Kamfanin jirgin sama na Turkiyya ya yi zarra a makon da ya gabata inda aka samu sauka da tashin jirage 1,594. Hoto/AA

Shekarar 2023 ce shekarar da kamfanin jirgin sama na Turkish Airlines ke cika shekara 90 da kafuwa, wanda shi ne “jirgin da ke jigila zuwa kasashe fiye da duk wani kamfanin jirgi na duniya.”

A ranar 20 ga watan Mayun 1933, kamfanin jirgin wanda ake kira State Airlines Administration ya soma jigila inda matukin jirgin sama na Turkiyya na farko Fesa Evrensev ya soma jagorantar kaddamar da jigilar inda kamfanin yake da ma’aikata 30 da kuma jirage biyar masu kujeru 28.

Kamfanin jirgin saman ya soma jigilarsa ta farko a tsakanin Ankara zuwa Istanbul zuwa Athens a 1947.

A halin yanzu jirgin yana zuwa wurare 344 da ke kasashe 129 da kuma nahiyoyi biyar na duniya. Kamfanin yana da jimillar ma’aikata 82,000 da kuma jirage 418 wadanda ke zagaye duniya dauke da tutar Turkiyya.

Kamfanin ya fadada matuka a cikin gomman shekaru. Kamar yadda kuri’ar jin ra’ayi ta nuna wanda wani shahararren kamfanin tuntuba ya yi, kamfanin jirgin shi ne wani abu mallakar Turkiyya wanda aka fi ji ko tinkaho da shi a shekara shida a jere.

A yau, yin zarra ya kasance wani abin yau da kullum ga jirgin saman Turkiyya.

A watan Mayun 2023, kamfanin ya kafa tarihi inda alkaluma suka nuna ya yi jigilir fasinjoji miliyan 7.4.

Tauraruwar da ke haskawa

Ganin cewa kamfanin shi ne ya fi sabbin jirage kuma na zamani a Turai, jiragen kamfanin suna bunkasa sakamakon fasahar zamani da rashin shan mai da tafiya daidai da muhalli da kuma yadda suke da walwala a cikinsu.

Kamfann jirgin saman ya samu lambar yabo ta gwarzon jirgin sama na Turai a 2022 sakamakon yadda yake zagaye ko ina da kuma irin sabbin jiragensa da yanayin kujerunsa da kuma abincin cikinsa.

Kamfanin ya dada bunkasa sunansa bayan da wasu shahararru a duniya suka yi masa talla da suka hada da Kobe Bryant da Lionel Messi da Morgan Freeman da dai sauransu.

Duk da cikas din da annobar korona ta kawo kan sufurin jiragen sama a 2021, amma duk da haka sai da jirgin saman ya samu ribar dala miliyan 959, wanda hakan ke nufin ya samu ci gaba kan faduwar da ya yi ta dala miliyan 836 a 2020 sakamakon korona.

TRT World