Mutane na guduwa daga kusa da wani babban kantin saye da sayarwa a yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin Sheikh hasina a babban birnin Dakha a ranar 4 ga Agusta, 2024. / Hoto: AP

Lamarin da ya faro a matsayin zanga-zangar lumana da dalibai ke yi a Bangladesh don nuna adawa ga tsarin rabon ayyukan yi a gwamnati ya rikide zuwa wani kalubale da bore ga Firamnista Sheikh hasina da jam'iyyarta ta Awami League.

Masu zanga-zangar adawa da gwamnati a fadin kasar sun ce za su yi tattaki har zuwa babban birnin Dhaka, a ranar Litinin din nan bayan rikicin da ya yi ajalin mutane da dama a karshen makon da ya gabata, kuma sojoji sun saka takunkumin hana fita, an kuma katse hanyoyin sadarwar yanar gizo.

Suna bukatar Hasina ta yi murabus, sannan suna neman adalci game da wadanda aka kashe. Tun bayan fara rikicin a watan Yuli, mutane kusan 300 sun rasa rayukansu, kamar yadda kafafan yada labarai na cikin gida suka sanar.

Ga abubuwan da ya kamata mu sani:

Ya zuwa yanzu me ya faru?

Zanga-Zangar, wadda ta ja hankalin dubu daruruwan mutane ta fara ne a watan Yuli inda dalibai suke nuna adawarsu ga tsarin rabon ayyukan gwamnati.

A ranar 16 ga Yuni lamarin ya rikide zuwa rikici a lokacin da dalibai suka yi arangama da jami'an tsaro da masu fafutuka da ke goyon bayan gwamnati, jami'an tsaro sun harba hayaki mai sa hawaye, harba harsasan roba tare da saka dokar hana fita da kuma cewa za a harbi duk wanda aka gani a waje. An katse sadarwar yanar gizo gaba daya a kasar.

Gwamnati ta bayyana cewa kusan mutane 150 sun mutu a watan da ya gabata, amma kafafan yada labarankasar sun rawaito rasa rayuka sama da 200.

A yanzu abubuwa sun fara lafawa a hankali bayan Kotun Koli ta shiga lamarin inda ta daidaita batun rabon ayyukan na gwamnati, wanda na daga bukatar masu zanga-zangar.

Amma duk da haka an ci gaba da zanga-zangar, tana jan hankalin mutane daga dukkan bangarori kuma ta samu goyon bayan 'yan adawar siyasa.

A karshen makon nan sabuwar zanga-zangar adawa da gwmanati ta barke, an samu sabuwar arangama da rikici. Ranar Lahadi ce mafi muni wajen rasa rayuka, inda aka kashe akalla mutum 95 kamar yadda kafafen yada labaran yankin suka bayyana.

Makarantu da jami'o'i da suka rufe tun watan jiya na ci gaba da kasancewa a rufe.

Me ya sa suke zanga-zanga?

Da fari, zanga-zangar adawa da tsarin rabon ayyuka ake yi inda aka nuna kin amincewa da ware kashi 30 na ayyukan gwamnati ga iyalan jaruman da suka fafata yakin kwatar 'yancin kai a Bangaladash a 1971 inda suka kalubalanci Pakistan.

Masu zanga-zangar sun ce tsarin na nuna wariya kuma ya fi fifita magoya bayan Firaminista Sheikh Hasina da jam'iyyarta ta Awami League, wadda ita ce ta jagoranci gwagwarmayar kwatar 'yancin kan.

A yayin da rikicin ya yi tsamari, a watan da ya gabata Kotun Koli ta yanke hukuncin cewar za a bai wa iyalan jaruman kashi biyar na guraben ayyukan, sannan kashi 93 kuma ga sauran jama'ar kasa da suka cancanta, sauran kashi biyu kuma ga mambobin al'umma 'yan tsiraru da nakasassu.

Gwamnati ta karbi wannan hukunci, ta dawo da sadarwar yanar gizo tana tunanin cewar lamarin zai kwanta. Amma sai zanga-zangar ta ci gaba cikin sauri.

Kungiyoyin dalibai sun ce suna da bukata kwaya ɗaya tal: shi ne Firaministan Hasina da majalisar zartarwarta su yi murabus, wadanda suka ce su ke da alhakin rikicin.

Me gwamnatin ta ce?

Hasina ta mayar da martani ga rikicin baya-bayan nan inda ta zargi masu zanga-zangar da 'zagon kasa' da kuma yanke hanyoyin sadarwar yanar gizo don kwnatar da tarzomar.

Ta ce masu zanga-zangar da ke barnatar da dukiyoyin kasa sun fita daga sahun dalibai sun zama 'yan daba kuma dole ne a magance su da karfi.

Masu zanga-zangar sun kai hari kan babban asibitin gwamnati da ke Dhaka tare da kona ababan hawa da yawa da kuma ofisohin jam'iyya mai mulki a ranar Lahadi. Bidiyon ya nuna yadda 'yan sanda suka bude wuta kan dandazon jama'a da harsasan gaske, harsasan roba da hayaki mai sa hawaye.

Jam'iyyarta ta Awami League ta ce bukatar neman murabus din Hasina na nuni ga babbar jam'iyyar adawa ta BNP da Jam'iyyar Jamaat Islam da aka haramta sun kwace filin zanga-zangar, kuma na dora musu alhakin rura wutar rikicin.

Jam'iyyun adawar sun ce suna goyon bayan zanga-zangar amma sun musanta rura wutar rikicin, kuma sun maimaita kira ga gwamnati da ta yi murabus.

Hasina ta yi alkawarin gudanar da bincike kan rasa rayuka da hukunta masu hannu a ciki. Ta kuma mika bukatar za ta tattauna da shugabannin daliban.

Me zai faru a nan gaba?

Zanga-Zangar da ba ta da niyyar zuwa karshe, ta zama wani babban rikici ga Hasina, wadda shugabanci da mamayarta na tsawon shekaru 15 a kasar ke fuskantar jarrabawar da ba a taba gani ba.

Hasina mai shekaru 76, ta samu nasarar zabe har sau hudu a jere inda 'yan adawa suka kaurace wa zaben da ya gabata. Masu suka na tambayar ko an yi zabe na gaskiya, amma gwamnatin ta ce an yi zabe na gaskiya.

TRT World