Sanarwar ta umarci jami'an hukumar shige da fice ta Nijeriya da su yi aiki cikin basira da nuna ƙwarewa kuma kada su ci zarafin kowa. / Hoto: AFP

Hukumomin gwamnatin tarayyar Nijeriya sun bayar da umarni a tsaurara matakan tsaro a kan iyakar ƙasar da maƙotanta a yayin da wasu ƙungiyoyi suke shirin gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a ƙasar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, KT Udo ya fitar ya ambato shugaban hukumar yana mai bayar da umarnin ƙara tsaro a cikin ƙasar da ma kan iyakokinta da ƙasashe maƙota.

“Babbar Kwanturola ta Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, KN Nandap, ta bayar da umarni ga dukkan shugabannin yankuna da na jihohi da na gundumomi a faɗin ƙasar nan su ƙara sanya ido sannan su sanya ƙarin matakan tsaro sakamakon shirin da wasu ƙungiyoyi suke yi na gudanar da zanga-zanga a Nijeriya," in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa “Babban Kwanturola ya kuma bayar da umarni ga manyan Kwanturololi da ke kan iyaka su tabbatar cewa jami'an da ke aiki a kan iyakoki sun tashi tsaye wajen hana duk wasu ɓata-gari daga ƙasashen waje shigowa ƙasar nan domin aiwatar da mugun nufinsu.”

Sanarwar ta umarci jami'an hukumar da su yi aiki cikin basira da nuna ƙwarewa kuma kada su ci zarafin kowa.

Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta ɗauki wannan mataki ne bayan sauran jami'an tsaron ƙasar da suka haɗa da rundunar 'yan sanda da rundunar soji sun ja kunnen masu shirin gudanar da zanga-zangar, suna masu zargin cewa akwai yiwuwar ta rikiɗe zuwa tarzoma kamar yadda ya faru a Kenya.

Sai dai masu shirin zanga-zangar, wadda aka tsara gudanarwa daga ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa, sun kafe kai-da-fata cewa sai sun yi zanga-zangar domin nuna wa gwamnati matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar sakamakon matakan da gwamnatin Bola Tinubu ta ɗauka tun da ta hau kan mulki a 2023.

Sun ƙara da cewa matakan da gwamnati ta ɗauka na cire tallafin fetur da barin kasuwa ta yi halinta kan kuɗin ƙasar wato Naira sun ƙara jefa ta cikin bala'in, abin da ya sa hauhawar farashi ta kai kimanin 34.19.

Shi kansa Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga masu shirin zanga-zangar da su ba shi lokaci domin aiwatar da "kyawawan" manufofinsa, inda kuma ya gana da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnoni da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da sauransu domin rarrashin masu shirin zanga-zangar.

TRT Afrika