsararrakinmu, ba mu saka jari ba, muna yaudarar kanmu. Wadancan gyare-gyaren sun zama dole," kamar yadda ya shaida wa manema labarai.

Dangane da ko gwamnati ta shirya yin wani abu game da ayyukan 'mutanen da ke saye da adana amfanin gona don kara farashinsu, shugaban ya ce: "Ban yarda da ƙayyade farashi."

A cewarsa, abin da ya fi dacewa a yi shi ne tabbatar da wadata kasuwa da kuma ci gaba da tallafa wa manoma da kayan aiki kamar tarakta 2,000 da kasar ke shigo da su domin bunkasa noman zamani.

"Magana ce ta bukatar kaya da kuma samar da su. Za a zo wani mataki da ba za a iya daurewa ba. Za a zo wannan matakin. Matsalolin tattalin arziki za su mummunan tasiri a kanku," in ji shugaban kasar yana magana a kan masu sayen amfanin gona daga manoma suna boyewa.

"Dauki misali farashin man fetur, mun bar shi a hannun kasuwa ta yi halinta, yanzu farashin yana raguwa a hankali."

'Yan Nijeriya ba za su yi fatan a sake samun wani bala'in na turmutsutsu irin wannan ba a wajen karbar tallafin abinci zuwa lokacin da farashin kayan abinci zai yi kasa, kamar yadda gwamnati ta yi hasashe.

TRT Afrika