Tinubu ya ce a shirye yake a yi sauye-sauye kan dokar harajin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar. /Hoto:Fadar Shugaban Nijeriya

Ranar Litinin da maraice Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi tattaunawarsa ta farko da ‘yan jarida tun bayan da ya karɓi ragamar mulkin ƙasar a watan Mayun shekarar 2023.

A tattaunawar da aka watsa a gidan talabijin na ƙasar, shugaban ya amsa tambayoyi game abubuwan da suka fi ci wa ‘yan ƙasar tuwo a ƙwarya.

Ga biyar daga cikin abubuwan da shugaban ya amsa tambayoyi a kansu da kuma amsoshin da ya bayar.

Cire tallafi man fetur da dala

Da aka tambaye shi game da yadda ya ji ganin irin tasirin da cire tallafi ya yi kan tattalin arzikin ƙasar, Shugaba Tinubu ya ce babu wata hanya da ƙasar za ta iya bi idan ba ta cire tallafi a lokacin da ya cire ba.

Cire tallafin man fetur da kuma dala dai ya haddasa ƙarin tsadar rayuwa a ƙasar. Sai dai kuma shugaban Nijeriya ya ce bai yi nadamar cire tallafin ba.

“Makomarmu muke lalatawa (da tallafin). Arzikin ‘ya’ya da jikokinmu muke kashewa. Ba ma zuba jari. Yaudarar kanmu kawai muke ta yi. Waɗannan gyare-gyaren sun zama dole,” in ji shugaban a lokacin da yake magana game da illar tallafin man fetur da dala.

Dokar Haraji

Da yake amsa tambaya kan dokar sake fasalin harajin ƙasa kuwa Shugaba Tinubu ya ce ya shirya domin tattaunawa da kuma yin sauye-sauye game da ababen da suka janyo ce-ce-ku-ce kan dokar musamman maganar harajin VAT.

Shugaban ya ce sake fasalin dokar na buƙatar tattaunawa da kuma yarjejeniya kuma shi ya shirya domin yin hakan.

Tsadar rayuwa

Da aka tambaye shi kan matakin da gwamnatinsa take ɗauka game da hauhawar farashin kayayyaki, shugaban ya ce: “kawai za mu ci gaba da ƙara yawan abubuwan da ake kai wa kasuwa ne. Za mu yi aiki tuƙuru domin ƙara yawan abubuwa da ake kai wa kasuwa.”

Da aka ƙara jan hankalin shugaban game da illar dillalai masu sayen abubuwa daga manoma domin cin riba, Shugaba Tinubu ya ce shi bai yarda da ƙayyade farashin kayayyaki ba, kuma ko ba jima ko ba daɗe idan aka ci gaba da ƙara yawan abubuwa da ake kai wa kasuwa dillalan za su faɗi.

“Alal misali, dubi farashin man fetur. Na samar da tsarin sayen ɗanyen mai da dala wanda ba su so bi ba. Sun yi jayayya da ni. Na ce to ku bari kasuwa ta yi halinta. Na bar shi. A yanzu farashin ya fara saukowa a hankali,” in ji shugaban.

Daga baya kuma shugaban ya sake magan kan tallafa wa manoma ta yadda za su ƙara yawan abincin da suke samarwa.

“Za mu sake bayar da ƙarin tallafi ga manoma, bashi mai sauƙin kuɗin ruwa, noman zamani mai amfani da injuna. Ba zai yiwu ba a koma irin yadda kakana ya yi noma. Ba zai yiwu ba a halin yanzu. Ya kamata a ƙawata shi, a zauna a kan tarakta a girbe masara da kuma kayayyakin da ake fitarwa,” in ji shugaban.

“Ina ganin hakan ya fi mana a Nijeriya. Kuma muna kan turbar aiwatar da wannan mataki. Ina da fiye da tarakta 2,000 da suke kan hanyar shigowa wannan ƙasa domin noman da ake da injuna,” a cewarsa.

Raba tallafi

Game da batun turmutsutsun da aka samu a wuraren raba tallafi a makon jiya inda fiye da mutum sittin suka mutu kuwa, Shugaba Tinubu cewa ya yi kurakuran waɗanda suka shirya ba da tallafin ne suka janyo turmutsutsun.

“Abin takaici ne mutane ba su tsara taron ba yadda ya kamata. Ya kamata mu kasance masu tsari a rayuwarmu. Ina miƙa saƙon ta’aziyya ga waɗanda suka rasa ‘yan'uwa, amma bayar da kyauta abu ne mai kyau,” in ji Tinubu.

Shugaban ya ce ya shafe shekara 25 yana ba da tallafi a gidansa da ke Legas ba tare da samun irin wannan matslar ba saboda tsari.

“Ko wace al’umma, ko Amerika ce, tana da wurin ba da abinci kyauta. Suna da mutane da ke jin yunwa. A Birtaniya, suna da wuraren ba da abinci da kuma wuraren adana abinci, kuma suna da tsari. Suna layi domin karɓar abinci,” in ji shi.

Tsadar gudanar da gwamnati

Da aka tambaye shi kan ko zai rage yawan ministocinsa domin rage tsadar gudanar da gwamnati, Shugaba Tinubu ya ce shi ba zai rage yawan ministocin nasa ba.

“Ban yi shirin rage yawan ministocina ba. Ni na san dalilin da ya sa na naɗa su. Ba na bai wa mutum aikin da na san ba zai iya yi ba,” in ji shi.

“Dole bayanin aiki ya zama cikakke da kuma ingantacce. Nijeriya ƙasa ce babba. Idan kana son ka ciyar da mutum fiye da miliyan 200, ka yi lissafin yawan ma’aikatan da za ka buƙata. Bari mu mayar da hankali kan inganci. Inganci shi ne abu mafi muhimmanci game da majalisar ministoci. Ina buƙatarsu,” a cewar shugaban.

TRT Afrika