Daga Dayo Yussuf
Gwagwarmayar matasa na yaɗuwa a kasashen Afirka, nahiyar da ke da manyan damarmaki da suke fuskantar burace-buracen da aka gaza cim mawa.
Shafukan sada zumunta, fagen zamani na ma'unin ra'ayoyin jama'a, na tattare da tunane-tunanen da ke goyon bayan ra'ayoyin mutane da dama a fadin Afirka da suke tunkarar gwamnatocinsu suna neman bahasi daga shugabanninsu.
Da yawa na yi wa hakan kallon al'amarin da zamaninsa ya zo.
Idan zanga-zangar adawa da sabbin haraji da matasa 'yan zamani suka jagoranta kwanan nan a Kenya na fito da ɓacin ran jama'a, ana yi wa ingiza zanga-zanga a wasu yankunan nahiyar kallon ma'aunin yadda jama'a suka kosa da shugabanci, rashin damarmakin tattalin arziki da cinhanci da rashawa.
Duk da cewar barna da satar kayan jama'a sun gurbata zanga-zangar a Kenya, kalaman 'KenyaProtests (zanga-zangar Kenya) na ci gaba da jan hankali.
A Nijeriya, matasa na shirin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar a ranar 1 ga Agusta don neman ilimi kyauta, kawo karshen matsalar abinci, da a dauki matakan dakatar da hauhawar farashi.
Afirka ta Kudu ma, ta fuskanci korafe-korafe kan matsin tattalin arziki.
Amon matsaloli iri guda
Matsaloli iri guda da ke damun jama'a su ne damuwar rashin daidaito wajen samun arziki, rashin ayyukan yi, da cinhanci da rashawa.
Matasan Afirka da dama na jin cewar gwamnatocinsu sun gaza samar musu da damarmaki da goyon bayan da suke bukata don rayuwa mai kyau.
"Ina tunanin abin ya fi addabar matasa saboda yadda a yanzu sun fi fahimtar halin siyasa sama da kowanne lokaci a tarihi," Mike Muchiri, matasin dan gwagwarmaya ya fada wa TRT Afirka.
"Namu dai ra'ayi ne da ke bisa doron ilimi kan me ke gudana a fagen siyasa. Mun fahimci yadda kowanne bangare da ma'aikata suke aiki da kuma yada ake yin siyasa," in ji shi.
Matasan Kenya da ke zanga-zanga a tsawon sama da wata guda, sun sha alwashin ci gaba da matsa lamba, har sai sun ga wani "ƙwaƙƙwaran sauyi."
Matasan Uganda ma na kalubalantar halin da kasarsu ke ciki.
Tuni gwamnatin Nijeriya ta fara samar da wasu tsare-tsaren neman sulhu don ganin ba a yi zanga-zangar da ka iya ɓarkewa a kowanne lokaci ba.
Kwanaki kafin gudanar da znaga-zangar saboda matsalolin shugabanci da tsadar rayuwa, gwamnatin Bolan Ahmed Tinubu ta ba wa 'yan kasar aiki a kamfanin mai na kasa a biliyoyin kudade, da ma sauran tsare-tsare don karya musu gwiwa su fasa zanga-zangar.
Amma kira ga a gudanar da znaga-zangar na nan har yanzu.
Alkawuran da za a kiyaye
To me za a yi ko wane sauyi za a kawo idan matasan kasa suka fita tituna suna kalubalantar gwamnatin wannan lokaci?
"Abu na farko shi ne kyakkyawan jagoranci," in ji Dr Bello Galadanchi, malami kuma kwararre a Nijeriya yayin da yake tattaunawa a TRT Afirka.
"Abinda suke so (Masu zanga-zanga) sama da komai shi ne gaskiya da shugabancin da zai kula da al'umma."
Tabbas, bukatar neman wani abu cikin gaggawa na iya bambanta daga kasa zuwa kasa, amma za ku yi mamaki idan kuka ga yadda ake da bukatu iri guda da yawa.
Inshorar lafiya da daukar karin likitoci da ma'aikatan jiyya aiki ne bukatun da aka baiwa fifiko a kasashen da suke fama da matsalolin kula da lafiya da asibitoci marasa isassun kayan aiki.
Wannan na tattare da al'adar jami'an gwamnati da ke fita zuwa kasashen waje don kula da lafiyarsu da ta iyalansu.
Rashin isassun ayyukan yi ga matasan da suka kammala jami'a ma wata matsala ce da ake fama da ita a kasar.
Afirka na da mafi yawan matasa a duniya, ind akashi 70 na jama'ar nahiyar 'yan kasa da shakaru 30 ne.
Har yanzu nahiyar na baya a duniya wajen samar da ayyuka, inda Afika ta Kudu ta samu adadin marasa aikin yi mafi yawa da ya kai kashi 32.9 a shekarar 2023. Rashin ayyukan yi a Nijeriya da kenya ya yi yawa.
Haka zalika, rikici sakamakon tsadar kayan masarufi na daduwa a fadin nahiyar Afirka.
"Rayuwa ta yi tsada sosai, musamman kayan abinci," in ji Dr Bello. "Hauhawar farashin ya tashi sama sosai (34.19) a watan Yuni, kamar yadda Babban bankin Nijeriya ya sanar. matsakaicin albashi bai isa ka ci abinci sau uku a rana ba," in ji Galadanchi.
Matakan gaggawa ba za su isa ba
Tun bayan fara zanga-zangar a Kenya, Shugaba Wiliam Ruto ya fitar da sanarwar daukar matakan gyara na wuri don kwantar da hankalin masu zanga-zangar.
Muchiri ya ce "Matasa na kallo da idanuwan basira. Suna son sauyi na tsawon lokaci kuma mai dore wa."
"Wadannan bukatu ba sabbi ba ne. Mafi yawan shugabannin sun hau mulki bayan yin alkawarin za su yi abubuwanda matasan ke so kuma sun jera su a manufofin da za su aiwatar. Amma a yanzu suna cewa babu kudin aiwatar da wadannan ayyuka na inganta rayuwa."
A yayinda alkawuran da 'yan siyasa suka yi suka gaza cikuwa, zargin rayuwar kasaita da halin ko in kula da wasu shugabannin ke nuna wa ya janyo bacin ran jama'a ga gwamnatoci.
"Matasa na bukatar sauyi bisa tsari. ba lallai su san meye akwai ba, amma ba sa son abubuwa su ci gaba da tafiya yadda suke a yanzu haka," in ji Galadanchi.