Saudiyya ta ce tsaron sararin saman ƙasar ya tare ya kuma lalata jiragen sama marasa matuki guda uku bayan sun shiga sararin samaniyarta daga Iraki.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Tsaro, Turki al-Maliki, ya ce an kakkaɓo waɗannan jiragen marasa matuki a safiyar Lahadi bayan sun shiga sararin samaniyar Saudiyya daga cikin Iraki.
Maliki ya jaddada cewa masarautar tana da haƙƙin mayar da martani a lokaci da wurin da ya dace.
Ya ce: 'Saudiyya za ta ɗauki kuma ta aiwatar da duk wasau matakai da suka wajaba don mayar da martani ga kowane yunƙuri na keta ikon cin gashin kan ƙasar, da tsaro da amincin 'yan ƙasar da mazaunanta.'
Tashin hankali a yankin ya ƙaru tun bayan da Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare kan Iran a watan Fabrairu. Tehran ta rama da hare-hare a kan Isra'ila da ƙawayen Amurka a yankin Tekun Fasha, ciki har da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, tare da rufe Mashigar Hormuz.
An fara tsagaita wuta a ranar 8 ga Afrilu bayan Pakistan ta shiga tsakani, amma tattaunawar da aka yi a Islamabad ba ta haifar da yarjejeniya mai ɗorewa ba. Daga baya, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tsawaita yarjejeniyar ba tare da sanya wa'adi ba.
Tun da farko a wannan ranar, harin jirgi mara matuƙi ya haifar da tashin gobara a kusa da wata tashar samar da wutar lantarki ta nukiliya a Abu Dhabi, in ji hukumomi, inda suka ce babu raunuka ko wani tasiri kan yanayin tashin turiri.
Ofishin Watsa Labarai na Abu Dhabi ya ce: 'Hukumomi sun ɗauki mataki kan gobarar da ta ɓarke a cikin injinan samar da wutar lantarki a hararbar cibiyar samar da makamashin nukiliya ta Barakah a yankin Al Dhafra, wadda harin jirgi mara matuƙi ya haifar.'








