Tabarbarewar tattalin arzikin Nijeriya da hauhawar farashin man fetur ya tilasta wa Bolaji Emmanuel sallamar direbansa da haƙura da hawa motarsa kirar Honda Pilot, yayin da yake fama da tsadar rayuwa.
Ba Emmanuel ne kaɗai ke cikin wannan yanayi ba. Da yawan mutane a ƙasar wacce ta fi yawan al'umma a Afirka suna haƙura da motocinsu saboda tsadar kula da su.
Farashin man fetur ya ƙaru matuƙa har fiye da sau biyar tun daga lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023.
Na ajiye motata a gidan ɗana. Yanzu motar haya nake hawa," kamar yadda Emmanuel mai shekara 72, wanda ya daɗe da yin ritaya a matsayin ma'aikacin lafiya, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP.
"Lamarin ba daɗi kam, amma yanayin tattalin arzikin ne ya jawo haka."
Janye tallafin man fetur
Tun hawansa karagar mulki, Tinubu ya kawo karshen tallafin man fetur da ke matuƙar cin kudi tare da sakin kudin Naira don kasuwa ta yi halinta, a sauye-sauyen da jami’an gwamnati da manazarta ke cewa zai farfado da tattalin arzikin kasar da kuma jawo masu zuba jari.
Sai dai a cikin ƙanƙanin lokaci, Nijeriya ta fuskanci daya daga cikin mafi munin rikicin cikin shekaru tare da hauhawar farashin kayayyaki a tsawon shekaru uku.
Ana sayar da litar man fetur a kusan naira 195 kafin Tinubu ya hau mulki. Farashin ya tashi zuwa akalla Naira 998 ($0.61) kan kowace lita a Legas da kuma Naira 1,030 a babban birnin tarayya Abuja, a farkon watan Oktoba. Farashin litar man na iya kaiwa har naira 1,300 a wasu wuraren a ƙasar.
Hauhawar farashi mafi yawa a shekara 30
Haɓakar hauhawar farashin kayayyaki ya kai kashi 34.19 cikin 100 a watan Yuni, mafi yawa a cikin shekara 30.
Wahalar sayen wutar lantarki na ƙara jefa jama’ar ƙasar cikin wahala, inda sama da kashi 40 na al’ummar kasar ke fama da talauci, a cewar Bankin Duniya. Ana sa ran wannan adadi zai ƙaru a 2024 da 2025, kafin ya daidaita a 2026.
Mutane masu matsakaicin samu a Nijeriya, waɗanda yawan su ya kai kusan kashi 20 cikin 100 na al'ummar kasar a shekarar 2020, yanzu haka sun sadaukar da jin dadin amfani da motocinsu domin su sauƙaƙa wa kansu.
Dillalan motoci a Legas da Abuja sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa, sun ga mutane da dama suna sayar da motocinsu masu amfani da fetur da masu shan mai sosai don sayen masu sauƙin shan mai.
Motoci sun rage zirga-zirga a kan tituna
Wani dillalin motoci a Abuja, Maji Abubakar, ya shaida wa AFP cewa, "A gaskiya mutane na sayar da manyan motocinsu a kwanakin nan." "Matsalar ita ce, ko da za a saka su a kasuwa, ba a bukatar su sosai."
Ya ƙara da cewa, sama da shekara guda kenan na sayar da motata mai injin Silinder takwas, kuma babban dalili shi ne farashin man fetur.
Sakamakon yadda zirga-zirgar ababen hawa ya ragu, a yanzu ko irin cunkoso da ake samu a titunan Legas ma ya ragu.
Wani ɗan kasuwa mai suna Elijah Bello a jihar Ogun da ke kudancin kasar ya shafe watanni yana neman wanda zai sayi motarsa kirar Lexus RX 350 SUV.
Tuni ya sayi wata ƙaramar Toyota Corolla marar shan mai sosai don maye gurbin waccar.
Yanayin sayar da motoci da aka fara a bara, "zai tsananta" kuma "za mu daina ganin motoci masu a kan tituna", in ji Bunmi Bailey, shugaban cibiyar leƙen asiri ta SBM Intelligence.
Bailey na iya cika karamar motarsa da man naira 55,000. "Zan iya amfani da shi na tsawon makonni biyu don zuwa wajen aiki yau da kullum," in ji shi, yayin da babbar motarsa ke shan man fetur na Naira 110,000 a cikin kwanaki takwas kacal.
Raguwar buƙatar sayen motoci
Kasuwar sabbin motoci ta ragu da kashi 10 zuwa 14 cikin 100 a shekarar da ta gabata, in ji Kunle Jaiyesimi, mataimakin darakta a kamfanin sayar da motoci na CFAO da ke Legas.
"Mota ƙirar SUV da ake sayar da ita a kan Naira miliyan 40 zuwa 45 (dala 24,000 zuwa dala 27,000) kimanin shekaru biyu da suka wuce, a yanzu farashinta ya kai tsakanin miliyan 95 ko 100 ($57,000 zuwa $60,000). ," in ji Jaiyesinmi.
Sai dai hauhawar farashin kayayyaki ta sa mutane masu matsakaicin samu nesanta da motoci ƙirar Amurka da Japan suna komawa na waɗanda aka ƙera a China.
Wasu na komawa amfani da keke, duk da rashin samar da ababen more rayuwa a garuruwa kamar Legas, inda ake yawan samun hadurran motoci.
"Tabbas, mun lura an koma amfani da keke sosai ... a tsawon watanni tun lokacin da farashi man fetur ya fara hawa," in ji Femi Thomas, shugaban ƙungiyar da ke inganta amfani da keke ta FT Cycle Care da ke Legas
Dandalin isar da abinci Glovo ya ce ya samu karuwar sha'awar kai saƙonni da keke a tsakanin 'yan aikensa.
Kimanin kashi 20 cikin 100 na odar ana kai su ne ta hanyar keke, kamar yadda jami'in hulda da jama'a na dandalin a Nijeriya Chidera Akwuba ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.