| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Harin ta'addanci a Burkina Faso ya yi ajalin mutane 11
Wata ƙungiya mai alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kai harin, tana cewa ta ƙwace iko da wani sansani na sojojin Burkina Faso.
Harin ta'addanci a Burkina Faso ya yi ajalin mutane 11
Harin ta'addanci a arewacin Burkina Faso ya kashe akalla mutane 11 a ranar 29 ga watan Afrilu, 2026. / Getty Images

Aƙalla fararen hula 11, mafi yawansu 'yan sa-kai da ke taimaka wa sojoji, ‘yan ta’adda suka kashe a arewacin Burkina Faso, kamar yadda mutanen yankin da jami'an tsaro suka bayyana wa kamfanin dillanci labarai na AFP a ranar Alhamis.

Wata ƙungiyar 'yan ta'adda mai alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin harin da aka kai ranar Laraba, kuma ta ce ta "karɓe iko da wata tashar soji ta rundunar sojin Burkina Faso", ba tare da ta bayar da cikakken bayani ba.

"Jiya da misalin ƙarfe 3:00 na yamma (1500 GMT) 'yan ta'adda ɗauke da manyan makamai a kan babura sun kai hari a garin Bagare," in ji wani mazaunin yankin a lardin arewa na Passore.

"An shafe fiye da awa ɗaya ana musayar wuta, sannan 'yan ta'addan sun ƙone shaguna da yawa, da motoci da babura," in ji shi.

‘An yi nasarar daƙile abokan gaba’

"Ɓarnar da aka yi tana da yawa, amma musamman muna bakin ciki da asarar rayukan jama’a, wadanda masu kai hari suka nufa kai-tsaye," in ji wani mazaunin garin, yana nufin 'Volunteers for the Defence of the Homeland' (VDP) ko 'Yan Sa-Kai na Kariyar Kasa (VDP).

Wani jami'in tsaro na yankin ya tabbatar da harin ga AFP, ya ce: "Tabbas ‘yan ta’addan sun nufi shingen VDP, amma martanin da sojoji suka mayar ya yi nasarar tarwatsa abokan gaba."

Wani mazaunin yankin ya ce mutane daga kauyuka makwabta sun nemi mafaka a Bagare kafin a kai mata hari a ranar Larabar.

Burkina Faso ta ƙarfafa matakan tsaro

A ranar Talata, gwamnati ta ƙaddamar da wani aikin soja da nufin ƙarfafa tsaro a fadin Burkina Faso

Har ila yau, ta tsaurara tsaro a babban birnin ƙasar, Ouagadougou.

Matakan sun biyo bayan tsararrun hare-hare da ‘yan ta’adda da Abzinawa masu neman ɓallewa suka kai a makwabciyar ƙasar, Mali.