| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Ministan yaɗa labaran Nijeriya ya musanta zargin mayar da ƙasar tsarin jam’iyya ɗaya
Da yake magana a wata hira ta musamman da TRT Afrika Hausa, Ministan Yaɗa Labaran Ƙasar, Mohammed Idris ya ƙaryata zarge-zargen da ‘yan adawa ke yi cewa jam’iyyar mai mulki ta APC na ƙoƙarin mamaye fagen siyasa.
Ministan yaɗa labaran Nijeriya ya musanta zargin mayar da ƙasar tsarin jam’iyya ɗaya
Ministan yaɗa labaran Nijeriya ya musanta zargin mayar da ƙasar tsarin jam’iyya ɗaya / Reuters

Wani babban minista a gwamnatin tarayya ya musanta zargin cewa Nijeriya na dab da komawa tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da bin ƙa’idojin dimokuraɗiyya.

Da yake magana a wata hira ta musamman da TRT Afrika Hausa, Ministan Yaɗa Labaran Ƙasar, Mohammed Idris ya ƙaryata zarge-zargen da ‘yan adawa ke yi cewa jam’iyyar mai mulki ta APC na ƙoƙarin mamaye fagen siyasa.

Ya bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe, yana mai cewa Shugaba Tinubu mutum ne da ya shafe rayuwarsa gaba ɗaya cikin harkar dimokuraɗiyya, kuma ba shi da niyyar tauye tsarin jam’iyyu da dama.

A cewarsa, yawan sauya sheƙa da gwamnonin jihohi da ‘yanmajalisa ke yi zuwa APC bai kamata a ɗauke shi a matsayin wata manufa ta ƙarfafa jam’iyya ɗaya ba.

Ya ce sauyin jam’iyya abu ne na al’ada a tsarin dimokuraɗiyya, inda ‘yansiyasa ke komawa inda suke ganin manufofi da akidu sun fi dacewa da su.

“An taɓa yin lokacin da Jam’iyyar PDP ke da kusan jihohi 31, amma ba a ce Nijeriya ta koma jam’iyya ɗaya ba,” in ji shi, yana ƙara da cewa abin da ke faruwa yanzu yana nuna amincewa da manufofin gwamnatin Tinubu ne, ba wai tilastawa ba.

Ministan ya kuma musanta zargin cewa gwamnati na da hannu a rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyun adawa, musamman jam’iyyar ADC, wadda ke fuskantar wasu sabani a ciki. Ya ce waɗannan matsaloli al’amura ne na cikin gida da ya kamata jam’iyyar ta warware da kanta.

Dangane da batun haɗakar jam’iyyun adawa kafin zaɓen 2027, ministan ya ce APC ba ta jin tsoro, yana mai cewa haɗakar jam’iyyu ba sabon abu ba ne a siyasar Nijeriya, inda ya yi nuni da yadda irin wannan haɗaka ta kawo sauyin gwamnati a shekarar 2015.

“Su fitar da ɗantakarar da suke ganin zai iya fafatawa da mu, mu ma za mu fitar da namu, sai ‘yan Nijeriya su yanke hukunci,” in ji shi.

Game da zarge-zargen da ake yi kan shugabancin Hukumar Zaɓe mai Zaman Kanta (INEC), ministan ya amince cewa irin waɗannan korafe-korafe ba sabon abu ba ne. Sai dai ya ce akwai hanyoyi na doka da za a bi domin gabatar da irin waɗannan koke-koke, ciki har da kai su gaban Majalisar Tarayya.

Da yake duban gaba zuwa zaɓen 2027, ministan ya bayyana cewa gyare-gyaren tattalin arziki da gwamnati ke yi za su zama ginshiƙin yakin neman zaɓe.

Ya ce an samu gagarumin ci gaba wajen farfaɗo da tattalin arziki, inganta kuɗaɗen jihohi, da kuma dawo da amincewar masu zuba jari daga ƙasashen waje.

Ya ƙara da cewa kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki, jihohi da dama na fama da rashin iya biyan albashi, yayin da kaso mai yawa na kuɗaɗen shiga na ƙasa ke tafiya wajen biyan basussuka.

Ya ce yanzu al’amura sun inganta, inda aka samu ƙarin ƙarfin tattalin arziki da kuma dawowar masu zuba jari na duniya.

A ƙarshe, ministan ya bayyana cewa gwamnati za ta dogara da ayyukanta wajen neman sake zaɓe a 2027, yana mai fatan cewa ‘yan Nijeriya za su sake ba ta dama bisa la’akari da sauye-sauyen da ake ci gaba da aiwatarwa.

MAJIYA:TRT Afrika Hausa