Wani jirgi mai saukar ungulu ya fadi a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya.
Lamarin ya faru ne ranar Talata a unguwar Oba Akran da ke Ikeja.
Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya (NEMA) suna wurin da lamarin ya auku.
Amma kawo yanzu dai ba su bayani game da yawan mutanen da lamarin ya rutsa da su ba.
Sai dai gidan talbijin na Channels TV ya ambato wani jami’in NEMA yana cewa mutum biyu ne a cikinsa.
Babban jami’in NEMA da ke kula da shiyyar kudu maso yammacin Nijeriya, Ibrahim Farinloye, ya wallafa sako a dandalin WhatsApp na hukumar da ke cewa, ko da yake ba a san sunan matukin helikwaftan ba, amma an ceto mutum biyun da ke cikinsa.
TRT Afrika da abokan hulda