| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
'Lokaci na ƙurewa' Trump ya yi gargaɗi ga Iran yayin da ƙofofin diflomasiyya ke rufewa
Daga farko dai Shugaban Amurkan ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar na halin "rai-kwakwai-mutu-kwakwai“ bayan ya yi watsi da buƙatun Tehran, waɗanda ya bayyana a matsayin “abin da ba za a laumta ba kwata-kwata”.
'Lokaci na ƙurewa' Trump ya yi gargaɗi ga Iran yayin da ƙofofin diflomasiyya ke rufewa
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce “lokaci na ƙurewa” yayin da tattaunawa da Iran ƙe barazanar ga ƙoƙarin kawo ƙarshen yaƙin. (TSOHON HOTO) / Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗi ga Iran, yana mai cewa "lokaci na ƙurewa" domin "su ɗauki mataki" kafin "ya kasance babu abin da zai rage daga cikinsu."

"LOKACI NA DA MUHIMMANCI!" a cewarsa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social ranar Lahadi.

Kalaman Trump na zuwa ne cikin barazanar da ake yawan yi wa Tehran kan ta amince da buƙatun Amurka na tsagaita wuta, waɗanda suka haɗa da ɗaukar alƙawarin rashin inganta kayayyakin nukiliya da kuma miƙa ingantattun sinadarin yureniyom da ke a tashoshin nukiliyar Iran ga dakarun Amurka da kuma sake buɗe mashigin ruwan Hormuz.

Tashin hankali a yankin ya ƙaru sosai tun lokacin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran ranar 28 ga watan Fabrairu, lamarin da ya haifar da ramuwar gayya daga Tehran kan Isra’ila da kuma ƙwayen Amurka a cikin ƙasashen Larabawan da ke gaɓar tekun Fasaha tare da rufe mashigin ruwan Hormuz.

An tsagaita wuta ranar 8 ga watan Afrilu ta hanyar shiga tsakanin Pakistan, amma tattaunawa a Islamabad ta gaza cim ma matsaya mai ɗorewa.

Daga baya Shugaban Amurka Donald Trump ya tsawaita tsagaita wutar har sai baba ta gani.

Yayin da tsagaita wutar ke ci gaba da aiki, ta ƙasace ƙarƙashin ƙarin matsi a cikin ‘yan kwanakin nan, inda Trump ke bayyana ranar Litinin cewa tana cikin hali na “rai-kwawkai-mutu kwakwai" bayan ya yi watsi da shawarwarin tsagaita wutar Tehran na baya bayan nan a matsayin wani abin da “ba za a lamunta ba.”

“Yaƙi na zaɓi"

Yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar a kanIran ya kuma kasance kan ajandar ziyarar aiki da Trump ya kai Beijing kwanan nan.

A wata sanarwar da ta fitar daga baya ranar Lahadi, fadar White House ta ce Trump da Shugaban China Xi Jinping sun yarda cewa Iran “ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, kuma sun yi kira da a sake buɗe mashigin ruwan Hormuz tare da cim ma matsayar cewa babu wata ƙasa ko ƙungiya da za a ƙyale ta rinƙa karɓar haraji a kan mashigin.”

Iran, a nata ɓangaren, ta yi gargaɗin cewa idan Amurka ta sake fara “yaƙinta na zaɓi," za ta fuskanci ƙarin sakamako na tattalin arziki wanda za ta “iya kauce wa” idan ba ta yi hakan ba.

“Ka ma ajiye ƙarin kuɗin mai da taɓaraɓarewar kasuwar hannayen jari. Asalin wuyar za ta fara ne a lokacin da matakin bashin Amurka da bashin gidaje suka fara tashin gwauron zabi,” a cewar ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi a ƙarshen mako.