Tattalin arziƙin Nijeriya na fama da hauhawar farashin kayayyaki. / Hoto: Reuters

By Shamsiyya Hamza Ibrahim

A yayin da tattalin arziƙin Nijeriya ke fama da hauhawar farashi da rashin aikin yi da kuma tafiyar hawainiya a haɓakar tattalin arziƙin ƙasar, tafiyar da tattalin arzƙin ƙasar ya ƙara gamuwa da cikas bayan cire tallafin man fetur a 2023 da kuma sakin kudin ƙasar a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje da sauran na waje.

A halin yanzu da aka fito da shawarar daidaita kuɗaɗen ƙasashen waje, muhawarar da ake tafkawa a yanzu ita ce wace dama ce ta rage wa Nijeriya?

Kasimu Garba Kurfi, wanda mai sharhi ne kan tattalin arziƙi na ganin cewa babban dalilin da ke jawo rashin daidaito ga tattalin arzikin Nijeriya shi ne kashe kuɗin da gwamnatin ƙasar ke yi.

Haka kuma ƙoƙarin daidaita kasuwar canjin kuɗaɗen waje ya jawo karya darajar naira, wadda ita ce kuɗin da ta fi rashin samun tagomashi a Afirka a 2023, kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana.

Giɓi a kasafin kuɗi

Gwamnatin Nijeriya na aiki tsawon shekara biyar da kasafin kuɗi mai giɓi, wanda ƙarancin samun kuɗaɗen shiga na daga cikin abubuwan da suka jawo matsalar.

Wannan ya jawo ƙasar take cin bashi, wanda zuwa yanzu hakan ya jawo adadin kuɗin da ake bin ƙasar ya kai naira tiriliyan 87. Tattalin arzƙin Nijeriya ya dogara ne kan kuɗaɗen shigar da ake samu daga man fetur, kuma ƙasar mamba ce mai muhimmanci a ƙungiyar OPEC.

Duk da cewa gwamnatin Nijeriya na yin iyakar ƙoƙrinta domin daƙile maƙarƙashiyar da ake shirya mata ta ɓangaren tattalin arziƙi, satar ɗanyen man fetur na ci gaba da gudana, wanda hakan yake ja ƙasar ba ta iya samar da adadin da OPEC ke bukatar ta samar na man fetur.

"Haka kuma akwa ƙalubalen da ake fuskanta na gaza samar da isassun dalar Amurka domin cikin gida wanda hakan ke ƙara jawo karyewar nairar," kamar yadda Dakta isa Abdulahi ya bayyana, shugaban tsangar koyar da ilimin tattalin arziki na Jami'ar Kashere da ke Jihar Gombe a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Wani abin kuma a cewarsa shi ne rufe matatun mai. "Wannan ya bar mu ba tare da wani zabi ba illa shigo da tataccen man fetur don amfanin gida."

An buɗe matatar man Dangote a 2023 a Legas inda ake sa ran cewa za ta taimaka wa matatun man ƙasar. / Hoto: Reuters

Abubuwan da aka fi so da farko, masana sun ce hanyar da za ta bi wajen shawo kan matsalar ita ce ta dakatar da ba da tallafin kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa.

Ƙara adadin ɗanyen man fetur da ƙasar ke samarwa musamman a yankin Neja Delta domin cimma adadin da OPEC ke buƙata ita ma wata shawara ce da masana suka bayar.

Idan matatun man ƙasar suka soma aiki, hakan zai ƙara cika asusun ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar da kuma rage dogara da man fetur tattace wanda ake shiga da shi ƙasar.

Akwai kuma buƙatar gwamnati ta yi matuƙar mayar da hankali ga ɓangarorin haƙar ma'adinai da kuma ayyukan gona domin taimaka musu samar da kuɗaɗen shiga daga gwamnatin tarayya ta hanyar fitar da kayayyaki.

Daƙile cin hanci da rashawa da kuma daidaita farashi ɗaya na daga cikin abubuwan da ya kamata gwamnatin ƙasar ta mayar da hankalinta a kansu, in ji masanan.

Matsalar amfani da dala

Nijeriya ta dogara ne matuƙa da shigo da man fetur wanda ake amfani da dala domin shigar da shi ƙasar, lamarin da masana tattalin arziƙi suka daɗe suna jawo hankalin ƙasar a kai. Dalar Amurka ta kasance abin da ake amfani da ita wurin kasuwanci a Nijeriya, wanda amfani da ita wurin kasuwanci a ƙasar na ƙara karya farashin naira.

Naira na daga cikin kuɗaɗen da suka fi shan kashi a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen ƙasashen waje. / Hoto: Reuters

Mutane da yawa suna ganin wannan a matsayin abin da ke haifar da ci rashin haɓakar tattalin arziki da rashin daidaiton farashi, wanda ke zuwa tare da matsalar hauhawar farashin kayayyaki waɗanda ake ganin rashin tsare-tsare masu kyau ke haifar da su.

"Daitaita farashi na da matuƙar muhimmanci a tattalin arziƙi sakamakon hakan yana taimaka wa kayayyaki, wanda hakan ke haifar da ci gaban tattalin arziki da kuma kara karfin saye da sayarwa," kamar yadda Kurfi ya shaida wa TRT Afrika.

"Misali, yadda aka samu tashin farashin man fetur ba tsammani ya jawo ƴan Nijeriya da dama sun daina hawa motocinsu, lamarin da ya ja aka rage sayen man fetur a ƙasar.

Ɗage takunkuman da ake saka wa kasuwannin hada-hadar canjin kuɗaɗe waɗanda suka haɗa da tura dala tsakanin bankuna kan iya kawo sauƙi da rage wahalar samun kuɗaɗen wajen, haka kuma zai iya rage adadin kuɗaɗen da ake buƙata na soma kasuwanci idan aka dawo da kuɗin ruwan da ake karɓa wanda bai wuce kaso 9 cikin 100 ba.

Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin samar da kuɗaɗen waje a cikin Nijeriya ta hanyar fito da tsare-tsare waɗanda suka haɗa da jawo hankalin sabbin masu zuba jari da ƙara yawan fetur ɗin da ake samarwa da kuma yin garambawul ga kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje.

A faɗin duniya, farashin kayayyaki na tasiri matuƙa ga ƙasashe ta ɓangaren kasuwanci, kuma Nijeriya ma hakan take.

TRT Afrika