Ajaero ya ce an yi masa tambayoyi kan zargin bayar da tallafin ta’addanci da ya shafi wani dan Birtaniya, Andrew Wynne.

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta saki shugaban kungiyar kwadago Joe Ajaero, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Ajaero, wanda ya tabbatar da sakinsa ga Channels, ya ce ‘yan sandan sirrin sun ba shi damar komawa gida da misalin karfe 11 na daren ranar Litinin.

An sake shi 'yan mintoci kadan kafin wa'adin karfe 12 na dare da kungiyar kwadago ta bayar, wanda ta ɗauki mataki a wani taro da ta gudanar cewa ko a sake shi ko ta tsunduma jayin aiki na duka ƙasa.

Shugaban Kungiyar Kwadago ta Nijeriya ya ce an shafe kimanin sa’o’i 15 ana masa tambayoyi tun bayan kama shi da misalin karfe 7 na safe a filin jirgin sama na Abuja.

Ajaero ya ce hukumar DSS ɗin ta ƙwace fasfo dinsa na tafiya.

Shugaban kungiyar kwadagon ya ce duk da cewa hukumar DSS ce ta tsare shi, wasu jami’an ‘yan sanda kuma sun je wajen domin sake yi masa tambayoyi a ofishin DSS da ke Abuja kan zanga-zangar #EndBadGovernance da aka yi a fadin kasar a watan Agusta.

Ajaero ya ce an yi masa tambayoyi kan zargin bayar da tallafin ta’addanci da ya shafi wani dan Birtaniya, Andrew Wynne.

Shugaban kungiyar kwadagon dai yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Birtaniya ne a jiya Litinin domin halartar taron kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) inda aka kama shi a filin jirgin saman Abuja.

TRT Afrika