Nigeria food crisis

Daga Abdulwasiu Hassan

Bayanai na cewa motoci makare da hatsi da sauran kayan abinci na fitar da kayan abinci ta barauniyar hanya daga jihohin Nijeriya zuwa kasashe makota, duk da cewa su yan Nijeriya din na fama da wahalhalun yunwa saboda boye abinci da ake yi da kuma tashin farashin kayan abincin.

Mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya fito fili ya bayyana yadda girman matsalar fitar da abincin take a wajen wanu taro a Abuja, ranar 20 ga Fabrairu.

“A kwanaki uku da suka gabata kawai, an kama manyan motoci 45 makare da masara, ana kan hanyar fitar da su kasashe makota,” kamar yadda Shettima ya bayyana wa taron.

“Daga lokacin da aka kama wadannan kayan abincin, a lokacin buhun masara ya dawo 10,000… akwai wasu miyagu da suka dage da yi wa kasarmu zagon kasa.”

Kafin mataimakin shugaban kasar ya yi maganar a wajen taron, hukumar hana fasa ƙwauri ta ba da raohoton cewa ta kama motoci maƙare da kayan abinci da wasu masu fa ƙwauri suke kokarin fitar da su ta hanyoyi da dama, da suka hada da wasu a Jigawa a arewa maso yammacin ƙasar.

Staple foods such as rice is smuggled out through illegal routes. Photo: Getty Images 

Ba a fiya jin hukumar ta hana fasa kwauri na kama abincin da ake fita da shi ta kan iyakoki ba. Babban aikinta shi ne hana shigar da wasu nau’ikan abinci kasar, kamar shinkafa, don tabbatar da manufar gwamnati ta bunkasa noman shinkafar a gida.

In ban da ‘yan shekarun nan, babbar kalubalen Nijeriya shi ne yadda za a hana faksa kwaurin man fetur din da ake bai wa yan kasa tallafi a kansa zuwa kasashen ketare.

Lokacin da hukumomi suka gaza hana fitar da man zuwa kasashe makota, sai suka rufe iyake Same tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Benin a 2019.

A cewar gwamnati, wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa aka janye tallafin man fetur, abin da kuma ya haifar da wasu matsalolin.

A yanzu Nijeriya na yaki da mummunan tashin farashin kayan abinci, wanda Hukumar Kidadiga ta Kasar ta ce ya kai 35.41% a watan Janairu.

Matakan gyara

Tangal-tangal din da naira ta ke yi ya janyo karyewar darajarta daga kimanin naira 450 a kan dala daya, zuwa fiye da 1,500 akan dala daya a kasuwannin musayar kudaden kasashen waje.

Karyaewar naira wacce sakamakon daukar wasu matakai na hukumomi, kudin CFA na Afrika ta Yamma da CFA din Tsakiyar Afirka da maƙwabtan Nijeriya

Hakan ya sa fasa kwaurin abinci daga wasu kasashen zuwa Nijeriya ya fi tsada, sannan sayar da abinci a kasashen waje ya fi kawo wa yan kasuwa riba.

Masana sun ce wannan na daya daga cikin dalilan da suka sa hukumar hana fasa kwauri take yawan kama motoci makare da abinci ana shirin fitar da su waje.

Mutuwar kasko

Duk da cewa yunkurin gwamnati na adana kudaden waje da take samu suna yin aiki, a bangare daya kuma mafi yawan yan kasar na fama da matsananciyar tsadar rayuwa.

Nigeria food crisis

Shugaba Tinubu ya ce ya ce yana sane da cewa sauye-sauyen da ake yi suna haifar wahala ga yan kasa, amma ya yi alkawarin cewa wahalar ta dan wani lokaci ce.

Ya ba da umarnin fitio da abinci daga rumbunan ajiyar abincin na kasar, tare da wasu matakan, domin rage tashin farashin kayayyaki.

Hukumomin hana fasa kwauri sun fara sayar da shinkafar da suka kwace a kan farashi mai rahusa na N10,000 a kan kowane buhu mai nauyi 25kg don saukaka wa jama’a wahalhalu. Suma wasu jihohi na kaddamar da na su tsare-tsaren na ba da tallafi don ragewa jama’a radadi.

Buɗaɗɗun iyayoki

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bayyana a taron Abuja cewa a yankin Illela kadai a jihar Sokoto, an bankado haramtattun hanyoyin 32 da ake fasa kwauri ta cikinsu.

Za a iya gane girman matsalar ta la’akari da cewa iyakar Illala dan karamin yanki ne daga kilomita 1,600 na budaddun iyakoki tsakanin Nijeriya da Nijar kawai. Kasar tana kuma da iyakoki da suka kai dubban kilomita tsakaninta da Kamaru da Chadi.

Wasu masu hasashe sun ce yawan haramtattun iyakokin da ake bi don fasa kwauri sun haura 1,000, abin da ya sa zai yi wahala a ce an tare su duka.

Akwai masu ganin cewa takaita cinikayya ce kawai za ta maganta matsalar, to sai dai wannan din da sauran matakan na rufe iyakoki tsofaffin matakai ne na tattalin arziki, a wannan sabon zamani, da duniya ke kara dunkulewa.

Akwai abubuwa da dama da kasa za ta iya samu idan har tana huldar kasuwanci a bude. Rashin ba da damar gogayya na mayar da masana’antun cikin gida baya, sannan kudin da ake kashe wa wajen sarrafa kayan zai sa su ringa yi wa jama’ar da za su saya tsada.

Nijeriya za ta iya saukar da farashin kayayyakin abinci ta hanyar bin wasu dabarun hanyoyin cinikayya, soke wasu manufofin tattalin arziki da suka ta’azzara rayuwa, sannan matakin dogon lokaci kuma, zuba kudi masu yawa a bangaren noma, da kuma bude bangaren ta yadda za a samu masu zuba jari daga kasashen waje.

Wata hanyar kuma ita ce sany ido a kan harkar musayar kudaden ketare don rage fitar da abinci. Fitar da kaya abu ne mai kyau, amma ba ta irin wannan hanya ba.

Murƙushe masu mugun tanadi

Bayan Hukumar Yaki da Rashawa da Karbar Korafi da Kararrakin Jama’a ta Kano ta fara kai farmaki kan mutanen da ta ce masu boye kayan abinci ne, Shugaba Tinubu ya umarci hukumomin tsaro su ringa bankado masu boye abinci a sauran sassan kasar.

“Wannan lokaci ne da za mu hada karfinmu waje guda, mu goyi bayan shugabanmu da gwamnatinmu, da kowa da kowa. Muna da dukkan abin da ake bukata, muna da masu basira, kuma za mu iya sauya al’amura. Muna kan hanyar inganta tattalin arzikinmu,” a cewar gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Ya ce gwamnatinsa za ta bunkasa noma a yankunan karkara, a matsayin mafari.

“Ya kamata mu ringa cin abin da muke nomawa, sannan mu noma abin da muke ci. Ya kamata mu tunkari wannan kalubalen, sannan mu yi amfani da filayen da muke da su, don noma abinci,” a kalaman Sanwo-Olu ga mutanen Legas.

TRT Afrika