Daga Eric Mbadinga
Lokacin da giwaye suke fada ciyawa ce take shan wahala. Wannan karin maganar harshen Swahili yana da muhimmanci saboda tasirin kudi wajen samar da agajin abinci a Afirka da kuma sauran sassan duniya.
A 'yan makonnin da suka wuce Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya bayyana wahalar da ake fuskanta dangane da karin bukatar agajin abinci a duniya.
Shirin na Majalisar Dinkin Duniya ya ce ana samun haka ne saboda raguwar kudin gudanarwa da aka fuskanta da kaso 60 cikin 100 a bana, wannan ne adadi mafi yawa da aka taba gani a tarihi.
"A karon farko, shirin WFP ya ga raguwa na kudaden da yake samu na gudunmawa a daidai lokacin da bukatar abinci take karuwa a duniya," in ji WFP, inda shirin ya bayyana matsalolin karancin gudunmawar da yake samu a matsayin dalili.
Kalubalen karancin kudin gudanarwar ya yi tasiri sosai a Afirka, inda kasashe da dama suke bukatar agaji wajen ciyar da miliyoyin mutanenta masu fama da yunwa.
Djaouns Mandjiagar, shi ne mai bai wa shirin shawara kan sadarwa kuma mai magana da yawunta a yankin Yammaci da Tsakiyar Afirka, ya ce abu ne da aka yi hasashen faruwarsa."
Idan ana so a fahimci matsalar kudin da shirin WFP ke fuskanta, to sai mun yi dubi halin tattalin arzikin da duniya ke ciki," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Tun bayan annobar korona, gwamnatocin kasashe da dama a duniya suna fama da matsalar tattalin arziki masu tushe a ciki da wajen kasashen. Saboda tasirin wannan wasu masu ba mu gudunmawa ba sa iya ba mu akalla a baya-baya nan, don damar da taimakon da ya dace wajen tafiyar da shirin.
"Shugaban shirin Cindy McCain ya fitar da sanarwa a watan da ya wuce inda ya jaddada muhimmancin "bukatar gaggawa da ake da ita ta kara samun kudin gudanarwa, musamman saboda ganin yadda aka kara mutum miliyan 24 cikin mutum miliyan 40 da ake da su a kasa a shirin samar da abinci na gaggawa".
Karuwar bukatar abinci
Mandjiagar ya ce halin da ake ciki a duniya shi ne bukatar abinci da ake da ita a duniya ya karu yayin da albarkatu suke raguwa a kullum.
A watan Yulin 2023, kaso 45 cikin 100 na masu karbar agaji a Syria da kuma daya bisa hudu na wadanda suke cikin jerin shirin WFP a Haiti ba a ba su agajin.
Haka zalika a Somaliya, inda mutum miliyan 4.7 ba sa samun agajin abinci daga Majalisar Dinkin Duniya a bara.
A Afirka ta Yamma, tasirin abin ya shafi shirye-shirye da dama."Misali a Burkina Faso shirin WFP ya rage taimakon abincin da yake bayarwa tun karshen shekarar 2021, inda ake bayarwa ga rabin mutanen da aka saba ba wato mutum 800,000," in ji Mandjiagar.
Ba Burkina Faso ba ce kadai ta fuskanci wannan matsalar ta rage agajin abincin da suke bayarwa a Afirka.
A Jamhuriyyar Tsakiyar Afirka, shirin WFP ya rage adadin abincin da yake bayarwa da kaso 25 cikin 100 ga 'yan gudun hijira da mutanen da ke cikin matsalar karancin abinci.
Chadi ita ma tana cikin kasashen da aka ragewa agajin abinci.
"Chadi ta karbi 'yan gudun hijirar Sudan tun watan Afrilun da ya wuce.Wadannan 'yan gudun hijirar kari ne a kan wadanda ake da su. Sai dai bukatarsu tana karuwa, shirin ba shi da kudi," in ji Mandjiagar.
