Ana sa rai dokar da aka gabatar za ta rage tasirin Kotun Koli a kan gwamnati. / Hoto: Reuters

Manyan sojoji akalla 161 da kwamandojin hedikwatar rundunar sojin saman Isra'ila ne suka ajiye aikinsu na ko-ta-kwana sakamakon shirin gwamnatin na yin garambawul ga fannin shari'ar kasar.

A wata rubutacciyar sanarwa da suka fitar a ranar Talata, jami'an sun ce shirin sake fasalin shari'a na gwamnati da ke cike da ce-ce-ku-ce zai ruguza tsarin dimokuradiyyar kasar tare da share fage ga "mulkin kama karya."

A halin da ake ciki dai, ana ci gaba da zanga-zanga da bijire wa gwamnati a yayi Firaiminista Benjamin Netanyahu ke shirin gabatar da daftarin dokar ga majalisar dokokin kasar.

Burin dokar shi ne takaita tasirin da kotun kolin kasar ke da shi a kan gwamnati.

Isra'ila ta fada cikin rudanin siyasa a watannin baya-bayan nan, sakamakon shirin gwamnati na yin garambawul a fannin shari'ar kasar, wanda 'yan adawa suka kira da matakin bangaren zartarwa na kwace madafun iko.

'Yan adawar na zargin Netanyahu, wanda ake tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa, da yin amfani da batun gyaran fuska a fannin shari'ar kasar don kare kansa daga tuhuma.

Netanyahu ya musanta tuhumar da ake yi masa, ya kuma yi watsi da duk wata alakanta batun garambawul din da shari'ar da ake yi masa.

''Ranar bore ta kasa"

A ranar Talata, dubban masu zanga-zanga sun mamaye tashoshin jiragen kasa tare da toshe hanyoyi a daidai lokacin da ake shirin kada kuri'a a majalisar dokokin kasar kan shirin gwamnati na yin gyara a fannin shari'a.

Jama'a sun taru a birnin Tel Aviv da ke gabar teku kana cibiyar kasuwancin Isra'ila, bayan amsa kiran wadanda suka shirya gangamin na "ranar bore ta kasa" gabanin shirin kada kuri'ar da 'yan majalisar za su yi.

Da dama daga cikin mutanen da suka halarci wajen na sanye da huluna don kare kansu daga tsananin zafin da ake yi, inda suke rera take tare da buga ganguna.

Gwamnatin Netanyahu, wacce ta hada Yahudawa masu tsattsauran ra'ayi, ta ce sauye-sauyen sun zama dole domin a daidaita daunin iko tsakanin zababbun jami'an da bangaren shari'a.

A wani biki da ya halarta a ranar Talata, Netanyahu ya ce gwamnati ta “himmatu wajen kiyaye dimokuradiyya, ‘yanci, da sassaucin ra’ayi, kuma duk tana kiyaye tsarin mulki mai rinjaye da ‘yancin kai kowa a kasar.

Sauye-sauyen da ake shirin yi sun janyo suka daga kasashen duniya, ciki har da babbar abokiyarta Washington.

TRT World