Shugaban Mali ya jaddada ranar Talata cewa lamura sun “koma daidai” a ƙasarsa yayin da ya yi jawabinsa na farko a bainar jama’a tun bayan hare-haren ‘yanta’adda da aka kai a ƙarshen mako.
‘Yanta’adda da ‘yan a-ware ƙarƙashin jagorancin Abzinawa suna da ƙarfi a arewacin ƙasar ta yankin Sahel, kwanaki uku bayan sun kai hare-hare, wanda shugaba Assimi Goita ya amince cewa wani lamari ne mai "matsanancin hatsari".
Goita bai bayyana bainar jama’a ko kuma fitar da wata sanarwa ba cikin kwanaki uku, amma ranar Talata da yamma ya yi jawabi ga ƙsar ta gidan talabijin ɗin ƙasar.
"A yanzu haka da ne muka magana, an saƙe ƙarfafa tsare-tsaren tsaro. Lamarin na ƙarƙashin iko kuma ayyuka na share wurare da ƙoƙarin bincike da tattara bayanan sirri da kuma matakan tsaro suna ci gaba," in ji shi.

Ya yi kira ga mutanen su "guji rarrabuwar kai da kuma raba ƙasa", yana mai cewa ƙasar ta Yammacin Afirka na buƙatar "bayani, ba tsoro " ba.
Daga farko a ranar Talata, ofishinsa ya fitar da wasu hotunansa inda yake ganawa da sojojin da suka ji rauni da fararen hula, da kuma jakadan muhimmin ƙawa Rasha.
Hotunan su ne karon farko da aka ga hoton Goita tun bayan harin da aka kai cikin sanyin safiyar ranar Asabar, ciki har da a wurare a kewayen Bamako.
A ƙalla mutum 23 ne aka kashe cikin kwanaki biyu na yaƙi babu ƙaƙƙauntawa, kamar yadda wata majiya ta asibiti ta shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP ranar Talata . Ministan tsaro Sadio Camara yana cikin waɗanda aka kashe .
An yi jerin arangamar ne tsakanin soji da ‘yan-a-ware ƙaƙarashin jagorancin Abinzinawa da kuma abokananensu daga ƙungiyar ta’addanci ta JNIM .
A ganawarsa da Goita, jakadan Rasha Igor Gromyko ya "sake jaddada jajircewar ƙasarsa ta kasancewa da Mali a yaƙin da take da ta’addanci", in ji ofishin shugaban na Mali.
Hare-haren na ƙarshen mako sun tunatar wa mutane rikicin Mali na shekarar 2012, lokacin da ‘yan-a-ware da Abizinawa ke jagoranta suka haɗa ƙarfi da ‘yanta’adda wajen ƙwace muhimman wurare a arewacin ƙasar.












