| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
'Yansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da Faransa a taron Afirka-Faransa a Kenya
Wasu daga cikin masu zanga-zangar na ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce, yayin da wasu ke daga jajayen tutoci masu ɗauke da alamomin gurguzu da hotunan wasu mutane.
'Yansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da Faransa a taron Afirka-Faransa a Kenya
'Yansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da Faransa a taron Afirka-Faransa a Kenya / Anadolu Agency

‘Yansandan Kenya sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye a ranar Talata domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar adawa da Faransa da suka yi ƙoƙarin isa cibiyar taruka ta Kenyatta International Convention Centre (KICC) a Nairobi, inda ake gudanar da taron Africa Forward Summit.

Masu zanga-zangar, ciki har da wasu ‘yan ƙasashen waje, sun taru ne a titin Uhuru Highway ɗauke da jajayen tutoci da allunan nuna adawa da mulkin mallaka, kafin jami’an ‘yansanda masu yaki da tarzoma su tare su tare da hana su isa wajen taron da ke cike da tsauraran matakan tsaro.

Bidiyoyi daga wajen sun nuna yadda ‘yansanda ke korar masu zanga-zangar ta wasu sassan tsakiyar birnin yayin da hayaki mai sa hawaye ya mamaye sararin samaniya. An kuma ga jami’an tsaro suna tura wasu masu zanga-zangar cikin motocin ‘yansanda yayin samamen.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar na ɗauke da alluna masu rubuce-rubuce, yayin da wasu ke daga jajayen tutoci masu ɗauke da alamomin gurguzu da hotunan wasu mutane.

Haka kuma ana jin masu zanga-zangar suna rera taken adawa yayin da ‘yansanda suka ƙara tsaurara shingen tsaro a hanyoyin da ke kaiwa wajen taron na KICC.

Zanga-zangar ta zo ne a daidai lokacin da shugabanni fiye da 30 daga Afirka da Turai suka hallara a Nairobi domin taron Africa Forward Summit, wanda Kenya da Faransa suka shirya tare, inda ake tattauna harkokin kasuwanci, zuba jari, gine-ginen more rayuwa da haɗin gwiwar yaƙi da sauyin yanayi.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Sakatare Janar na Majalisar DInkin Duniya Antonio Guterres na daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron tare da shugabannin ƙasashen Afirka, ‘yankasuwa, jami’an diflomasiyya da abokan hulɗar ci gaba.

An ci gaba da ganin jami’an tsaro a ko ina cikin tsakiyar Nairobi tsawon ranar, inda ‘yansanda suka taƙaita zirga-zirga a kusa da manyan gine-ginen gwamnati, otal-otal da hanyoyin da ke haɗe da wajen taron.

Rumbun Labarai
‘Yanta’adda sun kashe aƙalla mutum 70 a Mali a cikin kwanaki biyu
Nijar ta dakatar da kafafen yada labarai na Faransa guda 10
Kenya ta zaɓi amfani da 'fetur mai datti' saboda yaƙin Iran da ya kawo cikas ga jigilar mai
Masu haƙar zinari ba bisa ƙa'ida ba biyar sun maƙale a ƙarƙashin ƙasa bayan rami ya rufta a Zambia
Chadi ta ayyana zaman makoki na ƙasa bayan Boko Haram ta kashe sojojinta
Burkina Faso ta sake haramta wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu, inda adadin ya kai 205
Rundunar sojin Chadi ta ce an kashe jami'anta 23 a wani harin Boko Haram
Afirka ta Kudu na bincike kan satar makaman soji
Harin jirgi mara matuƙi a Sudan ya kashe ’yan’uwa tara na wani kwamandan da ke mara wa soji baya
Mali tana binciken sojoji da ’yan siyasa da ke da alaƙa da hare-haren ta’addanci
’Yan tawaye sun ƙwace muhimmin sansani daga sojojin Mali da sojojin haya na Rasha - rahotanni
Amurka ta amince a sayar wa Isra’ila, UAE, Kuwait, Qatar makaman da suka haura na dala biliyan 8.6
Masana kimiyya a Kenya suna bincike don habaka yi wa kwayoyin halittar shanu kwaskwarima
Harin ta'addanci a Burkina Faso ya yi ajalin mutane 11
Mali za ta yi faretin soji na ban girma a jana'izar ministan tsaron da aka kashe a harin ta'addanci
Chadi ta kama tare da korar 'yan Nijeriya da suka guje wa 'yanta'adda
Ghana na neman ‘yankasuwa masu zuba jari a sabon kamfanin jiragen saman Ƙasar
Shugaban Mali ya ce komai ya 'koma daidai' a jawabinsa na farko tun bayan hare-haren 'yanta'adda
Ghana ta ƙi karɓar tallafin lafiya na Amurka na dala miliyan 109 bisa damuwa kan tsaron bayanai
An kashe mutum 10 tare da kama 11 a harin 'yanbindiga kan ayarin sojin Ghana