Afirka
Za mu riƙa sayar da litar fetur a kan N960 ga jiragen ruwan dakon mai, N990 ga tankokin mai – Matatar Dangote
Hakan ya biyo bayan wani iƙirari da Ƙungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Nijeriya (IPMAN) da Ƙungiyar Masu Sarin Mai ta Nijeriya (PETROAN) suka yi cewa sun shigo da man fetur cikin ƙasar a farashi mai rahusa fiye da na Matatar Dangote.Kasuwanci
CBN zai ɗauki kowane mataki wajen ɗakile hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya - Cardoso
Cardoso ya ce matakan da CBN ya ɓullo da su suna ƙara wa masu zuba jari ƙwarin gwiwa, sannan a halin yanzu babu wasu ƙorafe-ƙorafe da ake samu game da rashin kuɗaɗen waje idan aka kwatanta da lokutan baya da mutane ƙalilan ne kawai suke iya samu.Afirka
Tinubu ya sanar da matakan rage kashe kudade a ma'aikatun gwamanatin Nijeriya
A watan Janairun wannan shekara ne dai Shugaba Tinubu ya dauki muhimman matakai na rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa, ta hanyar rage yawan mukarrabansa da ke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje daga 50 zuwa 20.Afirka
'Yan Nijeriya sun fara haƙura da amfani da motocinsu saboda tsadar rayuwa
Masu matsakaicin samu a Nijeriya yanzu haka suna sadaukar da jin dadin amfani da motocinsu don zriga-zirga, saboda yadda hauhawar farashin man fetur ta ninka fiye da sau biyar, tun daga lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023.Afirka
'Yan sanda sun ce mutum bakwai ne suka mutu a zanga-zanga a Nijeriya
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta musanta zargin cewa mutum 13 sun rasu inda ta ce mutum huɗu sun rasu sakamakon harin 'yan boko haram, biyu kuma mota ce ta kaɗe su, sannan kuma ɗaya ɗan bijilanti ya harbe shi a yayin satar kayayyakin shago.Afirka
An ba da umarni a ƙara tsaro a kan iyakokin Nijeriya game da shirin zanga-zanga
“Babbar Kwanturola ta kuma bayar da umarni ga manyan Kwanturololi da ke kan iyakoki su tabbatar cewa jami'an da ke aiki a kan iyakoki sun tashi tsaye wajen hana duk wasu ɓata-gari daga ƙasashen waje shigowa ƙasar nan domin aiwatar da mugun nufinsu.”
Shahararru
Mashahuran makaloli