Sabbin hare-haren da ‘yan ta’adda suka kai a tsakiyar ƙasar Mali sun kashe mutane da dama, kamar yadda majiyoyin yankin da jami’an tsaro suka bayyana a ranar Asabar.
Kungiyar JNIM mai alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin hare-haren da aka kai ranar a Jumma’a, bayan da tuni ta kashe akalla mutane 30 a hare-haren da aka kai kan ƙauyuka a ranar Laraba.
Wani jami’in yankin ya ce sabbin hare-haren da kungiyoyin masu ɗauke da makamai suka kai sun sa adadin waɗanda suka mutu ya haura 70 a cikin kwanakin baya-bayan nan.
Wani jami’in yankin daban ya bayyana cewa adadin mamatan ya kai 80.
“Zukatanmu na cikin ƙunci,” in ji wani shugaban matasan yankin, yana zargin sansanonin sojoji da ke kusa da rashin kawo taimako duk da kiraye-kirayen neman agaji da aka yi sau da dama.
Wata majiya ta tsaro ta bayyana halin da ake ciki a yankin a matsayin “abin damuwa.” Majiyar ta ƙara da cewa, “Kungiyar JNIM na kai hare-hare kan ƙauyukan da suka ƙi sanya hannu kan yarjejeniyoyin cikin gida.”
Sabbin hare-haren na zuwa ne bayan da ƙungiyar JNIM da kuma ta ‘yan awaren Azbinawa suka kai wani hari da ba a taɓa ganin irinsa ba kan gwamnatin mulkin sojin Mali a watan da ya gabata.
Tun daga lokacin, matsalar tsaro a Mali ta tsananta, inda yanzu ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke iko da yankuna da dama a arewacin ƙasar.












