Shugaban Amurka Donald Trump da sauran mahalarta wani gagarumin taron cin abinci na manema labarai a Washington sun fice cikin gaggawa a daren ranar Asabar bayan an harba bindiga.
Yayin da cikakkun bayanai ke ci gaba da fitowa kuma ana tsaka da gudanar da bincike, ga abubuwan da muka sani zuwa yanzu game da harbe-harben:
Me ya faru a babban zauren?
An ji ƙarar harbe-harbe bayan jawabin maraba a wurin taron cin abinci na shekara-shekara na Ƙungiyar Masu ba da Rahoton fadar White House (WHCA) da ake gudanarwa a otel ɗin Washington Hilton, kamar yadda manema labarai na AFP da sauran shaidu suka bayyana.
Tawagar jami’an tsaro na musamman ɗauke da bindigogi sun mamaye dandamalin da Trump yake zaune tare da mai ɗakinsa Melania, da Mataimakin Shugaban Ƙasa JD Vance da sauran mambobin majalisar ministoci, waɗanda aka fitar da su cikin gaggawa.
Daruruwan baƙi da suka ci ado a cikin zauren sun fake a ƙarƙashin tebura, daga baya kuma suka fito zuwa harabar otel ɗin sannan suka fita waje yayin da aka dage taron. Hukumomi sun ce babu wani babban jami’i ko baƙo da ya ji rauni.
Yaya harbe-harben suka faru?
Wani “mahari guda ɗaya” ya yi yunƙurin kutsa kai ta shingen bincike a harabar otel ɗin, daidai wajen babban zauren da ake taron da misalin ƙarfe 8:36 na dare (0036 GMT), a cewar hukumomi.
Trump ya wallafa bidiyo a shafinsa na Truth Social wanda ke nuna wanda ake zargin yana rugawa zuwa shingen binciken kafin jami’ai su yi masa rubdugu.
“Yana ɗauke da bindigar mafarauta, da bindigar hannu, da kuma wuƙaƙe da dama,” in ji babban jami’in ’yansandan yankin (MPD), Jeffery Carroll, yayin da yake magana da manema labarai.
Jami’an tsaro sun yi musayar wuta da wanda ake zargin kuma suka “dakile wannan mutumin.”
Wani jami’in hukumar jami’in tsaro na sirri (Secret Service) sanye da kaki ya samu “rauni a jikin rigarsa ta sulke” kuma aka kai shi asibiti, amma yana samun sauƙi, in ji Carroll. Maharin bai samu raunin harbi ba, amma an kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.
Yana tsare kuma za a gurfanar da shi ranar Litinin a kotun tarayya.
Mutumin da ake tsare da shi, wanda jami’ai suka yi amannar ya isa wurin a matsayin baƙo a otel ɗin, ana tunanin shi kaɗai ne ya aikata hakan.
Babbar Lauyar Amurka Jeanine Pirro ta ce yana fuskantar tuhume-tuhume guda biyu: amfani da makami yayin aikata laifi, da kuma kai wa jami’in gwamnati hari ta amfani da makami mai haɗari.
Wane ne mutumin da ake zargin?
Trump ya wallafa hotunan wanda ake zargin, ba shi da riga kuma an sanya masa ankwa a hannu, sannan ya yi rub-da-ciki a kan kafet a harabar Hilton. Hukumomi ba su riga sun tabbatar da ko shi wane ne ba a hukumance, amma kafafen yaɗa labarai na Amurka da dama sun bayar da rahoton cewa wanda ake zargin wani mutumi ne ɗan shekara 31 mai suna Cole Tomas Allen daga Torrance, a Jihar California.
An ga jami’an FBI a wajen wani gida mai hawa biyu a Torrance a daren ranar Asabar.
“Ina ganin ya yi aikin ne shi kaɗai,” in ji Trump, inda ya ƙara da cewa dalilin maharin na kai harin bai fito fili ba tukunna amma ya yi imanin cewa maharin “ba shi da lafiyar ƙwaƙwalwa.”
Wani shafi na LinkedIn mai sunan “Cole Allen” ya nuna hoton mutumin da ya yi daidai da hoton wanda ake zargin da Trump ya wallafa.
Shafin ya nuna cewa Allen injiniya ne, masanin kimiyyar kwamfuta, mai ƙirƙirar wasannin bidiyo, kuma malami. Wata jami’ar kwalejin Caltech ta shaida wa jaridar New York Times cewa wani mutumi mai suna Cole Allen ya kammala karatu a makarantar a shekarar 2017.
Shin ko akwai gazawar jami’an tsaro?
Tambayoyi sun yawaita game da yanayin tsaro a wajen taron da kuma yadda aka shigar da bindiga cikin otel ɗin. Mahalarta taron sun nuna cewa akwai na’urar binciken ƙarfe a wajen babban zauren, amma babu irin wannan na’urar kafin nan ko a babbar ƙofar shiga otel ɗin kansa.
Da farko Trump ya ce ginin “ba shi da cikakken tsaro,” amma daga baya ya ce ba a sami damar kutsawa babban zauren da ake taron ba, kuma yana da “tsaro sosai.”
Shingen binciken da wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin ƙetarewa yana “daidai wajen babban zauren taron ne,” in ji hukumomi. “Saboda wannan shingen ya yi aiki, shi ya sa ba a samu wanda ya ji rauni ba,” in ji Pirro.
A cewar Trump, jami’an tsaro sun yi “aikin da ya fi na Butler kyau,” inda aka yi ƙoƙarin kashe shi a shekarar 2024 yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓe a jihar Pennsylvania.
DUNIYA
4 minti karatu
Abubuwan da muka sani game da harbe-harben da aka yi a taron liyafar Trump da manema labarai
Fargabar tsaro ta ƙaru bayan afkuwar harbe-harben, tare da yin tambayoyi kan gibin da aka samu wajen bincike a otel ɗin, duk da cewa akwai shingen bincike da ya kamata ya hana maharin shiga babban zauren taron.
Rumbun Labarai










