Darajar kudin Nijeriya Naira ta sake durƙushewa a ranar Juma’a inda canjinta ya kai N1,000 a kan dala ɗaya, a cewar ƴan kasuwar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje da dama da TRT Afrika ta ji ta bakinsu a Kano da Abuja da Legas har ma da biranen duniya irin su Istanbul.
Wannan ne karo na farko a tarihi da farashin dala ya yi irin wannan tashin gwauron zabin, inda ba ma a Nijeriya ba har a kasashen wajen da ‘yan Nijeriya ke zama haka aka wayi gari ana sayar da ita.
Me ya jawo wannan tashi na dala?
Masana tattalin arziki sun bayyana dalilan da a ganinsu su suka jawo tashin dalar da ya yi sanadin sake faɗuwar naira warwas.
Masanin harkokin tattalin arziki Dokta Isa Abdullahi, wanda malami ne a fannin Tsimi da Tanadi na Jami’ar Kashere ta Jihar Gomben Nijeriya, ya shaida wa TRT Afirka cewa mafi yawan dalilan da suka jawo wannan matsala sakaci ne na gwamnati.
1. Tsarin hade farashin dala a kasuwar bayan-fage da bankuna na daga cikin dalilan da suka jawo dala ta yi ta ci gaba da tashi tun bayan hawan Shugaba Bola Tinubu, in ji shi.
2. Rashin wadatuwar dala a Nijeriya, saboda idan aka sayar da ɗanyen fetur sai kuma a sake amfani da dalar da aka sayar ɗin a sayo tattacen man.
3. Rade-radi da jita-jita da akan yaɗa cewa dalar za ta yi ƙaranci ma na janyo tashinta, sai mutane su ɓoye wacce suke da ita, sannan masu son shigowa da ita ma sai su ɗan tsahirta, lamarin da yake kai ga sake tashinta.
4. Sakaci da arzikin da Allah Ya bai wa Nijeriya inda hukumomi ba sa mayar da hankali har ta kai ga wasu manyan ƙasashen duniya ke iya shiga ƙasar gaba-gaɗi su sace wa Nijeriya ma’adananta.
Wadannan ma’adanan da za a mayar da hankali a kan haƙo su da sarrafa su a hukumance bisa tsari da Nijeriya za ta iya samun makuɗan kuɗaɗen ƙasashen waje ta hanyar sayar da su ga ƙasashen duniya, a cewar Dokta Isa.
“Amma a yanzu sai dai ƙasashen su yi amfani da ƙarfi su shigo da makamai su bai wa ‘yan bindiga su tare musu tare da taya su haƙo ma’adanan su sace su fita da su, kamar yadda shi kansa Shugaba Tinubu ya faɗa wa taron Majalisar Dinkin Duniya kwanan nan a Amurka,” a cewar Dokta Isa.
Sannan ya ba da misali na yadda ake sace gangar ɗanyen fetur 400,000 duk rana a Nijeriya, inda ake yi wa ƙasar asarar kusan dala biliyan huɗu kenan duk rana.
5. Rashin masana’antu da rashin sarrafa kayayyaki ma na ƙara ta’azzara hauhawar farashin kuɗaɗen ƙasashen waje.
“Ana shigo da fiye da rabin abincin da ake ci a Nijeriya daga ƙasashen waje, kuma duk sai an buƙaci kuɗaɗen waje kafin a yi hakan.
Mu kuma a Nijeriya babu abin da ake zuwa a saya a wajenmu shi ya sa ba a bukatar Naira daga ƙasashen waje, balle har buƙatar tata ta yi yawan da za ta yi daraja.
Tasirin hawan dalar a kan ƴan ƙasar
Dole ne wannan tashi da dala ya yi ya yi mummunan tasiri a kan Nijeriya da al’ummarta a cewar masu sharhi.
Dokta Isa Abdullahi ya zayyano abu uku da tashin dalar za su jawo:
1. Hauhawar farashin kayayyaki – Ta’allakar da Nijeriya ta yi a kan sayo komai daga kasashen waje kama daga abinci zuwa tufafi da kayayyakin amfanin more rayuwa, wadanda da kudaden kasashen waje ake sayo su, to dole a samu karin hauhawar farashin kayayyaki a kowane fanni.
