Daga Mazhun Idris
Ana ci gaba da samun sabbin rahotanni kan matsalar nan ta kwacen waya da take kamari a birnin Kano da ke Arewacin Nijeriya.
Rahotannin suna nuna wannan masifa tana kara ta’azzara a halin yanzu, duk da da ma can lafawa ta yi.
Abin ya fara tayarwa da mazauna birnin hankali, saboda ko a cikin makon nan an tabbatar da mutuwar wani matashi da kuma jikkata wasu da dama da aka yi a kokarin kwace musu waya.
A kwanakin baya ma an jiyo mai magana da yawun Rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Kano yana bayyana yadda wasu masu kwacen waya suka raunata wani dan sanda.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa ya je, “Ziyarar duba abokin aikinsa “Musa Aliyu (Khan) wanda wasu bata gari suka yi wa rauni da yunkurin kwace masa waya.”
Daga ranar Alhamis zuwa Juma'ar nan muhawara da kiraye-kiraye sun kaure a shafukan sada zumunta da ma wuraren tattaunawa, bayan labarin mutuwar wani matashi da masu kwacen wayar suka hallaka a ranar Alhamis din.
Mutane sun yi ta kira kan a gaggauta magance wannan matsala da ke janyo asarar dukiya har ma da rayukan al’umma.
Wasu ma sun bayyana yadda abin ya taba faruwa da su.
Me mutane ke cewa?
Mutane sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu a kafafen sadarwa. Sannan an yi ta wallafa hotuna da sunayen wadanda zuwa yanzu aka tabbatar da cewa masu kwacen wayar ne suka yi ajalinsu.
Kazalika wasu kuma sun bayyana wuraren da suka ce a nan aka fi yin wannan muguwar aika-aika a cikin Birnin na Dabo, kamar irin su:
- Titin Makarantar Legal
- Dan Agundi wajan ofishin Hisba
- Wajen Masallachin Idi na Sarki
- Titin I B B
- Titin Sitadiyom na Kofar Mata
- Tal'udu
- Kofar Wambai
- Zaria Road
- France Road
- Bakin Kasuwar Rimi
- Zoo road
- Court Road
- Kuntau, da sauran wasu wuraren.
Wasu mutanen da dama kuma na kira ne da aka fara daukar tsattsauran hukunci kamar yanke wa duk wanda aka kama da laifin, hukunci kisa, yayin da wasu ke ganin ya kamata mutane su dinga daukar hukunci a hannunsu idan suka kama su.
Sai dai wani fitaccen mai amfani da shafin Facebook Yakubu Musa ya wallafa a shafinsa cewa ba daukar doka a hannu ce mafita ba.
"Har yanzu mutane ba su gane illar jungle justice ba. Kofa ce daga an bude ta to an bude kofar barna. Za ka sha mamaki inda za a kashe wanda ba ruwansa. Matsalar nan fa matukar an hada kai tsakanin gwamnati da al'umma to za a iya shawo kanta.
"Gwamnati ta fito da matakai, jama’a su ba da hadin kai. Shin za ka iya ba da rahoto in kanin ka ko danka yana wannnan aika-aika?"
Da yake tattaunawa da TRT Afrika, wani jami’in tsaro na ICSIS wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya ce “za a iya cewa wannan matsala ta fi karfin jami’an tsaro su kadai”.
“Akwai bukatar rukunonin mahukunta da ke cikin al’umma su dauki matsalar a matsayin wadda kowa yake da alhaki. ‘Yan jaridu da malamai duk sai sun shigo don a yaki matsalar.”
Lokutan da aka fi yin aika-aikar
Da yake sharhi kan wasu matakai da gwamnati take dauka jami'in tsaron ya ce, “Mun ga tasirin hana zirga-zirgar ababen hawa na haya da dare a Kano, wanda mahukunta suka yi. Wannan ya rage damar yaduwar munanan laifuka da daddare.”
Yawanci dai, da dare ne aka fi shiga tarkon masu kwacen waya, haka kuma ‘yan daba sukan yi zuga tsakiyar rana don yin aika-aikar. Amma akan samu wasu bata gari, yawancinsu matasa da ke amfani da muggan makamai rana tsaka.
Sukan yi amfani da wuka ko adda, ko kuma a wasu lokutan sukan fizge wayar ne ta karfi ko bayan sun shammaci mutum.
An sha samun lokutan da hakan ke faruwa cikin ababen sufuri na jama’a, kamar keken adaidaita sahu, inda akan zargi hannun wasu masu sana’ar. Sai dai kuma a wasu lokutan su kansu matukan ne suke fada wa tarkon azzaluman.
Duk da masu tafiya a kafa, da masu hawan babura aka fi yi wa kwacen, a wasu lokutan ma akan tsayar da mota a hanya, a nemi na cikin motar su miko wayoyinsu bayan an musu barazana da makami.
TRT Afrika ta kuma tambayi masanin tsaron game da hanyoyin rage hadarin kwacan waya ga daidaikun mutane. Sai ya ce, “Mutane su rage amfani da babbar waya a bainar jama’a kamar tsakiyar hanya, musamman da dare ko a cikin lungu”.
Ya kuma ba da shawarar cewa, “Mutane su daina yin dare a inda bai kamata ba. A sauran wurare kuma, a guji yawo da dare ko fitowa da jijjifin asuba, idan ba da kwakkwaran dalili ba.”
Ko kafa dokar hukuncin kisa kan kwacen waya za ta taimaka?
Kiraye-kirayen mutane kan gaggauta magance yawaitar kwacen waya a birnin Kano ta kunshi shawarwarin yadda kowa yake ganin ya kamata a tunkari matsalar.
Wasu na ganin sai an kawo wasu dokoki da za su dakile matsalar, musamman hanyoyin da masu laifim suke bi su ci moriyar ta’asar tasu, wato siyar da kayan satar.
Idan za a iya ganowa da kama wadanda ke siyan wayoyin sata, to bincike zai iya kaiwa ga su kansu bata garin.
Masanin da TRT ta tattauna da shi ya ce,”A tsaurara tanade-tanaden doka da hukuncin shari’a, kamar ka’idojin bayar da beli. A kirkiro da hukunci mai tsanani kan masu aikata lafin kuma a kafa kotun tafi-da-gidanka don gaggauta yin hukunci.”
Wasu matakan daban
Har ila yau, akwai masu ganin dacewar yin sabuwar doka da za ta kallon kwacen waya a matsayin fashi da makami.
A cikin masu irin wannan ra’ayi, akwai wani shahararren dan fina-finan Hausa, mai suna Abba Almustapha. Ya wallafa a shafinsa na Twitter mai lakabin Abba El-mustapha @abbaelmustaph1, cewa yana goyon bayan kiran.
“Muna Kira da babbar murya ga kafatanin Yan majalisun mu na jahar Kano da zarar an rantsar daku Abin farko da muke da bukata shine kuyi Dokar Kisa Akan Duk Wanda Aka Kama Da Laifin Kwacen Waya a Jihar Kano.”
Amma da TRT Afrika ta nemi jin ta bakin masanin harkar tsaro, sai ya ce “Da wahala haka ta yiwu, saboda yawanci laifin bai kai na fashi da makami ba. Amma dai masana shari’a su za su fayyace mana”
“Amma za a iya ware wata kafa nuna yadda ake shari’ar masu wannan laifi, lowa ya gansu, kuma a nemo iyayensu idan yara na kanana. Ana yawan zargin iyaye da yin sakaci wajen tarbiyar ‘ya’yansu.”