Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya isa ƙasar Rasha a yayin da ƙoƙarin samar da zaman lafiya tsakanin Iran da Amurka ke cikin rashin tabbas, bayan jerin tattaunawar diflomasiyya a yankin da kuma rugujewar tattaunawar da aka yi a Islamabad.
“Ya isa ne da sanyin safiyar ranar Litinin da nufin ganawa da kuma tattaunawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin,” kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Iran, IRNA, ya wallafa a shafinsa na Telegram.
Kamfanin dillancin labarai na TASS da ke Moscow ya tabbatar da cewa Putin na shirin ganawa da Araghchi, inda ya ruwaito kakakin Rasha, Dmitry Peskov.
Araghchi ya ziyarci Oman ne tsakanin tafiye-tafiyensa zuwa Islamabad, babban birnin Pakistan.
A ranar Asabar, ministan harkokin wajen na Iran ya gana da babban hafsan sojin Pakistan, Asim Munir, Firayim Minista Shehbaz Sharif, da Ministan Harkokin Waje Ishaq Dar kafin ya wuce Oman sannan ya sake komawa Islamabad.

Daga baya ya nufi Rasha domin tattaunawa da manyan jami’ai, in ji ma’aikatarsa. Kasar Rasha ta tabbatar da ziyarar.
A matsayin manuniyar cewa ana ci gaba da ƙoƙari, kamfanin dillancin labarai na Fars ya ce Iran ta aika wa Amurkawa “saƙonni a rubuce” ta hannun Pakistan mai shiga tsakani, inda ta fayyace iyakokinta (red lines), ciki har da batun nukiliya da Mashigar Hormuz.
Sai dai Fars ya ce saƙonnin ba sa cikin tsarin tattaunawa ta hukuma.
Har yanzu ana bin yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran, amma tasirinsa ga tattalin arziki na ci gaba da shafar duniya baki ɗaya.
Iran ta toshe mashigar, lamarin da ya datse zirga-zirgar mai, iskar gas, da takin zamani, wanda hakan ya sa farashi ya tashi sama, tare da tada fargabar haifar da matsalar rashin abinci a ƙasashe masu tasowa.
An sanya rai kan tattaunawa yayin ziyarar da aka tsara Witkoff da Kushner za su kai, amma Trump ya soke tafiyar, inda ya bayyana ta a matsayin “zama ana surutu kan abin da babu shi.”
A ranar Lahadi, Trump ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na Amurka cewa idan Iran na son tattaunawa, “za su iya zuwa gare mu, ko kuma su kira mu, kun sani, akwai waya, muna da layuka masu tsaro sosai.”
Lokacin da aka tambaye shi ko soke tafiyar na nufin za a koma faɗa, Trump ya ce: “A’a, ba haka ba ne.”
Shakkun game da diflomasiyya
A tsakiyar wannan jerin tarurruka, Araghchi ya ce “har yanzu bai gani ba ko Amurka da gaske take wajen son diflomasiyya.”
Matsin lamba na kawo ƙarshen yaƙin ya ƙaru yayin da Mashigar Hormuz ke ci gaba da kasancewa a rufe. Rundunar dakarun juyin juya halin Iran (IRGC) ta ce ba ta da niyyar janye takunkumin toshe hanyar, wanda ya girgiza kasuwannin makamashi.
“Iko da Mashigar Hormuz da kuma ci gaba da nuna barazanar hakan ga Amurka da masu goyon bayan fadar White House a yankin, shi ne dabarar ƙarshe ta Iran ta Musulunci,” in ji dakarun a shafinsu na Telegram.
Ita ma Amurka ta kafa takunkumin toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran a matsayin martani.
A cikin wata sanarwa da kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito, sojojin Iran sun yi gargaɗin cewa ci gaba da “toshe, fashi da makami ne a teku,” da Amurka ke yi zai jawo martani.

