2. Ƙaruwar talauci – Idan hauhawar farashi ya yi ƙamari, to dole talauci ya ƙaru ya ta’azzara. Misali, a ce komai na harkar noma daga taki zuwa maganin kwari da kayan amfanin gona sai manoma sun sayo daga waje, to kayan abincin ma da ake nomawa a cikin gida sai ya tashi.
Daga nan kuma sai yawan wadanda ba za su iya sayen abinci ba ba ya karu. Daga cikin manyan nau’ikan talauci har da mutane su kasa sayen abin da za su ci, ko sayen suturar da za su saka ko kuma su kasa biyan abin da ya shafi harkar lafiya da ilimin ‘ya’yansu.
Ko kuma mutane su kasa samun kuɗaɗen biyan haya ko samun gida mai aminci da za su zauna.
3. Rashin tsaro – Duk wadannan matsaloli na karuwar talauci daga baya su suke rikidewa su samar da ta’azzarar rashin tsaro. Saboda iyaye ba sa iya sauke bukatun ‘ya’yansu na ciyarwa da lafiya da ilimintarwa da samar musu tufafi da muhalli, sai yaran su bazama su shiga bin hanyoyin da za su zame wa al’umma alaƙaƙai.
Matakan da suka kamata gwamnati ta ɗauka
Dokta Isa ya ce akwai matsaloli da yawa a Nijaeiyr, ba wai bangaren hada-hadar kudi ba ne kawai tattalin arziki, kamar yadda gwamnati ta fi mayar da hankali a kai.
1. Ya kamata gwamnati ta fito da salon amfani da damar ma’adanai da Allah Ya bai wa kasar.
2. Gwamnati da ‘yan kasuwa su samar da yanayi na fitar da wasu abubuwa kasashen waje ta yadda za a samu shigowar kudaden kasashen wajen sosai.
3. Cike gurbin fitar da danyen man fetur. An bai wa Nijeriya gurbin fitar da ɗanyen fetur ganga 2.4 amma da kyar muke fitar da ganga miliyan 1.8 don samun karin kudade.
4. Dakile masu ta’annati da yi wa gamnati ɓarna da arzikin kasa ta hana yi mata sata.
Akwai ma’adanan da idan aka yi amfani da su yadda ya kamata a Nijeriya za su iya samar wa kasar dalar Amurka biliyan 700, kamar yadda Dele Alake Ministan Ma’adanan kasar ya fada kwanan nan, in ji masanin tattalin arzikin. "Dole Nijeriya ta fito da hanyoyin yakar duk wasu barayin ma’adananta," ya ce.
5. Tace fetur a cikin gida. Dole a nemi hanyoyin yin hakan saboda zai fitar da fetur sannan a sayo tatacce da tsada.
Ya ba da misali da yadda gwamnati za ta iya amfani da matasan yankin Neja-Delta da suke iya tace mai ta ɓarauniyar hanya, ta jawo su jiki ta yi musu lasisi su dinga yin hakan a hukumance.
“Ko da durom-durom za su dinga tacewa ba tare da injina ba, ya fi mana mu sayo daga waje.”
6. Duk dan wajen da zai kafa jari a Nijeriya ya zama dole sai an samu dan Nijeriya a ciki, sannan a samar wa ‘yan kasar ayyukan-yi. Hakan zai sa a samu karin kudaden waje.
7. Farfaɗo da masana'antu da kafa kamfanonin ayyukan noma. Wannan aiki ne da gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da manyan ‘yan kasuwa za su yi don wadatar da kasar da abinci a irin tsari na zamani yadda ya dace.
Hoɓɓasar da talaka zai yi daga bangarensa
Malamin jami’ar ya ce shi talaka a matsayinsa ba shi da cewa a kan kudaden kasashen waje don ba shi da hannu a kan kafa dokoki.
Mafi yawan ‘yan Nijeriya ma ba su taba ganin dala balle su san yaya ake samunta.
Amma duk da haka ya ce a ɗaiɗaikun mutanen ma suna da rawar da za su taka kamar haka:
1. Talaka ya dinga kokarin noma abincinsa da kansa don fin ƙarfin abin da zai ci.
2. Ma’aikatan gwamnati ma su shiga cikin harkar noma ko daga lokaci zuwa lokaci ne ta yadda ko albashinsa bai kai shi ba to noman zai taimaka masa.
3. Mutane su rage kashe kudade a banza, kamar tara motoci masu yawa yana sha musu mai, ko yawace-yawancen da ba kudi zai kawo musu ba da kuma rayuwar karya.