Bankunan Turkiyya na da yawan ma’aikata 207,153. Photo: AA

Bankunan Turkiyya sun sanar da samun ribar tsabar kudi har dala biliyan 9.28 daga watan Janairu zuwa Mayun 2023, in ji wata sanarwa da hukumar sanya idanu kan bankunan kasar ta fitar.

Ya zuwa karshen watan Mayun bana, jimillar kadarorin da bankunan ke da su sun kai Lira tiriliyan 16.84 (dala biliyan 843.5), wanda ya karu daga Lira tiriliyan 13 (dala biliyan 692.09) a watan Mayun 2012, kamar yadda alkaluma a Hukumar Kula da Bankunan Turkiyya suka bayyana.

Bashin da ake bayarwa wanda shi ne kadara mafi yawa da bankunan ke da shi ya kai Lira tiriliyan 9.2 (dala biliyan 447.5) a watan Mayu.

A bangaren kudaden da ake bin bankunan kuma, da kudaden da masu ajiya suka ajiye, akwai Lira tiriliyan 10.35 (dala biliyan 501.7).

Ya zuwa karshen watan Mayun 2023, bangaren sha’anin bankuna a Turkiyya na da yawan ma’aikata 207,153 da suke aiki a rassa 11,041 a ciki da wajen kasar.

Haka zalika bankunan na da injinan cira da ajiye kudi na ATM guda 48,810.

AA