Matatar mai ta Dangote ta bayyana cewa ta fara sayar da fetur a kan naira 990 kan kowace lita da za a loda a tankar dakon mai ko kuma naira 960 kan kowace lita ga jiragen ruwa, kamar yadda mai magana da yawun kamfanin ya bayyana.
Wannan ya biyo bayan wani ikirari da Kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Nijeriya (IPMAN) da kuma Kungiyar Masu Sarin Mai ta Nijeriya (PETROAN) suka yi cewa sun shigo da man fetur cikin kasar a farashi mai rahusa fiye da na Matatar Mai ta Dangote.
A makon jiya ne yayin wata ganawa da manema labarai dillalan suka yi ikirarin cewa suna samun mai daga ƙetare a farashi mai rahusa fiye da na Dangote.
Sai dai a wani martani da matatar mai ta Dangote ta mayar ranar Lahadi, matatar ta ce man da bai kai ingancin nasu ne kawai za a iya shigo da shi cikin ƙasar a farashi ƙasa da nasu.
A wata sanarwa da matatar mai ta Dangote ta fitar wacce ke ɗauke da sa hannun Babban Jami’in Hulɗa da Jama’a na Kamfanin, Anthony Chiejina, ta ce matatar ta bi tsarin farashin Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL) ne, inda ya ce farashin matatar man Dangote ya yi ƙasa na man da ake loda wa jiragen ruwa da farashin NNPLC.
Sanarwar ta ci gaba cewa dillalan man sun yi iƙirarin cewa za su iya shigo da man fetur cikin Nijeriya a ƙasa da farashin Dangote. Matatar man ta ce farashinta daidai yake da wanda ake sayar da fetur a kasuwannin ƙasashen duniya kuma ta ce farashi ne mai kyau idan aka kwakwanta da farashin da ake shigo da shi daga ƙasashen waje.
Daga nan sanarwar ta ce idan wani ya yi iƙirarin cewa zai iya samar da man fetur a cikin ƙasar kan ƙasa da yadda "muke sayarwa, to hakan na nufin an shigo da man fetur mara inganci ba tare da la’akari da lafiyar ’yan Nijeriya da kuma lafiyar ababen hawa ba."
Sanarwar ta yi zargin cewa hukumar da ke kula da ingancin man fetur a Nijeriya (NMDPRA) ba ta da dakin bincike da zai gano man fetur mara inganci da aka shigo da shi cikin kasar daga kasashen ketare.
Kazalika sanarwar ta ce bayan cire tallafin man fetur, kamfanin NNPCL ya sanya farashin mai ga dillalai na cikin gida a kan naira 971 a kan kowace lita wanda ake loda wa jiragen ruwa da kuma naira 990 kan kowace lita ga tankokin mai. Kamfanin ya ce wannan suka yi la’akari da shi kuma suka sanya farashinsu kasa da hakan, inda muke sayar da kowace lita a kan naira 960 ga jiragen ruwa da kuma naira 990 a kan kowace lita ga tankokin mai.
Sannan Matatar mai ta Dangote ta ce ta yi hakan ne da kyakkyawar niyya da kuma kishin kasa kuma a hakan ta fara sayar da man fetur din ba tare sanin farashin dalar da za ta yi amfani da shi ba wajen biyan danyen man da ta karba ba.
Matarta ta kuma yi zargin cewa wani kamfani kasuwanci na duniya ya karbi hayar wani defo a kusa da Matatar mai ta Dangote, inda a cewar sanarwar zai rika samar da mai mara inganci da zai rika gogayya da man Dangote mai inganci sosai.
Matatar man ta ce wannan cikas zai jawo wajen bunkasar matatar mai ta cikin gida. Kuma sanarwar ta ce ba bakon abu ba ne yadda wasu kasashe a nahiyar Turai da Yammacin Duniya suke kare masana’antunsu na cikin gida don samar da ayyuka da kawo ci gaba ga tattalin arzikinsu.
Sanarwar ta ce matatar za ta ci gaba da samar da mai fetur mai inganci da rahusa da aka tace a Nijeriya kuma ta bukaci jama’a da su yi watsi da labaran karya da wasu suke yadawa game da Matatar Mai ta Dangote.