An gudanar da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a manyan birane kasar. Hoto / Reuters

Daga Charles Mgbolu

Kishin kasa, wanda ake bayyanawa soyayya marar sharadi, mika wuya da zama cikin shirin sadaukar da kai don wanzuwar kasa, ya dauki sabon salo a lokacinda aka kalle shi da idanuwan ra'ayi mabambanta.

Daga asalinta na Girka da Roma - kalmar ta samo asali daga kalmar patri da ke nufin kasa a yaren Latin - kalmar ta kishin kasa ta smau ne ta hanyar fahimta da fassarar abubuwan da 'yan kasa suke ji game da kasa.

To, a ina matsayar kishin kasa ta ke a Nijeriya, a loakcin da matsaloli tattalin arziki da hauhawar farashi suka janyo bacin rai da karyewar gwiwa ga 'yan kasa?

"Matasa 'yan Nijeriya da dama na bakin ciki; ba sa jin dadin halin da tattalin arziki ke ciki a yanzu haka, da gwagwarmayar da ake yi na ganin an amfani kasa da za a yi alfahari da ita." in ji dan jarida Nnamdi Ojiego yayin tattaunawa da TRT Afirka.

Rashin nasara

Daga masu zanga-zanga da suka daga tutar Rasha a zanga-zangar baya-bayan nan a wasu yankunan kasar, zuw aga yadda wasu uka ki rera sabon taken kasa, akwai bacin rai da dugunzuma a kowanne bangare.

Kalubalen tattalin arziki a kasar na sanya komai ya zama cikin wahala. Da yawan mutane na neman kowacce hanya da za su bi don magance damuwar da suke ciki. Kishin kasa kamar yadda muka sani, babu shi ko kuma ba shi da wani karfi a zukatan matasanmu." in ji Ojiego.

Wani lauya mazaunin Legas Ebuka Iwueze na da ra'ayin cewa gwagwarmayar tattalin arziki da neman abin kaiwa baki ta bayar da gudunmowar shiga halin da ake ciki, duk da cewar bai amince da wannan abu na rashin kishin kasa da aka nuna ba.

Ya bayyana cewa "Halin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu ba dalili ba ne da zia sanya ka daga tutar wata kasa a yayin zanga-zanga sannan ka yi kira ga sojojin wata kasar da su kawo maka dauki. Amma kuma ba zai yi wu ka daki mutum ka hana shi kuka ba."

Iwueze na da ra'ayin cewar ana tsammanin irin bacin ran da tsadar rayuwa ta janyo a Nijeriya tun shekarar da ta gabata zai iya haifar da wani abu marar dadi.

"Wasu za su iya mayar da martani ga lamarin ta wata hanyar daban. Mutane na cikin dimuwa, musamman a arewacin Nijeriya, inda yunwa da cututtuka suke da yawa. Idan mutane suka ga wata hanya ta amayar da bacin ransu, za su yi amfani da ita." in ji shi.

Martani mai tsanani

Da yawa na kallon yadda ra'ayin nuna rashin kishin kasa ke bayyana, ana ganin hakan a yadda ake rusawa da lalata kayayyaki a yayin zanga-zangar, wand aabu ne da ke kira da a zo a dauki matakan da suka dace.

'Yan majalisar dokokin Nijeriya na shawarar yanke hukuncin daurin shekaru 10 ga ayyukan zagon kasa irin wadannan na 'lalata kayan jama'a' ko "kin rera taken kasa".

An janye kudirin dokar da aka gabatar a gaban majalisar bayan suka da aka yi masa sosai.

"Mataki ne marar kyau da bai dace ba," in ji Iwueze. Ya ci gaba da cewa "ba za ka iya amfani da doka wajen tirsasawa mutane bayyana ra'ayinsu ko nuna kishin kasa ba a bayyane."

Amma shin rashin tsayayyen ra'ayi kan wane aiki ne za a yi wa kallon rashin kishin kasa?

Wasu bidiyo da aka fitar a yayin zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa sun nuna yadda wasu masu zanga-zangar suke daga tutar Rasha suna kira ga Moscow da ta "kubutar" da su. Wannan ya jayo ofishin jakadancin Rasha a Nijeriya fitar da sanarwar cewa kasarsu ba ta da hannu a wannan abu.

Auna kalamai

‘Yan sandan Nijeriya sun ce an kama mutum sama da 90 dauke da tutar ƙasar Rasha.

“Zai yi wahala a kare wadannan mutane a kotu domin ba za a ɗauki uzurin cewa halin da tattalin arzikin kasar ke ciki ne ya sa suka aikata laifuka ba,” in ji Iwueze.

Ojiego ya yi imanin cewa ya kamata a fara gangamin wayar da kan jama'a don hana irin wadannan ayyuka. "Za mu iya ƙyamar 'yan siyasa, amma dole ne mu koya wa mutane su so kasarsu kuma mu yi duk abin da za mu iya don kare ta," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

A nata bangaren, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ta roƙi a yi hakuri, inda ta yi alkawarin nan ba da daɗewa ba za a ga amfanin manufofinta.

"Na roƙe ku, ku ƴan'uwana, ku ƙara 'yar ƙaramar sadaukarwa don ci gaban ƙasarmu. Domin amincewarku da imaninku a gare mu, ina tabbatar muku cewa sadaukarwarku ba za ta tafi a banza ba," in ji Tinubu a bara, jim kaɗan bayan cire tallafin man fetur.

'Yan Nijeriya sun ce sun gaji da jira, amma watakila ba su da zaɓi.

"Hanya daya tilo da za a dawo da kishin kasa ba tare da bata lokaci ba ita ce ta sake farfado da tattalin arzikin kasar. Idan har al'umma na cikin yunwa, to fa shawo kan mutane don su zama masu kishin ƙasa abu ne mai wahala," Iwueze ya shaida wa TRT Afrika.

TRT Afrika