Za a faɗaɗa yarjejeniyar kasuwanci mara shinge tsakanin Turkiyya da Birtaniya zuwa ɓangarori da dama, da manufar haɓaka jarin da ke tsakaninsu zuwa dala biliyan 30, a yayin da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya David Lammy suka gana a makon nan a Landan don tattauna yadda za a sabunta yarjejeniyar.
Tun shekarar 2021 Turkiyya da Birtaniya suka ƙulla yarjejeniyar, duk da cewar wani ɓangare na dokar da ya shafi Brexit, ya sanya dole ɓangarorin biyu su sake nazari kan alaƙarsu ta kasuwanci, tare da zurfafa dangantakar da ke tsakaninsu.
Yarjejeniyar da aka sabunta da faɗaɗa ta, za ta ƙunshi zuba jari da ƙarin sauƙaƙawa ga ɓangaren noma, wanda ake sa ran zai samar da babban jigon dokoki ga 'yan kasuwar ƙasashen biyu.
A 2023 Turkiyya ta fitar da kayayyaki na dala biliyan 12.5 zuwa Birtaniya, inda ta shigo da na dala biliyan 6.5 daga ƙasar, inda take da rarar dala biliyan 5.9, kamar yadda alƙaluman da Anadolu suka tattara, inda jarin kasuwancin da ke tsakanin ƙasashen biyu ya kai na dala biliyan 19.
Turkiyya ta fitar da kayayyaki na dala biliyan 11.2 zuwa Birtaniya a watanni tara na farkon wannan shekarar, inda ta kuma shigo da na dala biliyan 5.1, wanda ya kai jarin kasuwancin zuwa dala biliyan 16.3, da kuma rarar kuɗin kasuwanci na dala biliyan 6.1.
Ninka jarin kasuwanci, haɓaka zuwa sabbin ɓangarori
Yarjejeniyar kasuwncin mara shinge da aka sabunta da fadada wa na da manufar habaka jarin kasuwanci tsakanin kasashen zuwa dala biliyan 30, karin kusan kashi 60 kuma ana yabon hakan saboda kasancewa wata gaba mai muhimmanci ga tattalin arzikin Turkiyya da Birtaniya, kamar yadda sanarwar Ƙungiyar 'Yan Kasuwar Turkiyya ta bayyana.
Yarjejeniyar yanzu ta mayar da hankali ga kayayyakin masana'antu, amma sabuwar kuma ta hado da ayyuka, zuba jari, da tallafin noma tare da goyon bayan juna don habaka ayyukan kudade, injiniyanci, sufuri, fasahar kere-kere da ayyukan kwararru.
Yarjejeniyar da aka yi wa kwaskwarima ta hada da dokoki don karfafa kasuwaci ta yanar gizo, samun bayanai, da bayar da kariya ga hakkon mallaka na kayan fasaha.
Turkiyya, da ke da mutane miliyan 85, ta zama babbar damar tattalin arziki, ayyuka a bangaren kayan more rayuwa da zuba jari wajen rage iskar carbon na samar da damarmakin hadin kai da Birtaniya sosai.
Yarjejeniyar na da manufar rage tsaiko da shingen kasuwanci tare da samar da fitar da kayayyaki da kasuwancin intanet, kuma yana da muhimmanci yadda Turkiyya ta zama gadar tafiya zuwa Gabashi daga Yammacin duniya.
Kazalika, ga amfanin tattalin arziki, ana sa ran sabuwar yarjejeniyar za ta haɓaka alaƙar ƙasashen biyu a bangarorin tsaro, musayar al'adu, ilimi da yawon buɗe ido.
A yayin da aka fara tattaunawa a watan Satumba, sauye-sauyen dokoki da samun damar shiga kasuwanni a bangarori masu muhimmanci sosai na kawo ƙalubale, duk da ana ci gaba da ƙoƙarin sabunta wa da faɗaɗa yarjejeniyar, ana nuni da ƙasashen biyu na da aniyar haɗa-kai iye da yadda ake zato.