Mataimakin shugaban kasar ya kuma ce kasafin kudin Turkiyya na fannin tsaro ya kai a kalla dala biliyan 5.5 a 2022, inda a yanzu ya kai dala biliyan 90. / Photo: AA

Turkiyya na sa ran kasuwancinta na fitar da makamai kasashen waje ya haura dala biliyan 10 nan ba da dadewa ba, a cewar mataimakin shugaban kasar.

Da yake magana a wajen bikin bude baje-kolin kayayyakin tsaro na (IDEF) na 16 a Istanbul, Cevdet Yilmaz ya ce Turkiyya ta fitar da kayayyakin tsaro na jumullar dala biliyan 2.4 a rabin shekarar 2023, kuma ana sa ran yawan wadanda za a fitar su kai dala biliyan shida nan da karshen shekara.

A wajen baje-kolin na IDEF, wanda daya ne daga cikin manyan bukukuwan kayan tsaro na duniya da za a shafe kwanaki har zuwa Juma’a ana yi, za a baje-kolin kayayyaki da suka hada da makamai da makamai masu linzami da tankokin yaki da sauran abubuwa.

Yilmaz ya ce Turkiyya tana wani muhimmin yanki ne da rikice-rikice ke kamari, yana mai cewa “abubuwan da suka faru a baya sun nuna yadda Turkiyya ta dogara da kanta wajen samar da kayayyakin tsaro.”

Fannin tsaro na Turkiyya ya kasance wani gagarumi da ke samar da kayayyakinsa na yaki a cikin gida, inda yake da abokan kwangila a fadin duniya kamar cibiyoyin kanana da matsakaitan kasuwanci da cibiyoyin bincike da fasaha da masana’antu da sauran su, kamar yadda ya kara da cewa.

Mataimakin shugaban kasar ya kuma ce kasafin kudin Turkiyya na fannin tsaro ya kai a kalla dala biliyan 5.5 a 2022, inda a yanzu ya kai dala biliyan 90.

Mista Yilmaz ya bayyana cewa fannin tsaron yana da kamfanoni 3,000 da ma’aikata fiye da 80,000, “sannan ayyukan da muke yi sun karu da kusan 850.”

Ya kara da cewa Turkiyya na daga cikin manyan kasashe uku da suke da fasahar kera jirage marasa matuka sannan tana cikin manyan kasashe 10 da ke kera jiragen ruwa na yaki.

“A shirye muke mu yada iliminmu da kwarewarmu da fasahar da muka samu a fannin tsaro ga kawayenmu,” in ji shi.

“Mu ba kasa ce mai nuna kyashi da rowa kamar wasu ba.”

AA