Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya gabatar da jawabi ga 'yan kasa a yammacin Litinin din nan, inda ya mayar da hankali kan kokarin da gwamnatinsa ke yi na rage radadin matsin tattalin arzikin da al'ummar kasar ke fama da shi.
Ya bude jawabin nasa da cewa "Ina so na yi muku magana kan tattalin arzikin kasa, saboda yana da muhimmanci ku fahimci dalilan da suka sa na dauki matakai da tsare-tsaren da na gabatar don kawar da manyan kalubalen da kasarmu ke fuskanta."
Ga manyan batutuwan da shugaban ya zayyana a jawabin nasa:
1. Samar da bas 3000 mai daukar mutum-20
Karanta labari mai alaka: Ina jin radadin da kuke ji kan cire tallafin fetur – Shugaba Tinubu
2 Kara albashin ma'aikata
"Ina so na sanar da ma'aikata cewa: Karin albashinku na nan tafe," in ji shugaban kasar.
Ya ce gwamnati ta amince ta daga darajar mafi karancin albashin da za a biya ma'aikata a fadin kasar, kuma za a saka batun a kasafin kudi don ya fara aiki nan ba da jimawa ba.
Gwamnatin ta bayyana cewa ta fitar da hatsi da ya kai tan 200,000 daga rumbun hatsi na gwamnati, don raba wa ga magidanta a fadin kasar.
Haka nan gwamnati za ta samar da taki da iri da ya kai tan 225,000, hade da sauran kayayyakin noma, don tabbatar da abincin da al'umma ke ci yau da kullum ya zamo mai rangwame.
A yunkurinta na karfafa masana'antu su inganta matakinsu na samar da ayyukan yi, gwamnati za ta kashe Naira biliyan 75 tsakanin watan Yuli na shekarar 2023 da Maris na 2024.
Manufar ita ce samar da kudi ga kamfanoni 75 masu kyakkyawan alamomin habaka, don karfafa damarsu ta samar da kayayyaki.
Kowane kamfani cikin 75 din nan, zai samu bashin Naira biliyan 1, da kudin ruwa kashi 9% duk shekara, mai lokacin biya na watanni 60 ga manyan bashi, sai watanni 12 ga masu neman jarin gudanarwa.
5 Daukar mataki kan hauhawar farashin man fetur
Baya ga wannan, shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cimma nasarar adana Naira tiriliyan daya sakamakon janye tallafin man fetur kuma za ta yi amfani da kudin wajne inganta rayuwar 'yan Nijeriya.