Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanar da wasu sabbin matakai na rage kashe kuɗaɗe a ma’aikatun gwamnati.
A wata sanarwa a mai taimaka masa kan harkokin watsa labarai Bayo Onanuga ya fitara ranar Alhamis, Shugaba Tinubun ya zayyana matakan kamar haka:
Ya taƙaita yawan motocin da ministoci da shugabannin ma’aikatun gwamnatin tarayya za su dinga amfani da su a ayarinsu zuwa guda uku.
Ba za a ƙara musu yawan motoci saboda zirga-zirgarsu ba.
A watan Janairun wannan shekara ne dai Shugaba Tinubu ya dauki muhimman matakai na rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa, ta hanyar rage yawan mukarrabansa da ke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje daga 50 zuwa 20, sai kuma ya rage jami’ai masu raka shi bulaguro a cikin gida zuwa 25.
Hakazalika ya rage yawan tawagar mataimakin shugaban kasar zuwa jami’ai biyar a tafiye-tafiyen kasashen waje da 15 na tafiye-tafiyen cikin gida.
A cikin umarnin da ya bayar a yau, Shugaba Tinubu ya kuma umurci cewa daga yanzu jami’an tsaro biyar ne kawai za su dinga kasancewa da kowane minista da shugabannin hukumomi. Tawagar tsaron za ta kunshi ‘yan sanda hudu da jami’in DSS guda daya.
Ba za a ba da karin jami’an tsaro ba, in ji umarnin nasa.
Shugaba Tinubu ya umurci mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da ya hada hannu da jami’an soji, da jami’an tsaro domin sanin matakin da ya dace a rage na jami’an tsaron da za su dinga bin ayarin motocinsu.
Ana sa ran dukkan jami'an da abin ya shafa za su bi wadannan sabbin matakan nan take, tare da jaddada muhimmancin wadannan sauye-sauye.