Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta musanta zargin da ƙungiyar Amnesty International ta yi cewa mutum 13 sun rasu sakamakon zanga-zanga wadda aka soma a ranar 1 ga watan Agusta a ƙasar.
Rundunar ta musanta zargin ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce jumullar mutum bakwai ne suka rasu a kwana biyun farko na soma zanga-zangar.
Haka kuma rundunar ta yi watsi da wani zargin da ƙungiyar ta Amnesty International ta yi kan cewa jami’an ‘yan sanda na amfani da dabaru dagangan domin kashe masu zanga-zangar.
“Rundunar ‘yan sanda na son bayar da sahihan bayanai game da abubuwan da suka faru a kwanaki biyun farko na zanga-zangar ƙasa baki ɗaya. A Jihar Borno, mutum huɗu sun rasa rayukansu talatin da huɗu kuma sun samu rauni sakamakon wani hari da mayaƙan Boko Haram/ISWAP suka kai waɗanda suka saje da masu zanga-zangar inda suka tayar da bam,” in ji sanarwar.
“Haka kuma wani lamarin ya faru wanda ya shafi wata mota ƙirar Honda Prelude wadda ba ta da rajista inda ta afka wa masu zanga-zanga, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar farar hula biyu. Direban ya ƙyale motar inda ya gudu daga wurin.
“Duk da cewa an farfasa motar bayan lamarin, an ƙwatota kuma tana hannun ‘yan sanda. Ana ƙoƙarin gano direban da kuma ɗaukar mataki a kansa,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.
“Wani lamarin kuma ya faru a Ƙaramar Hukumar Yauri da ke Jihar Kebi inda gungun wasu matasa suka taru suka sace kayayyakin wani shago. A yayin da suke satar, wani ɗan bijilanti ya harbe ɗaya daga cikin masu satar inda ya kashe shi. A halin yanzu kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kebbi na gudanar da bincike dangane da lamarin. Wannan ne ya kawo adadin waɗanda suka rasu a wuraren zanga-zangar zuwa bakwai.
“Yana da kyau a sani cewa babu wanda aka tabbatar ya mutu a lokacin zanga-zangar baya ga waɗannan da aka lissafo,” in ji sanarwar.
Sai dai ‘yan sandan sun yi ƙarin haske inda suka ce an samu fashi da makami da sace kayayyakin al’umma a wuraren gwamnatin da na ‘yan kasuwa a yayin da ake zanga-zangar.
‘Yan sandan sun ce sun kama wasu daga cikin ɓarayin haka kuma suna aikin gano wasu daga cikin kayayyakin da aka sace.
'Yan sandan sun kuma tabbatar da cewa a kwanaki biyun farko na soma wannan zanga-zanga sun samu nasarar kama mutum 681 a faɗin ƙasar.
Rundunar ta ce a Abuja babban birnin Nijeriya an kama mutum 38 a rana ta farko sai mutum shida a rana ta biyu, a Gombe kuwa an kama mutum 17 a rana ta farko, a rana ta biyu ba a kama kowa ba, sai Jigawa an kama mutum 75 a ranar farko, a rana ta biyu ma ba a kama kowa ba.
A Jihar Kaduna kuwa, a ranar farko an kama mutum 24 a rana ta biyu kuma ba a kama kowa ba sai Jihar Kano ce ke da adadi mafi yawa na waɗanda aka kama inda aka kama mutum 326 a rana ta farko sai kuma mutum 57 a rana ta biyu.
Sai Jihar Katsina an kama mutum bakwai a ranar farko sai a rana ta biyu ba a kama kowa ba sai Nasarawa an kama mutum 50 a ranar farko sai a rana ta biyu ita ma ba a kama kowa ba sai Sokoto an kama mutum 81 a ranar farko sai a rana ta biyu ba a kama kowa ba, kamar yadda 'yan sandan suka tabbatar.
Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Nijeriya
A gefe guda, shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai gabatar da jawabi ga 'yan ƙasar game da zanga-zanga kan tsadar rayuwa da ake gudanarwa.
Wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya fitar ranar Asabar ta ce Shugaba Tinubu zai yi jawabi ranar Lahadi da misalin ƙarfe bakwai na safe a agogon ƙasar.
Sanarwar ta yi kira ga gidajen talbijin da rediyo da sauran hanyoyin sadarwa su watsa jawabin nasa.