Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana fargabarsa kan yadda ‘yan Nijeriya suke hulda tamkar abokai idan suka fita daga kasar, yayin da suke hulda kamar abokan gaba idan suna cikin kasar.
Obasanjo ya ce ‘yan kasar da ke kasashen waje suna kasancewa ababen alfahari ga Nijeriya a fannonin sana’o’insu.
Tsohon shugaban Nijeriya ya bayyana hakan ne a wata liyafa da aka yi a New Brunswick, da ke Jihar New Jersey a Amurka, yana mai neman ‘yan Nijeriya da ke ketare su kasance ‘yan kasa na gari a duk inda suke zaune.
A cikin wata sanarwar da matamakin Obasanjo na musamman kan harkar labarai Kehinde Akinyemi ya fitar, Obasanjo ya bayyana gamsuwarsa game da hadin kan da ‘yan Nijeriya suka nuna a Amurka.
Ya nemi ‘yan Nijeriyar da ke ketare su maimaita irin wannan hadin kan idan suka koma gida Nijeriya.
Ya yi maganar ne a madadin tawagar manyan sarakunan gargajiya da masana, wadanda suka hada da Olowu na masarautar Owu, Oba Saka Matemilola.
Ya ce, “Akasari ‘yan Nijeriya suna matukar hada kai idan suna ketare, amma za su zama wani abu daban idan sun koma kasar, saboda haka, ina son dukkanku ku zama ‘yan kasa na gari, ba a inda kuke kawai ba, har in kun dawo gida Nijeriya.”
Ya yaba wa jami’an gudanarwar Jami’ar Rutgers kan irin tarbar da suka yi wa tawagar da kuma tattaunawar da suka yi da su.