Saboda matsalar da ake ciki yanzu ma'aikatan shirin WFP suna "raba rabin adadin abincin da suka saba rabawa ne."
Ana ci gaba da samun kwararowar 'yan gudun hijira da mutanen da ke fama da matsalar abinci galibi a Mali da Nijar, shirin WFP yana samar da rabin abincin da yake bayarwa tun shekarar 2021 saboda karancin abinci.
Matsalar karancin abinci da kungiyoyin agaji suke fuskanta kamar shirin WFP ya jawo tambayoyi da dama kan yadda kananan kungiyoyi agaji su ma suke tafiyar da aikace-aikace.
A Kamaru, kungiyar agaji ta the Centre d'Appui au Développement local participatif Intégré (CADEPI), karkashin dokar Kamaru ta ci gaba da aikace-aikacen duk da "matsanancin halin da ake ciki".
Kungiyar bayar da agaji da suke da mambobi 40 sun shirya aikace-aikace ta hanyoyin da ba a saba yi ba.
Yayin da ainihin hanyoyin da ake bi wajen yaki da yunwa shi ne raba abinci, cibiyar CADEPI ta mayar da hankali wajen samar da hanyoyin samun abinci kamar ruwa da kasar noma mai albarka.
Kungiyar agajin a yankuna uku na arewacin Kamaru — Adamawa da Nord da kuma Extrême-Nord.
Wadannan yankunan, kungiyar CADEPI tana bayar da tallafi ga aikin gona ta hanyar samar da ingantattun iri da sauran shirye-shiryen bunkasa aikin gona.
Kungiyar agajin Kamarun tana kuma aiki wajen dawo da albarkar kasa da bunkasa kiwo. Kungiyar agaji ta CADEPI da aikace-aikacen bunkasa al'ummar don taimaka wa masu amfana da shiri da yaki da yunwa.
Wannan tsarin ya taimaka wa mutane su shigo a fafata da su a aikace, abin da ya sa suka karbi tsarin da kuma aikace-aikacensa.
"An mayar da hankali ne kan bunkasa mutane a yankuna kan samar da abinci da girbin amfanin gona da sauransu. Wannan tsarin yana da tasiri sosai wajen taimaka wa jama'a kan yadda za su jajirce yayin da suke cikin matsalar karancin abinci," kamar yadda shugaban kungiyar Khari Boukar ya shaida wa TRT Afrika.
Matsalar ta wuce ta kudi
A daidai lokacin da kungiyoyin agaji kamar shirin WFP suke fuskantar kalubalen tafiyar da aikace-aikacensu don yaki da yunwa, kungiyar agaji a Kamaru ta ce babbar hanyar samun kudinta tsawon shekara 20 ita ce dabarunta da jajircewarta.
"Jajircewa yana da muhimmanci a wannan fanni, hatta a yanayin da ake fuskantar matsalar karancin kudi, muna bakin kokarinmu wajen yaki da yunwa," in ji Boukar."
A halin da ake ciki akwai matsalar yunwa da talauci da tsaro da kuma sauyin yanayi. Muna kokari a wannan yaki da yin duk abin da ya dace ko ta fuskar kayan aiki ko kwarewarmu."
Don cimma wannan buri, kungiyar CADEPI ta dogara kan hanyoyin samun kudi daban-daban ciki har da ta hanyar wadanda suke amfana da shirye-shiryenta.
"Muna samun tallafi daga Tarayyar Turai kai-tsaye ko ta hanyar wasu kungiyoyin agaji na duniya. Muna kuma samun wasu tallafin daga wajen gwamnati ta hanyar shirye-shirye da take daukar nauyi daban-daban," in ji Boukar.
Ganin wannan kalubale, shirin WFP na yankin Afirka ta Yamma da Tsakiyar Afirka kamar CADEPI ya bukaci karin tallafi da agaji da kulawa daga gwamnatoci da masu bayar da gudunmawa.