Kamfanin kera jiragen yaki marasa matuka na Turkiyya ya kulla yarjejeniya da Saudiyya

Kamfanin kera jiragen yaki marasa matuka na Turkiyya ya kulla yarjejeniya da Saudiyya

Kamfanin Baykar da ke kera jiragen yaki marasa matuka a Turkiyya ya saka hannu kan babbar yarjejeniya ta tarihi da Saudiyya.
Turkiyya na ci gaba da habaka masana'antun kayan tsaro. Hoto: AA

Haluk Bayraktar, Janaral Manaja na kamfanin ya fitar da sanarwa ta shafinsa na Twitter cewa Baykar da Ma’aikatar Tsaron Saudiyya sun sanya hannu kan cinikin jirgin yaki mara matuki na Akinci.

Jirgin yaki mara matuki mai suna Akinci na iya daukar abubuwa masu nauyi, kuma sannan na da na’urorin Kirkirarriyar Basira guda biyu.

Jirgin na iya gudanar da ayyukan da ake yi da manyan jiragen yaki, yana kuma da karfin amfani da tallafi na lantarki a sama, tsarin amfani da tauraron dan adam guda biyu, na’urar hangen nesa, kauce wa karo da karfin gani a sama.

Ana iya amfani da jirgin na Akinci wajen kai hari a sama, ko a kai hari kasa daga sama.

A wani bangare na ziyarar da Shugaba Erdogan ya kai Saudiyya, kasashen biyu sun sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama a ranar Litinin da suka hada da na zuba jari, tsaro, makamashi da sadarwa.

Tun bayan fara aikin UAV da R&D a 2003, Baykar ya samu kaso 75 na kudaden shigarsa daga fitar da kayayyaki kasashen waje.

Kungiyar Masu Fitar da Kayayyaki Kasashen Waje daga Turkiyya ta bayyana cewa a 2021, su ne ke kan gaba wajen fitar da kayan tsaro zuwa kasashen waje a duniya.

Baykar da makin fitar da kayayyakinsa ya kai 99.3 a 2022, ya samu dala biliyan $1.18.

A watan Disambar bara, Albaniya ma ta sayi jiragen yaki na Bayraktar TB2 guda uku, jiragen da suka yi shuhura bayan kokarinsu da aka gani a yakin Rasha da Yukren.

TRT World